Shugabannin Turai sun nemi tsagaita wuta a Ukraine tare da jaddada tabbacin tsaronta

Asalin hoton, Getty Images
Shugabanni Turai sun bada kyakyawan shaida kan tattaunawarsu da shugaba Trump, yayinda suke jadadda alfannun tsagaita wuta cikin gaggawa a Ukraine.
Ƙasar Jamus, ta ce za ta bai wa Ukraine duk wata gudunmawa mafi dacewa, kuma za ta soma tattaunawa da Amurka kan tabbacin tsaron ƙasar.
Sannan babu batun Ukraine ta sadaukar da wani yanki nata.
Firaministan Burtaniya Keir Starmer ya nuna buƙatar ganin an bai wa Ukraine tabbacin tsaro.
Ita ma ƙasar Faransa, a ta bakin shugabanta Macron, na cewa Vladimir Putin bai nuna alamar dagaske yake yana son yaƙin ya zo ƙarshe ba, don haka dole Turai su tabbatar da tsaron Ukraine saboda gaba.


