Man United ta yi watsi da tayin Napoli kan Garnacho, Al-Hilal na tattaunawa da Liverpool kan Salah

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta yi watsi da tayin fam miliyan 40 da kulub din Napoli na Italiya ya yi ma ta kan dan wasan Argentina Alejandro Garnacho mai shekara 20. (Mirror)
Everton na duba yiwuwar dauko tsohon dan wasan Chelsea kuma mai kai hari na Brazil Willian, mai shekara 36, wanda ke shirin barin kulub din Olympiakos a watan Disambar bana. (Telegraph)
Watakil Manchester City za ta biya fam miliyan 67 kan dan wasan Juventus and kuma mai tsaron gida na Italiya Andrea Cambiaso, 24, idan an bude kasuwar musayar 'yan wasa a watan Junairu. (Gianluca di Marzio)
Borussia Dortmund ta bi sahun AC Milan a zawarcin dan wasan gaba na Ingila mai taka leda a Manchester United Marcus Rashford, 27. (Florian Plettenberg, Sky Germany)
Arsenal ta amince ta kara albashin dan wasan tsakiya na Sifaniya mai taka leda a Real Sociedad da ta ke zawarci, wato Martin Zubimendi. (Football Transfers)
West Ham da Tottenham ana son dan wasan gaba na Sifaniya mai taka leda a Barcelona Ansu Fati, 22. (Sport - in Spanish)
Real Madrid ma na son dan wasan tsakiya na Faransa mai taka leda a Arsenal William Saliba, mai shekara 23. (Foot Mercato)
Kulul din Al-Hilal na Saudiyya ya fara tattaunawa da wakilan dan wasan gaba na Masar mai taka leda a Liverpool, Muhammad Salah. (L'Equipe)
West Ham na duba yiwuwar daukar mai kai hari na Najeriya, da ke taka leda a Nottingham Forest, Taiwo Awoniyi mai shekara 27. (Florian Plettenberg)
Forest din na hankoron dan wasan Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo, mai taka leda a Brentford Yoane Wissa, idan ya bar kulub din a wannan watan. (Telegraph)
Dortmund na son dan wasan Jamus, mai taka leda Brentford Kevin Schade, 23. (Bild)
Atlanta United ta yi wa dan wasan Faransa mai taka leda a Crystal Palace Odsonne Edouard, tayin fan miliyan 16, wanda a yanzu ya ke zaman aro a Leicester City. (Mail Online)










