Sai da safe
Ƙarshen rahotonnin kenan a wannan shafi na ranar Laraba.
Muna tafe da wasu sababbi gobe da safe, amma za ku iya karanata waɗanda muka kawo a yau idan kuka duba ƙasa.
Umar Mikail ke cewa sai da safenku.
Wanan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Laraba 09/07/2025
Umaymah Sani Abdulmumin, Abdullahi Bello Diginza, da Umar Mikail
Ƙarshen rahotonnin kenan a wannan shafi na ranar Laraba.
Muna tafe da wasu sababbi gobe da safe, amma za ku iya karanata waɗanda muka kawo a yau idan kuka duba ƙasa.
Umar Mikail ke cewa sai da safenku.

Asalin hoton, Getty Images
Wata rundunar haɗin gwiwar jami'an tsaro ta Najeriya ta yi nasarar kashe 'yanfashin daji kusan 30 yayin wani samame da suka kai musu a ranar Talata.
Sai dai 'yansanda uku da sojoji biyu sun rasa rayukansu sakamakon ɓarin wutar da aka yi bayan 'yanbindigar sun kai hari yankunan Kadisau, da Raudama, da Sabon Layi na ƙaramar hukumar Faskari a jihar Katsina.
Wata sanarwa da Kwamashinan Tsaron na jihar katsina Nasir Mua’zu ya fitar a yau Laraba ta ce gwamnatin jihar na duba yadda za su taimaka wa iyalan jami'an da kuma yankunan da lamarin ya shafa.
A jiya Talata ne Gwamnan Katsina Dikko Umaru Radda ya ce galibin 'yanbindigar da suka addabi jihar tasa 'yan asalin jihar ne ba baƙi ba.

Asalin hoton, Dangote Refinery
Matatar mai ta Dangote za ta gina wani rumbun ajiyar man a ƙasar Namibiya domin adana ganga miliyan 1.6 na man fetur da dizel domin saayarwa a kudancin Afirka.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito wasu majiyoyi na cewa za a yi amfani da ma'adanar wajen yin hada-hadar fetur a ƙasashen Botswana, da Namibiya, da Zambiya, da kuma Zimbabwe.
Kazalika, Dangote na tunanin fara kai mai ƙasar Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.
Wani jami'in hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Namibiya ya tabbatar wa Reuters shirin, yana mai cea za a gina ma'adanar ne a yankin Walvis Bay.
Wata majiya ta bayyana a watan da ya gabata cewa matatar ta fara sayar da mai zuwa nahiyar Asiya, wanda shi ne zai zama karon farko da ta yi hakan a wajen nahiyar yammacin Afirka.
A Najeriya, hukumar babban birnin taraya na Abuja ta ɗauki matakin kama mabarata da ke gararamba cikin kwaryar birnin da kewaye.
Ministan Abuja Nyesom Wike ne ya bayar da umarnin yin kamen da kuma tayar da masu sayar da kayayyaki a wuraren da ba cikin kasuwa ba.
Hukumomi na cewa matakin zai kawar da yamutsi da kuma rashin tsari.

Asalin hoton, Reuters
Wata kotu a Sifaniya ta yanke wa tsohon kocin Real Madrid Carlo Ancelotti hukuncin shekara ɗaya a gidan yari saboda kauce wa biyan haraji game da kudaden da ya samu na haƙƙin mallakar hotonsa.
Kotun ta yi hukunci ne kan lamarin da ya faru a 2014 lokacin da yake horar da Real Madrid, in ji wani rahoton da aka fitar a yau Laraba.
Ancelotti, wanda ya horar da Real Madrid daga 2013 zuwa 2015 da kuma 2021 zuwa 2025, an taɓa wanke shi a irin wannan zargin a 2015.
Ya koma Landan a watan Mayun 2015 bayan da Real Madrid ta kore shi.
Sai dai a karkashin dokar Sifaniya, duk wani hukunci da ke kasa da shekara biyu idan bai shafi tashin hankali ba, yana da wuya a bukaci wanda ake tuhuma ba tare da an taɓa yanke masa hukunci a baya ba ya yi zaman gidan yari.
Mai shekara 66 ɗin da ya horar da Bayern Munich da Chelsea, shi ne na baya-bayan nan da hukumomin Sifaniya suka bincika da yanke hukunci kan zambar biyan haraji.

Asalin hoton, Reuters
Aƙalla mutum 95 ne suka mutu a lardin Kerr na jihar Texas da ke Amurka sakamakon ambaliyar ruwan da aka yi fama da ita tun daga makon da ya gabata.
Jimillar mutum 119 ambaliyar ta kashe bayan ruwan ya share yankunan jihar ranar Juma'a, a cewar hukumomi.
Shugaban 'yansandan lardin Kerr, Sheriff Larry, ya ce har yanzu akwai mutum 150 da ba a san inda suka shiga ba zuwa safiyar yau Laraba, ciki har da masu yawon shaƙatawa biyar da suka yi sansani a gefen Kogin Guadalupe.
Aƙalla yara 36 ne da manya 59 suka mutu a bala'in a lardin Kerr kaɗai, a cewar hukumomi.
Har yanzu ana ci gaba da aikin nemowa da ceto ta hanyar amfani da manyan motocin rusau, kamar yadda 'yansanda suka bayyana.

Asalin hoton, EPA
Mai gabatar da kara na kasar Mexico ya ce kotu ta yanke wa wani gungun mutum 10 na yanbindiga masu safarar miyagun kwayoyi hukuncin ɗaurin sama da shekara140 a gidan yari bayan samunsu da laifin kisa da kuma garkuwa da mutane.
An kama su ne a watan Satumban da ya gabata bayan musayar wuta da aka yi a wata gona.
Wakiliyar BBC ta ce mahukuntan sun bayyana cewa an yi amfani da gonar ne a matsayin cibiyar tilasta wa mutane shiga kungiyar Jalisco New Generation Cartel, daya daga cikin manyan gungun masu aikata laifuka a kasar.
Tun daga watan Maris din wannan shekarar, an ƙara kama wasu mutum 15 da suka hada da wani magajin gari da kuma jami'an 'yansanda.

Asalin hoton, Nigeria Immigration Service
Gwamnatin Najeriya ta ce ta damu game da matakin da Amurka ta ɗauka na taƙaita yawan adadin kwanakin biza da take bai wa 'yan Najeriya da ke neman zuwa Amurkar.
Wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta fitar a yau Laraba ta ce matakin "zai ƙuntata wa ɗalibai da 'yankasuwa da matafiya daga Najeriya".
A cewar sanarwar: "Wannan mataki ya saɓa da al'adar cuɗe ni in cuɗe ka, da daidaito, da kuma girmama juna da ƙasashe ƙawayen juna ke aiki da su."
Ta ƙara da cewa Najeriya ta shawarci Amurka ta sauya matakin "saboda ƙawance da aiki tare da kuma haƙƙin da ke kan ƙasashen biyu", yayin da take ci gaba yunƙurin sasanta lamarin ta hanyar difilomasiyya.
A jiya Talata ne ofishin jakadancin Amurka ya sanar cewa zai zaftare wa'adin biza da kuma dalilan bayar da bizar ga yawancin ƴan Najeriya.

Asalin hoton, @CCSoludo
Gwamanan jihar Anambra da ke kudancin Najeriya ya ce galibin waɗanda jami'an tsaro ke kamawa da aikata laifuka tsawon shekara uku da suka gabata ƴan kabilar Ibo ne mai rinjaye a jihar.
Charles Soludo ya bayyana hakan ne yayin wani taro da 'yan asalin jihar mazauna ƙetare suka gudanar a Amurka, inda ya yi watsi da zargin da ake yi wa Fulani makiyaya na aikata satar mutane a jihar.
"Yanzu shekara uku da wata uku kenan ina kan mulki. Idan muka kama masu laifi 100 to kashi 99 cikin 100 matasan ƙabilar Ibo ne," a cewar gwamnan.
"Karya da farfaganda ake yaɗawa cewa Fulani ne ke aikata laifukan. Waɗannan karerayin da ake yaɗawa su suka buɗe kofa ga matasanmu shiga satar mutane saboda ta fi kawo kuɗi kan sana'arsu ta 'Yahoo' da safarar ƙwayoyi."
Anambra na cikin jihohin kudu maso gabashin Najeriya da 'yanbindiga masu fafutikar kafa ƙasar Biafra suka dinga hana mutane fita harkokinsu duk ranar Litinin a baya domin nuna ɓacin ransu kan kamawa da kuma tsare jagoransu Nnamdi Kanu da gwamnatin tarayya ta yi.

Tsohon shugaban jam'iyyar APC mai mulki, Abdullahi Ganduje, ya kama aiki a matsayin shugaban hukumar gudanarwar ma'aikatar kula da filayen jirgin sama ta Najeriya, FAAN.
Gbenga Saka, mataimaki na musamman ga ministan ma'aikatar a fannin yaɗa labarai, Gbenga Saka ne ya tabbatar da hakan a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X.
An yi bikin raka shi Ofis a Abuja, makonni bayan Ganduje ya sauka daga shugabancin jam'iyyar APC.

Mai magana da yawun tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce babu wani rashin jituwa tsakanin mai gidansa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Mal Garba Shehu, Ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da BBC game da wani littafi da zai kaddamar a yau Laraba kan irin yadda suka yi aiki da Shugaba Buharin mai taken “According to the President: Lessons from a presidential spokesman’s experience.”
Garba Shehu ya ce akwai jita-jita ce irinta mutane da yaɗ abubuwa da basu da tabbas a kai.
Da aka yi masa tambaya kan me ya sa Buhari baya hallatar taruka ko tsokaci kan wasu abubuwa na gwamnati sai Malam Garba Shehuu ya ce; "Buhari ba mutum ba ne me son shiga abin da bai shafe shi ba, sannan yana da dalilansa na wasu matakan da yake ɗauka idan aka tuntuɓemu za mu ba da amsa".
Sannan game da littafin da ya rubuta ya ce yana ganin ya kamata mutane su fahimci wane ne Buhari da tsarin ayyukansa, ganin akwai mumunan fahimta da ake yi wa tsohon Shugaban.
Ya ce Allah ya ba shi damar aiki a fadar gwamnati, kuma tsawon shekarun da ya yi na aiki akwai darrusa da dama da suka koya da ya kamata na baya su sa ni.
Sannan matasa da masu karatun jarida akwai abubuwan koyo sosai daga rayuwar Buhari da ayyukansu a fadar gwamati.
Sannan littafi ya bayyana wane ne shugaba Buhari, tsarinsa da yanayin aikinsa, ganin ana yawaita samu masu kushe shi da cewa me ya yi a shekaru takwas da mulkinsa.
Littafi ya yi bayyani kan rayuwarsu ta Villa da fito da bayanai na gaskiya kan wasu zarge-zargen da aka rinka yi wa shugaban, kama daga batun tsaro, diflomasiyya da wasu batutuwa masu muhimmanci.
Ya ce karanta wannan littafi sai sake gamsar da al'umma fahimtar wane ne ainihn tsohon shugaba Buhari.
Sannan ko yanzu da aka ga yana kame jikinsa, kokari ne na ba wa kowa dama da kau da kai, saboda ba ya son shishigi kan wasu lamura da ba su shafe shi fa.
A saurari tattaunawar da muka yi da Garba Shehu a kasa
Fiye da mutane dari ne suka samu raunuka sakamakon wata gobarar daji da ta tashi wajen birnin Marseille, birni na biyu mafi girma a kasar Faransa.
Ministan harkokin cikin gida, Bruno Retailleau, wanda ya ziyarci yankin, ya ce ba a kammala shawo kan gobarar ba, amma ana kan kokarin yin hakan.
Gobarar ta tilasta rufe filin tashi da saukar jiragen sama na Marseille na tsawon sa'o'i a jiya Talata, yayan da aka soke tashin jirage sama da hamsin.
Tashin Gobarar daji ya yawaita a cikin 'yan kwanakin nan a kudancin Faransa, sakmakon matsanancin zafi da aka yi fama da shi a yankin.

Asalin hoton, Ruto/Facebook
Shugaban Kenya ya tsawatar da masu zanga-zangar adawa da gwamnati, inda ya yi barazanar ɗaukar duk wani mataki da ya wajaba domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
William Ruto ya ce duk wanda ya aikata tashin hankali ko ya kai hari kan jami’an tsaro, ya cancanci a harbe shi a ƙafa.
Wakilin BBC ya ce shugaba Ruto a jawabinsa na farko tun bayan zanga-zangar da ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, ya zargi abokan adawarsa da ƙoƙarin kifar da gwamnatin sa.
Ruto ya ce hakan daidai yake da ta’addanci da kuma ayyana yaƙi.
Hukumar kare haƙkin ɗan adam ta ƙasar Kenya ta ce mutane 31 ne suka mutu, fiye da 100 kuma sun jikkata a arangamar.

Jigo a babbar jam’iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ya ce zai bai wa shirin hadakar ‘yan hamayya cikakken haɗin kai da goyon baya don tabbatar da cewa an kawar da jam'iyyar APC a babban zaɓen 2027.
Sule Lamido, ya ce yana cikin jam'iyyar PDP daram amma zai yi wa jam'iyyar ADC aiki kamar yadda Nyesom Wike, ya ke yiwa jam’iyyar APC aiki alhali kuma ɗan PDP ne.
Tsohon gwamnan na Jigawa ya ce akwai rainin hankali dangane da yadda ake tafiyar da harkokin siyasa da abin da Wike ya ke musu a PDP, don haka shi ma dole ya marawa ADC kuma babu wanda zai rabashi da PDP.
Sule ya nuna cewa halin da Najeriya ke ciki a yanzu ba lokaci ba ne na nuna ɓangaranci ba, lokaci ne na duba wane ne ya cancanta a mara masa baya ba tare da la'akari da jam'iyya ba.
Ya ce batun Jam'iyya ya haifar da tarin kalubale da matsaloli na ɓangaranci da rabuwar kawuna a Najeriya wanda dole ne a warware hakan.
Ya ce duk matsalolin PDP haddasata aka yi, don haka babu inda zai je, kuma babu wanda ya ke tsoro ko nuna munafurci.
Ya ce abubuwa da dama ana sa son zuciya a ciki, don haka shi ya san tsarin da zai bi saboda al'umma ce a gabansa. Kuma dole ya yi aiki domin kare PDP da bai wa ADC ƙasar.
A saurari cikakkiyar tattaunawar a kasa

Gwamnan Katsina Umaru Dikko Radda ya ce galibin 'yan bindigar da suka addabi jiharsu 'yan asalin jihar ne ba wai baƙi ba.
Gwamna Radda ya shaida hakan ne a wata tattaunawa da kafar talabijin ta Channels a Najeriya kan matsalolin tsaro da hanyoyin kawo karshen 'yanbindiga.
Ya ce galibin 'yan bindigar sun fito ne daga asalin yankunan da matsalolin tsaron ya addaba. Kuma mun san iyayensu da kakaninsu kuma tare muke rayuwa, in ji Dikko.
A cewarsa, matsalolin tsaron sun tilastawa gwamnatinsa kafa jami'an tsaron sa-kai a yankunan domin taimaka musu wajen samun sauki.
Dikko Radda ya ce abu ne mai sauki ba, amma suna cigaba da aiki da al'umomin waɗannan yankunan wajen sake fahimtar matsalolin domin ganin yadda za a daƙile matsalar baki ɗaya.
A cewar gwamnan, babu wani cigaba da za a samu a yankunan da matsalolin tsaron ya addaba muddin ba a samu sauƙin yanayin da ake ciki ba.
Aƙalla mutum biyu ne suka mutu yayinda wasu da dama suka jikkata sakamakon wasu girgizar ƙasa da suka auku a ƙasar Guatemala.
Tun da farko an fara samun girgizar a kusa da babban birnin ƙasar da yammacin jiya Talata, kafin daga bisani lamarin ya bazu zuwa wasu sassa da dama a fadin ƙasar.
Hukumar kula da bala'o'i ta Guatemala ta ce sama da gidaje arba'in ne suka lalace kuma mutane da dama na kwance a asibiti.

Asalin hoton, Getty Images
Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, UAE ta sake sanya wasu dokoki masu tsauri ga 'yan Najeriya da ke neman bizar shiga ƙasarta domin yawon buɗe ido ko ziyarar wucin-gadi.
Sanarwar da ƙasar ta fitar ta haramta bai wa 'yan Najeriya bizar wucin-gadi.
Sannan ɗuk wani ɗan Najeriya mai shekaru 18 zuwa 45 ba za a ba shi bizar shiga ƙasar ba, sai tafiyar ta kasance da iyali.
Wannan na zuwa ne kusan shekara ɗaya da UAE da Najeriya suka shawo kan matsalar haramcin bizar na shekara biyu da aka kakabawa 'yan Najeriyar.
Amma dage haramcin ya zo da dokoki masu tsauri yanayin da ala tilas ya takaita wa 'yan Najeriya shiga ƙasar.
Rahotanni na cewa a kullum batun samawa 'yan Najeriyar bizar UAE na kara zama matsala cike da kalubale.
A yanzu dai wannan sabon doka na nufin an soke ba wa 'yan Najeriya bizar wucin-gadi baki ɗaya
Sannan ga wanda ya haura shekara 45 idan yana neman biza sai ya gabatar da takardar bayanan asusun ajiyarsa na banki na tsawon wata shida, wanda zai nuna yana da kuɗaɗen da suka kai dala dubu 10 a lokacin neman bizar.
Sai kuma bukatar gabatar da Otel din da mutum zai yi masauki da kuma wasu bayanai na fasfo.

Asalin hoton, Getty Images
Kamfanin matatar man Dangote ya rage farashin litar mai daga ₦840 zuwa ₦820.
A wata sanarwar da kamfanin ya fitar jiya Talata, rage naira 20 kan kowacce lita guda na da alaka da sauyin da aka samu na farashin mai a kasuwanni duniya.
Ko a watan jiya na Yuni sai da kamfanin ya rage farashi daga ₦880 zuwa ₦840.
Gidajen mai irinsu MRS da Ardova da Heyden da sauransu da ke da yarjejeniya ta musamman da kamfanin ana sa rai su rage farashinsu ya tafi daidai da yadda matatar ke sayar da feturin.
Wannan sauyin farashi da ake samu daga kamfanin Dangote lokaci zuwa lokaci na yawaita haifar da cece-kuce da martani daga sauran 'yan kasuwa da ke harkar man fetur.

Asalin hoton, Getty Images
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce ganawar da ya yi da Donald Trump a fadar White House, ta mayar da hankali ne kan kuɓutar da mutanen da ake garkuwa da su a Gaza.
Wannan dai shi ne karo na biyu da shugabannin biyu ke ganawa cikin kwanaki biyu don tattaunawa kan kokarin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.
An dai kasa cimma matsaya a tattaunawar da aka yi tsakanin Hamas da Isra'ila a Qatar, amma wakilin Mista Trump na musamman, Steve Witkoff, ya ce yana fatan nan da yan kwanaki masu zuwa za a cimma yarjejniya.
Ya nuna cewa "muna fatan nan da karshen wannan makon za mu cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwana sittin inda za a sako mutane goma daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su Gaza".

Asalin hoton, Getty Images
A yau Laraba ake saran shugaba Trump na Amurka zai soma ganawa da wasu shugabannin Afirka biyar da ya gayyata fadar gwamnatin ƙasar ta White House.
Shugabannin sun haɗa da na Senegal da Liberia da Guinea-Bissau da Mauritania da Gabon.
Sanarwar da gwamnatin Amurka ta fitar na cewa ganawar za ta mayar da hankali ne kan batun kasuwanci da tsaro da kuma wasu batutuwa na diflomasiya.
Kuma tun daga yau 9 ga wata za a kai har 11 ga watan Yuli ana tattaunawa kafin daga bisani a shirya liyafar cin abinci.
Wannan na zuwa ne yayin da Trump ke cigaba da daukan matakai masu tsauri na hana baƙi da sauran masu zuwa ci-rani Amurka.
Shugaban dai na cigaba da sanyawa wasu ƙasashen Afirka haramci biza, da kuma taƙaitawa wasu ƙasashen wa'adin bisa da zaman ƙasar.