Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya, 16/12/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Badamasi Abdulkadir Mukhtar, Aisha Aliyu Ja'afar, Rabiatu Runka

  1. Ademola Lookman ya zama gwarzon ɗan ƙwallon ƙafa na Afirka

    Ɗan wasan Super Eagles na Najeriya, Ademola Lookman

    Asalin hoton, Instagram/Ademola Lookman

    Ɗan wasan ƙwallon ƙafa na tawagar Super Eagles ta Najeriya da ƙungiyar Atalanta ta Italiya, Ademola Lookman ya lashe kyautar ɗan ƙwallon ƙafa na Afirka.

    Ɗan wasan ya doke fitattun zaratan ƴan wasa irin Achraf Hakimi na Morocco da Simon Adingra na tawagar Ivory Coast da ƙungiyar Brighton & Hove Albion ta Ingila da Ruto Williams na Afirka ta Kudu da Serhou Guirassy na ƙasar Guinea da ƙungiyar Dortmund ta Jamus domin lashe kyautar.

    An gudanar da bikin karrama gwarazan ƴanwasan na Afrika ne a a birnin Marrakech na ƙasar Morocco

    Lashe kyautar a wannan karon ya sa ƴan wasan Najeriya biyu sun lashe kyautar sau biyu a jere bayan Victor Osimhen da ya lashe kyautar a bara.

  2. Farashin abinci ya tashi a Najeriya - Rahoto

    KAYAN MASARUFI

    Asalin hoton, Getty Images

    Farashin kayan abinci a Najeriya ya ƙara tashi daga kashi 33.88 zuwa kashi 34.60, a watan Nuwanba 2024, kamar yadda hukumar kidaddiga ta ƙasar ta sanar a ranar Litinin.

    Rahoton hukumar ya ce an samu ƙarin kashi 0.72 cikin dari idan aka kwatanta da na watan Oktoba, 2024.

    'A rahoton shekara-shekara an samu ƙarin kashi 6.40 idan aka kwatanta da na watan Nuwanba 2023," cewar rahoton.

    Ana la'akari da farashin kayan masurufi da suka hada da shinkafa da fulawa da hatsi da busasshen kifi da ƙwai da naman shanu da na rago da kaji da sauransu.

    Farashin abinci da na kayan masarufi ya yi tashin gwauron zabi a Najeriya tun bayan kama mulkin shugaban ƙasar, Bola Tinubu, lamarin da ake ganin shi ne mafi muni da ƙasar ta taɓa faɗawa cikin tun bayan samun ƴanci, kimanin shekara 60 da suka gabata.

    Cire tallafin man fetur da barin naira ta tantance darajarta a kasuwa na daga cikin matakan da shugaban ya ɗauka waɗanda ake ganin su ne suka ta'azzara yanayin.

    A lokacin da ya karɓi cikin watan Mayun 2023, Tinubu ya ayyana cire tallafin man fetur, lamarin da ya sa farashin fetur ɗin ya zuwa yanzu ya zarta naira 1,000 a wasu sassan ƙasar.

    Hakan na nufin ƙarin farashin sufuri wanda shi kuma kan shafi farashin kayan masarufi.

  3. An ƙaddamar da asibitin bayar da kulawa kyauta a Katsina

    Dikko Radda

    Asalin hoton, Katsina Post

    Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda ya ƙaddamar da asibitin kulawa da marasa lafiya kyauta - musamman mata masu juna biyu da ƙananan yara - a babban birnin jihar.

    Asibitin wanda wata gidauniyar taimaka wa al'umma ta Maiwada Global ta gina, an samar da shi ne a cikin birnin na Katsina.

    Wanda ya gina asibitin, Haruna Maiwada ya ce an samar da asibitin ne "Domin tallafa wa a'ummar yankin da magani da kulawa kyauta".

    Gwamnan jihar, Dikko Radda ya bayyana cewa, gina asibitin zai taimaka wa ƙoƙarin gwamnati na inganta lafiyar al'umma da rage wahalhalun da jama'a ke fuskanta wajen samun magunguna da kulawar ƙwarrarun likitoci.

    Katsina na daga cikin jihohin da ƙananan yara ke fama da matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki wanda ke haifar da tamowa.

    Ƙungiyar likitoci masu bayar da agaji ta ƙasa da ƙasa (MSF), a cikin wani rahoto da ta fitar cikin wannan wata na Disamba, ta ce matsalar rashin abinci mai gina jiki a tsakanin ƙananan yara a wasu yankunan jihar ta Katsina "ya nunka idan aka kwatanta da bara".

    ...

    Asalin hoton, Katsina Post

  4. Majalisar zartarwar Najeriya ta amince da kasafin kuɗin Najeriya tiriliyan 47.9

    Tinubu

    Asalin hoton, Tinubu Facebook

    Majalisar zartarwar Najeriya ta amince da kasafin kudin 2025, wanda shugaba Tinubu zai gabatar.

    Da yake jawabi jim kaɗan bayan kammala taron majaliar zartarwa a fadar shugaban Najeriya, a yau Litinin, ministan kasafin kuɗi, Atiku Bagudu, ya ce kasafin kuɗin na 2025, an yi hasasshen za a kashe kusan naira tiriliyon 48.

    Ministan ya ec an yi kasasfin kudin ne kan farashin gangar mai dallar Amurka 75, tare da samar da gana sama da miliyan biyu duk rana, yayin aka yi hasashen farashin dalar Amurka kan naira 1,400.

    Minitan ya ce kuma an yi hasashen kuɗin shigar ƙasar kan kusan naira tiriliyon 35.

    Akwai alamun dake nuna cewa shugaba Tinubu ba zai gabatar da kasafin kuɗin gaban Majalisar Dokokin ƙasar a gobe Talata ba kamar yadda aka tsara tunda farko.

    Ministan yaɗa labaran ƙasar Muhammed Idris ya ce shugabannin majalissun da ɓangaren zartarwa na aiki tare domin samar da ranar da za a gabatar da ƙudurin.

  5. Shugaba Macron na jagorantar taron gaggawa kan guguwar Chido

    Masu aikin ceto na can na neman wadanda suka tsira daga guguwar Chido da ta fadawa tsuburin Mayotte na Faransa da ke yankin tekun India a ranar Asabar.

    Guguwar ta ɗaiɗaita kusan ɗaukacin yankin, taɓo da ɓaraguzai sun cika titunan babban birnin yankin Mamoudzou, a ya yin da kananan garuruwan da ke kewaye da wurin suka zama kufai.

    Ministan riko na harkokin wajen Faransa, Bruno Retailleau, ya ce za a dauki kwanaki kafin kafin a gano ainahin barnar da guguwar Chido ta yi, da kuma adadin wadanda suka mutu.

  6. EFCC ta kama mutum 792 a Legas kan zargin damfara ta intanet

    ...

    Asalin hoton, EFCC

    Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya, EFCC,Ola Olukoyede, ya bayyana cewa hukumar ta kama mutum 792 da ake zargi da aikata laifin damfara ta Intanet da suka gada da damfara ta hanyar soyayya.

    An gabatar da wadanda ake zargin ne a ranar Talata, 10 ga watan Disamba, 2024, yayin wani samame da jami'an hukumar suka kai a maɓoyar wadanda ake zargin, a cikin wani katafaren gini dake lamba bakwai, Oyin Jolayemi Street, Victoria Island, Lagos, bayan hukumar ta samu bayanan sirri.

    Da yake jawabi ga manema labarai, Olukoyede, a ranar Litinin, 16 ga watan Disamba, 2024, a ofishin hukumar dake Lagos ya bayyana cewa cikin wadanda aka kama akwai yan Chana 148, da mutum 40 ƴan ƙasar Filipinos da kuma ƴan Kharzartans biyu, sai ɗan Pakistan da ɗan Indonesia.

    Shugaban wanda ya samu wakilcin Diraktan hulda da jama'a na hukumar, CE Wilson Uwujaren, ƴan ƙasashen wajen na amfani da ginin a matsayin wajen da suke koyar da ƴan Najeriya yadda ake damfara ta Intanet musamman ta hanyar soyayya, "Ƙasa a cikin ginin an cika shi da manyan kamfutoci", in ji shi.

    "A hawa na biyar, masu binciken sun gano layukan waya 500 da wayoyin sadarwa da aka tana da domin gudanar da ayyukan ta'addanci, ana amfani da ƴan Najeriyar wajen yaudarar ƴan ƙasashen waje yawanci ƴan Amurka da Canada da Mexico da wasu ƙasashen Turai da dama.

    ...

    Asalin hoton, EFCC

  7. Shugaban HTS ya gana da Jakadan Majalisar Dinkin Duniya

    Manyan jami'an Diflomasiya na kara azama domin samun ganawa da sabbin shugabannin Syria, duk da damuwar da ake nunawa kan asalin na mayakan Jihadi.

    Kungiyar ta masu ikirarin jihadi da ta ƙwace mulki a Damascus, HTS ta ce shugabanta Ahmed al-Sharaa, ya gana da jakadan Majalisar Dinkin Duniya a kasar a kokarin ganin yadda za a tafiyar da mika mulki cikin kwanciyar hankali da kuma batutuwan da suka shafi sauyi a kwamitin tsaro na Majalisar da ya ayyana su a matsayin kungiyar ta'addanci.

    Amurka da Burtaniya sun ce yanzu haka suna tuntuba juna da shugaban 'yan tawayen, sannan tawagar Faransa na hanyar isa Syria yau Litinin.

    Qatar da Turkiyya na shirin sake bude ofishin jakadancinsu.

    Wakiliyar BBC ta ce "Takunkuman Amurka da Turai na daga cikin abubuwan dake haifar da tarnaki wajen kai wa kasar kayan agaji.

    Isra'ila dai na cigaba da kai hare-hare har yanzu a Syria.

  8. Majalisar zartarwar Najeriya za ta tafi hutu

    NIGERIAN PRESIDENT

    Asalin hoton, Tinubu/Twitter

    Majalisar zartarwar Najeriya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasar, Bola Tinubu ta sanar da cewa za ta tafi hutu daga ranar 18 ga watan Disamban 2024 zuwa 6 ga watan Janairun 2025.

    Majalisar ta bayyana hakan ne bayan wata tattaunawa da ta gudanar yau Litinin a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

    A bayanin bayan taron majalisar, hakan na nufin ba za a gudanar da wani taron majalisar ba a tsawon lokacin da za ta kwashe tana hutu.

    Majalisar zartaswar Najeriya ta ƙunshi shugaban ƙasa da mataimakinsa da kuma ministoci.

    Sanarwar da majalisar ta fitar ta nuna cewa a taron na yau Litinin ta kuma tattauna batun kasafin kuɗin shekarar 2025, da shugaban ƙasar zai gabatar a zauren Majalisar dokokin ƙasar.

    Sufuri kyauta:

    Majalisar zartaswar ta kuma ayyana sufuri kyauta ga ƴan ƙasar daga ranar 20 ga watan Disamba, 2024 zuwa 5 ga watan Janairun 2025 zuwa sassa daban-daban na ƙasar, kamar yadda gwamnati ta saba yi a lokacin "bukukuwan Sallah da na Kirisimeti."

    Sauya sunan jami'ar Abuja:

    "Majalisar ta kuma amince da sauya sunan Jami'ar Abuja zuwa sunan tsohon shugaban ƙasar mulkin soji, Janar Yakubu Gowon, matakin da majalisar ta ce za ta gabatar gaban majalisar dokokin ƙasar domin neman amincewa."

  9. Yadda hazo ya hana saukar jirage a Kano

    Northen Nigeria

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Gurɓacewar iska ta ta'azzara sosai a wasu sassan arewacin Najeriya a yanzu.

    A jihar Kano da ke yankin arewa masu yammacin Najeriya yanayin hazo ya kawo tsaiko ga harakokin jama’a na yau da kullum a cikin ‘yan kwanaki nan.

    Wannan lamari ya sa har ana karkatar da saukar wasu jirage a babban birnin jihar zuwa wasu wurare a ranar Lahadi, yayin da kuma yana hana wasu fitowa.

    Wani mazaunin Kano, malamin makaranta , Muhammad Lawalli Abdu, ya shaida wa BBC cewa akwai sanyi da hazo a garin na Kano, lamarin da ya sanya mutane da dama ke fama da mura.

    Adamu Danjuma Isa bakin Wafa ya shaida wa BBC cewa akwai sanyi ko da yake rana ta bude a yau, "Amman jiya akwai hazo sosai da ƙura amman yau akwai sauƙin ƙura da hazo, ƙadan ya rage jiya mu kunna fitila saboda duhu, kuma an samu tsaikon abubuwan da suka shafi kasuwa."

    Dr. Abubakar Maina Waziri , kwararren likita a Asibitin Dala da ke Kano, ya ce ana samun yaduwar cututtuka da suka hada da tari da mura da ciwon wuya da kuma ƙaruwar tashin ciwon Asthma, " Ya kamata idan mutane z asu fita su riƙa amfani da takunkumin kariya.

  10. HTS ta ce za ta rusa dukkan ƙungiyoyi masu riƙe da makamai na Syria

    Ahmed al-Sharaa

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Ahmed al-Sharaa

    Jagoran 'yan tawayen kungiyar Hayat Tahrir al-Sham Ahmad al-Sharaa da suka jagoranci hambarar da mulkin shugaba Bashar al-Assad na Syria, ya ce za a rusa dukkan kungiyoyi masu dauke da makamai karkashin jagorancin sabuwar gwamnatin rikon kasar.

    Mista al-Sharaa ya shaidawa ƴan jarida cewa sojojin Siriya ne kadai suke da ikon riƘe makamai.

    Shugabar hukumar Tarayyar Turai kan manufofin kasasshen waje, Kaja Kallas, ta ce ta aike babban jami'in Diplomasiyyar Turai zuwa Damascus, domin tattaunawa da shugabannin sabuwar gwamnati da 'yan kasar.

    "A yau za mu tattauna kan huldar kasashen waje, za mu tattauna da sabuwar gwamnatin Syria, maganar daya ce alaka tsakanin Turai da Syria za ta kullu ne idan sabuwar gwamnati na kan turbar da ta dace.

    A bangare guda kuma kungiyar ƴan tawayen Kurdawa a arewa maso gabashin Syria ta sanar da aje makamai, da aniyar miƙa wuya ga sabuwar gwamnatin Syria.

  11. Kotun ƙoli ta kori buƙatar sauke Tinubu daga mulki a bisa zargin ta'ammuli da ƙwaya

    Tinubu

    Asalin hoton, Tinubu/Facebook

    Kotun ƙolin Najeriya ta yi watsi da ƙarar da ke neman a tsige shugaban Ƙasar, Bola Tinubu daga muƙaminsa.

    Ƙarar wadda ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Hope Democratic Party a zaɓen 2019, Ambrose Aworu, ya fitar tana neman kotu ta cire shugaba Tinubu a bisa zargin alaƙa da miyagun ƙwayoyi.

    A hukuncin da suka bayar yau Litinin, alƙalan kotun suka bayar a ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Uwani Abba-Aji sun yanke wa Mr Owuru tarar naira Miliyan biyar

    Kotun ta kuma gargadi masu amsar ƙara kada su sake amsar ƙarar da bata da makama daga Mr Owuru.

    A cikin ƙarar da ya shigar, Mr Owuru ya kuma yi zargin cewa shugaba Tinubu ɗan leƙen asiri ne na hukumar CIA ta Amurka, lamarin da ya haƙiƙance cewa ya saɓa wa sharaɗin zama shugaba ƙasa a Najeriya.

  12. Ministocin Faransa uku sun isa Mayotte domin ganin ɓarnar da guguwa ta yi

    Ministoci uku na kasar Faransa sun isa yankin kasar da ke tekun Indiya na Mayotte, kwanaki biyu bayan mahaukaciyar guguwa ta afkawa yankin tare da lalata tsibirin.

    Sun isa filin jirgin saman Mayotte, wanda shi ma ya yi kaca-kaca, domin duba girman barnar da guguwar Chido ta yi a yankin.

    Gidaje da dama sun daidaice, ya yin da ake fargabar daruruwan mutane sun mutu wasu kuma ba asan inda suke ba.

    Kungiyar agaji ta Red Cross, ta ce ana cikin mummunan yanayi a Mayotte, ya yin da masu aikin ceto ke neman wadanda suka tsira a ɓaraguzan gine-ginen da suka rushe.

    Nan gaba kadan ake sa ran shugaba Emmanuel Macron zai jagoranci taron gaggawa kan halin da ake ciki.

  13. Harin Isra'la ya kashe mutane fiye da 50 a Gaza - Hamas

    Khan Younis

    Asalin hoton, afp

    Likitoci da ma'aikatan agaji sun ce hare-haren Isra'ila ta sama da kuma ta ƙasa sun kashe mutane fiye da 50 a Gaza.

    Sun ce daga cikin mutanen da aka kashe harda ƙananan yara da wani ma'aikacin gidan talabijin ɗin Al Jazeera da kuma jami'a tsaron Civil Defence.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai harin ne a wajen da mayaƙan Hamas da sauran ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi ke taruwa.

    Ma'aikatar lafiya ta Hamas ta ce idan aka tattara alƙaluma, ya zuwa yanzu Falasɗinawa fiye da 45,000 aka kashe tun bayan fara yaƙi tsakanin Isra'ila da Hamas, watanni 14 da suka wuce.

    Ma'aikatar ba ta banbance ba tsakanin fararen hula da kuma mayaƙa a cikin mutanen da aka kashen, amma a cikin wtan Oktoba ta bayar da rahoton cewa daga cikin mutanen da aka kashe akwai mata da ƙananan yara da kuma tsofaffi 29,980.

    Gwamnatin Isra'ila ta saba fitowa tana ƙaryata waɗannan alƙaluma, amma hukumomin Majalisar Dinkin Duniya sun amince da su.

    Yaƙin ya ɓalle ne bayan mayaƙan Hamas sun kai wani mummunan hari a a kudancin Isra'ila, a ranar 7 ga watan Oktoban 2023, inda ta kashe mutane 1,200 da kuma garkuwa da wasu 251.

  14. EU ta ƙaƙaba takunkumi kan Rasha saboda Ukraine

    EU

    Ƙungiyar tarayyar Turai ta amince da sabbin takunkumi a kan Rasha da dukkan masu hannu a yaƙin da Rashan ke yi da Ukraine.

    A karon farko kuma, ƙungiyar ta amince da sanya takunkumi a kan kamfanonin China masu bai wa Rasha kayan aiki, musamman na jirgin sama marar matuƙi da sauran kayan lantarki.

    Takunkumin ya haɗa da ɗaukar ƙwararan matakai a kan kamfanonin India da Serbia da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

    An kuma sanya takunkumi a kan jami'an Koriya ta Arewa biyu, da dakarun Rasha da suka kai harin rokoki kan asibitin yara a Ukraine, cikin watan Yuli.

  15. Yunwa da ƙishi na kashe mutane a tsibirin Mayotte

    Mayotte

    Asalin hoton, Reuters

    Ƴar majalisar dattawa mai wakiltar tsibirin Mayotte, ta ce mutane suna mutuwa saboda tsananin yunwa da ƙishi.

    A yayin ziyarar da ta kai wata makaranta da jama'a ke neman mafaka saboda mummunar guguwa da ruwan sama mai ƙarfi da ya raba su da muhalin su, Salama Ramia ta shaida wa gidan talabijin na BFM TV cewa: "Akwai marasa lafiya da dama, cikin su harda masu kwanciya a ƙasa saboda babu makwanci."

    Hukumomi sun ce an fara aikin gyara turakun lantarki da ruwan fanfo a tsibirin.

    Rahotannin da wasu hukumomin da ke aikin ceto a yankin suka fitar sun nuna cewa yankin yana fuskantar barazanar fari, kuma jama'a sun shiga yanayi na ƙarancin ruwa.

  16. Amnesty International ta zargi Serbia da keta ƴancin ƴan jarida

    Ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International, ta zargi hukumomi da amfani da wata manhaja wajen yi wa ƴan jarida leƙen asiri a Serbia.

    Ƙungiyar ta ce idan aka sanya manhajar a wayar ƴan jarida, tana tattara bayanan lambobin wayar, da kuma hotunan da ke ciki inda take tura su kai tsaye ga hukumomin tsaron sirri, baya ga buɗe na'urar ɗaukar hoto da ta naɗar bayanan wayar ƴan jarida kai tsaye domin amfanin jami'an tsaron na sirri.

    Amnesty ta yi zargin cewa wannan salon yana daga cikin yunƙurin gwamnatin Serbia na murƙushe ayyukan ƙungiyoyin fararen hula.

    Gwamnatin Serbia dai ba ta yi martani ba a kan wannan zargi.

  17. Hedikwatar tsaro ta musanta kafa sansanin sojin Faransa a Najeriya

    Janar Christopher Musa

    Asalin hoton, X/Defence HQ

    Hedikwatar tsaron Najeriya ta ce babu gaskiya a labaran da ake yaɗawa cewa dakarun Faransa na shirin kafa sansaninsu a Najeriya.

    Wata sanarwar da daraktan yaɗa labaran Hedikwatar tsaron Najeriya, Manjo Janar Edward Buba ya fitar a yau Litinin ta ce labaran jita-jita ce, kuma basu da tushe.

    Ya ce, “An ankarar da hedikwatar tsaron Najeriya a kan rahotannin da ake yaɗawa a shafuka sada zumunta da ke zargin cewa zangon farko na dakarun Faransa ya isoa Maiduguri a shirye-shirye kafa sansanin su a yanki Arewa maso gabashin Najeriya.

    “Rundunar sojin Najeriya na tabbatar da cewa wannan rahoto na ƙarya ne kuma bashi da makama. Idan za a iya tunawa babban hafsan Najeriya, Janar Christopher Musa, ya yi bayani game da wannan batu, kuma ya jaddada cewa jita-jita ne kawai aka kitsa a wannan labari.''

    Hedikwatar tsaron ta buƙaci jama'a su yi watsi da rahotannin ƙaryar, waɗanda ta ce har yanzu akwai masu ci gaba da yaɗa su domin cimma muradun su na son rai.

  18. Cancanta ya kamata mu bi wajen zaɓen shugaban ƙasa ba ɓangaranci ba - Shekarau

    Shekarau

    Asalin hoton, Shekarau Facebook

    Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya ce kamata ya yi ƴan Najeriya su mayar da hankali wajen zaɓen shugaban ƙasa da ya cancanta a zaɓe mai zuwa, a madadin karkata ga yankin da shugaban zai fito.

    Malam Shekarau ya ce batun yankin da shugaban ƙasa ya fito ba shi da wani muhimmanci a tsarin shugabanci na gari.

    Da ya ke tsokaci game da kiraye-kirayen mayar da mulkin Najeriya ga wani ɓangare na ƙasar a hirar sa da gidan talabijin na Channels a Najeriya, Malam Shekarau ya ce “Ya kamata jam'iyyu su fitar da tsari mai kyau na zaɓen wanda ya fi cancanta a tsakanin ƴan takara. Wannan zai bai wa ƴan Najeriya damar darjewa a tsakanin su, domin zaɓen wanda ya fi dacewa da zama shugaban ƙasa''

    An shafe watanni ana muhawara a kan kiraye-kirayen mayar da mulki arewacin Najeriya a shekarar 2017.

    Sai dai masu adawa da hakan sun ce yankun kudanci da shugaba Bola Tinubu ya fito bai kammala wa'adin sa na shekara takwas ba, don haka Arewa ta jira sai ya kammala.

    Amma tsohon gwamnan jihar Kano na ganin cewa ya kamata a mayar da hankali wajen zaɓen shuagabanni na gari da za su yi wa ƙasa aiki.

  19. HRW ta buƙaci a kare mata daga cin zarafi a Sudan

    Sudan

    Asalin hoton, AFP

    Kungiyar kare hakki ta Human Right Watch tayi kira ga Majalisar Dinkin Duniya ta kare mata da yara daga cin zarafi ta hanyar lalata a Sudan.

    Ta ce ayyukan Fyaɗe da mayakan RSF ke aikatawa laifukan yaƙi ne.

    A watan Oktoba, wani binciken Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa matsalar fyaɗe ta kai mataki mai ban tsoro a Sudan.

    Human Right ta tattauna da gwamman matan da galibinsu aka yi musu fyade a gaban ƴan uwansu ko iyalai.

    Ƙungiyar ta yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ƙasashen tarayyar Afirka su tura dakarun da za su tsare ko dakile irin wannan cin zarafin da kuma hukunta masu laifi.

  20. Kotu na shirin zama kan tsige shugaban Koriya ta Kudu

    Yoon Suk Yeol

    Asalin hoton, Reuters

    Kotun tsarin mulki a Koriya ta Kudu na ganawa domin shirye-shiryen soma sauraron batun tsige shugaba Yoon Suk Yeol.

    Masu shari'a na nazarin kuri'un da majalisa ta kada a ranar Asabar da suka amince a dakatar da shi daga Ofis bayan rashin nasara a yunkurinsa na sanya dokokin soji a kasar.

    Kotun na da kwana 180 ta yanke hukunci kan ko za ta amince da tsigewar, kuma hakan ne zai bada damar gudanar da zabe gadan-gadan ko kuma ta mayar da Mista Yoon.

    A ranar 27 ga watan Disamba za a yi zama na farko. Sanna A jiya Lahadi ya gaggara amsa gayyatar da aka masa domin amsa tambayoyi, kuma 'yan sanda na iya kamo shi idan bai bayyana kansa ba a wannan makon