Donald Trump ya fitar da sabon hotonsa na Shugaban ƙasa

Asalin hoton, TRUMP VANCE TRANSITION TEAM HANDOUT/EPA
A hukumance an bayyana hotuna sabon shugaban Amurka, Donald Trump da mataimakinsa, JD Vance gabanin rantsar da su a ranar Litinin mai zuwa.
Dukkanin mutanen biyu suna sanye ne da rigar kwat mai launin shuɗi, da farar riga a ciki, sai kuma shuɗin lakatayi.

Asalin hoton, TRUMP VANCE TRANSITION TEAM HANDOUT/EPA
Yanayin fuskar Trump a hoton ya yi hannun riga da na mataimakinsa, JD Vance, inda Trump ya murtuke fuska tare da tsuke baki.
Shi kuwa JD Vance ya saki fuska tare da yin murmushi, sannan ya rungume hannu a hoton nasa.
Hoton Trump na wannan karo ya sha bamban da wanda ya yi amfani da shi a mulkinsa na farko a shekarar 2017.

Asalin hoton, Library of Congress
Duk da cewa a hotonsa na baya yana sanye ne da kaya shigen irin na yanzu a hoton, to amma an ga yadda ya yi murmushi a cikin hoton.

















