Dalilin da ya sa gwamnoni suka amince da sabuwar dokar haraji - Uba Sani

Batun gyara a kan dokar harajin dai ya janyo rarrabuwar kawuna a tsakanin ɓangarorin ƙasar musamman al'ummar yankin arewaci da suka yi zargin cewa sauyin zai iya yi musu illa ga tattalin arziƙinsu.
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya shaida wa BBC cewa sun amince da dokar ne saboda an yi wa kowa adalci.
"Mun zauna mun ga tsarin, mun ga cewa babu wata jiha da za a iya cutar da ita, inda a sabon kasafin zai kasance kashi 50 cikin 100 ne ga dukkan jihohi, yayin da za a bada kashi 30 ga jiha daga cikin abin da ta tara, sai kuma kashi 20 za a yi amfani da yawan al'ummar jihar."
A zaman da gwamnonin Najeriyar suka gudanar a Abuja, sun yi gyare-gyare ga ƙudurin harajin na shugaba Tinubu, musamman ɓangaren rabon harajin kaya na VAT, wanda shi ne ya fi janyo ce-ce-ku-ce.
Gwamna Uba Sani ya ce a zaman nasu sun amince da soke batun ƙara kudin VAT.
"Mun cimma matsaya ba za taɓa manyan ma'aikatun gwamnati da a baya dokar ta shafa ba, irinsu TETfund da NITDA."
Sanarwar bayan taro da ƙungiyar gwamnonin Najeriyar ta fitar, wadda ta samu sa hannun shugabanta, kuma gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ta ce ba ta goyon bayan ƙarin harajin VAT a wannan lokaci.
Sannan kuma ta bayar da shawarar cire sashen sabon ƙudurin dokar da ya shata lokacin dakatar da ware wa Gidauniyar tallafa wa manyan makarantu da takwarorinta da sabuwar dokar ta ambato kuɗi.
"Mambobin wannan ƙungiya sun amince cewa ka da a yi ƙari a harajin VAT, ko rage harajin kamfanoni na CIT a wannan lokaci, domin tabbatar da daidaiton tattalin arziƙi," in ji sanarwar.
Tun farko, sabon tsarin rabon harajin VAT da ke ƙunshe a ƙudurin yin gyara ga dokar haraji da shugaba Tinubu ya gabatar wa Majalisar dokoki ya buƙaci a ware kashi 60 cikin ɗari ne domin rabawa gwargwadon gudumawar da kowace jiha ta bayar.
Wanda hakan ya nunka har sau biyu a kan asalin tsarin da ake amfani da shi na kashi 20 cikin ɗari.
Shawarar da gwamnonin suka yanke na nuna cewa an ƙara kashi 10 cikin ɗari a kan tsarin da ake amfani da shi a yanzu, yayin da aka zabtare kashi 30 cikin ɗari daga abin sabon tsarin da shugaba Tinubu ya gabatar wa Majalisa.










