Gwamnati na shirin sake kara kuɗin lantarki a Najeriya

Ministan Lantarki a Najeriya, Adebayo Adelabu, ya ce gwamnatin Najeriya na nazarin ƙarin kuɗin lantarki a kokarin cike giɓin bashin naira tiriliyan huɗu da ake bin ɓangaren.
Adebayo da ke waɗannan bayanai a taron masu ruwa da tsaki a Abuja, ya ce ta wannan hanya ce kaɗai za a iya ceto ɓangaren da kuma cigaba da gudanar da ayyukansa.
Duk da karin ƙudin lantarki da aka yi wa kwastamomi da ke tsarin Band A, 'yan Najeriyar na kokawa ganin cewa wutar ba ta waɗatar da su.
Amma Adelabu ya ce matakin na da muhimmanci wajen inganta tattalin arziki da cigaban ƙasar.
Wannan dai na nufin gwamnatin za ta kawo ƙarshen tsarin tallafin da ake bai wa ɓangaren lantarki, yanayin da zai tilasta ƙarin kuɗin wuta ga kowa.
Jaridar Daily Trust a Najeriya ta rawaito cewa a watannin shida na farkon wannan shekarar gwamnati ta biya tallafin naira tiriliyan ɗaya da miliyan ɗaya domin cike gibin da masana'antar ke fuskanta, wannan ƙari ne kan tiriliyan huɗu.


