Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 19/08/2025.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Isiyaku Muhammed da Aisha Babangida

  1. Hare-hare sun tilastawa MSF dakatar da wasu ayyukanta a Darfur

    An tilastawa ƙungiyar likitoci ta Médecins Sans Frontières (MSF) rage tawagoginta tare da dakatar da duk wasu ayyuka a asibitin da ƙungiyar ke tallafawa a jihar Darfur ta tsakiya, ta ƙasar Sudan, sakamakon wani mummunan hari da aka kai a cikin cibiyar a daren asabar ɗin da ta gabata.

    Harin ya yi sanadin mutuwar mutum ɗaya, sannan wasu biyar suka jikkata, ciki har da ma'aikacin ma'aikatar lafiya.

    Wannan dakatar da ayyukan jinya na zuwa ne a lokacin ɓarkewar cutar kwalara.

    MSF ta bayyana cewa ba za ta iya ci gaba da ayyukanta ba har sai dukkan ɓangarorin sun ba da tabbacin bayar da ingantaccen tsaro don kare ma'aikata da marasa lafiya.

    Tun a ranar 1 ga watan Agusta, MSF ke jagorantar agajin gaggawa na yaƙi da cutar kwalara a asibitin Zalingei, inda ta kula da marasa lafiya 162 a cikin kwanaki 16 kacal, tare da haɗin gwiwar Ma'aikatar Lafiya ta Jihar.

    Tuni dai cutar kwalara ta yio sanadiyar mutuwar mutane bakwai, kuma asibitin Zalingei ne kaɗai wurin da aka tanadar don kula da masu fama da munanan cututtuka a jihar Darfur ta tsakiya.

  2. An tsare tsohon Firaministan Mali bisa zargin cin hanci da rashawa

    Ana tuhumar tsohon Firaministan Mali Choguel Kokalla Maiga da laifin almubazzaranci da dukiyar jama'a da kuma buga takardun bogi.

    An tsare Mista Maiga’s ne a ranar Talata 19 ga watan Agusta, a yayin da ake ci gaba da da gwamnatin mulkin sojin Mali ke ci gaba da murkushe yan siyasa masu sukar gwamnati.

    Maiga wanda ya riƙe mukamin firaminista daga shekarar 2021 har zuwa lokacin da aka kore shi a ƙarshen shekara ta 2024, a baya ya soki gwamnatin mulkin sojan da ta jinkirta dawowar mulkin farar hula.

    Lauyansa, Cheick Oumar Konaré, ya bayyana lamarin a matsayin bita-da-ƙullin siyasa.

    Kamen dai ya biyo bayan tsare wasu jami'an soji sama da 50 da wani ɗan kasar Faransa a baya-bayan nan, waɗanda ake zargi da yunƙurin ta da zaune tsaye.

    Janar Assimi Goïta, wanda ya hau kan karagar mulki a shekara ta 2020, a baya-bayan nan ya zartar da wata doka da ta ba shi damar ci gaba da mulki har sai yadda hali ya yi, inda ya kafa hujja da yaƙin da ake yi da masu tayar da ƙayar baya a sassa daban-daban na ƙasar.

  3. Isra'ila ta buƙaci a sako dukkan mutanenta da aka yi garkuwa da su a lokaci guda

    Wani jami'in Isra'ila ya ce Isra'ila na buƙatar a sako dukkan mutane 50 da aka yi garkuwa da su a Gaza, yana mai nuna shakku kan ko za ta amince da sabuwar daftarin tsagaita wuta na kwanaki 60 da Hamas ta amince a ranar Litinin.

    Matsayin Isra'ila ya kasance "bisa ƙa'idojin da majalisar ministocin ƙasar ta gindaya na kawo ƙarshen yaƙin", in ji jami'in, ba tare da yin watsi kai-tsaye da daftarin da ƙasashen Qatar da Masar suka gabatar ba.

    Daftarin, wanda ke bayar da shawarar a sako kusan rabin mutanen da aka yi garkuwa da su, ''kusan iri ɗaya ne da " da shawarar Amurka da Isra'ila ta amince da ita a baya, in ji Qatar.

    Majiyoyin Falasdɗinawa sun ce za a miƙa waɗanda aka yi garkuwa da su 10 masu rai da kuma matattu 18 yayin da ɓangarorin za su ci gaba da tattaunawar tsagaita wuta na dindindin da kuma dawo da sauran waɗanda aka yi garkuwa da su.

    Isra'ila ta yi imanin cewa 20 daga cikin 50 wadanda aka yi garkuwa da su ne ke raye bayan watanni 22 ana gwabza yaƙi.

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu bai ce uffan ba a bainar jama'a game da daftarin ba, sai dai a ranar Litinin ya ce Hamas na fuskantar tsananin matsin lamba.

    A cikin makon nan ne ake sa ran majalisar ministocin Isra'ila za ta amince da shirin sojojin ƙasar na mamaye birnin Gaza baki ɗaya, inda tuni hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da kai wa suka sanya dubban mutane tserewa daga gidajensu.

  4. Ƴanbindiga sun kashe masallata 15 a Katsina

    Wasu ƴanbindiga sun kashe mutum 15 a wani hari da suka kai kan wani masallaci a Unguwan Mantau da ke yankin ƙaramar hukumar Malumfashi a jihar Katsina.

    Kakakin rundunar yansandan jihar, DSP Abubakar Sadik Aliyu ya tabbatar wa BBC faruwar lamarin, inda ya ce lamarin ya faru ne lokacin da mutanen ke tsaka da sallar asuba.

    DSP Aliyu ya ce ya ce harin na ramuwar gayya ne kan mazauna unguwar bayan da suka tsare unguarsu daga harin ƴanbidigar a ƴankwanakin baya-bayan nan.

    Tuni dai gwamnatin jihar ɗauka matakan tsaro domin daidaita al'amura a garin, kamar yadda kwamishin tsaro da al'amuran cikin gida na jihar ya bayyana.

    Ya ce yanzu jami'an tsaro na cikin garin Unguwan Mantau domin maido da zaman lafiya.

  5. Starmer ya yaba da ci gaban da aka samu a tattaunawar Ukraine

    Sir Keir Starmer ya kira ƙudurin shugaban Amurka Donald Trump na bayar da tabbacin tsaro ga Ukraine a matsayin ci gaba, yayin da ya yaba da yunkurin da ake yi na tabbatar da ganawa tsakanin Volodymyr Zelensky da Vladimir Putin.

    Firaministan ya halarci taron shugabannin a fadar White House ranar Litinin, bayan da ya katse hutun da ya ke yi a Scotland tare da iyalinsa.

    Ya jagoranci wani taro na kawancen ƙasashen Turai da ƙungiyar Commonwealth ranar Talata don tattaunawa da shugabannin kan matakai na gaba.

    Shugabannin sun kuma tattauna kan matakan da za a ɗauka na ƙara matsawa Putin lamba, ciki har da takunkumai.

    A nasa ɓangaren, Trump ya shaidawa Fox News cewa Ukraine "ba za ta shiga ƙungiyar tsaro ta NATO ba", amma ya yi nuni da cewa sojojin Turai za su kasance a Ukraine don daƙile duk wani harin da Rasha za ta kai nan gaba.

  6. Nakiya ta kashe mutum ɗaya tare da jikkata shida a Borno

    A Najeriya, Rundunar ‘yan sandan ƙasar ta tabbatar da mutuwar wani ƙaramin yaro tare da jikkatar mutum 4 a lokacin da wani bam haɗin gida ya fashe a ƙaramar hukumar Konduga ta jihar Borno.

    Lamarin ya auku a gefen hanyar da ake aikin zuba kwalta a babbar hanyar mashigar Konduga.

    Kakakin rundunar ƴansandan jihar Borno, ASP Nahum Kenneth Daso ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ce mutum ɗaya ne ya mutu bayan nakiyar ta fashe da yammacin ranar Lahadi.

    "Mun samu labarin cewa yaran sun haƙo nakiyoyin ne suka tafi da su gida. Sai suka fashe, inda a nan take mutum ɗaya ya rasu, sannan ya jikka wasu mutum shida," in ji shi.

  7. Dole ne fasinjoji su kashe waya bayan shiga jirgi - NCAA

    Sakamakon wasu abubuwa marasa daɗi da suka auku a filayen tashi da saukar jiragen sama na baya-bayan nan, hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Najeriya (NCAA) ta bayar da umarnin cewa dukkan fasinjojin su kashe wayarsu a lokacin da suka shiga jirgin sama.

    A wani taron manema labarai a Abuja ranar Talata, Darakta Janar na hukumar ta NCAA, Chris Najomo, ya ce dole ne fasinjoji su kashe duk wayoyi a lokacin da jirage ke sauka ko tashi a dukkan filayen jiragen saman Najeriya.

    Umarnin da hukumar ta bayar ya biyo bayan ce-ce-ku-cen da aka yi a baya-bayan nan da ya shafi wata fasinja mai suna Comfort Emmanson, da ma’aikaciyar kamfanin jirgin sama na Ibom Air.

    Shugaban hukumar ta NCAA ya ce hakan zai dakatar saɓanin da ake samu a ƙa’idojin kamfanonin jiragen sama, waɗanda suka haifar da ruɗani a tsakanin fasinjoji.

    “A matsayin hanyar da za a bi don guje wa ruɗani, yanzu dole ne a kashe duk wayoyi da duk wasu na'urorin laturoni na tafi-da-gidanka a lokacin da jirgin ke sauka ko tashi a dukkan kamfanonin jiragen sama na Najeriya. A kashe wayar baki ɗaya, babu sauran batun tsarin kashe layi na 'flight mode'', kamar yadda ya bayyana.

    "Saboda haka ana buƙatar kamfanonin jiragen sama na Najeriya su yi gyara ga kundin tsarin aikinsu don tabbatar da wannan doka sannan su miƙa ga hukumar NCAA domin neman amincewa," in ji shi

  8. An zargi ɗan sarauniyar Norway da aikata fyaɗe

    Wani mai gabatar da ƙara ya ce ana tuhumar babban ɗan gimbiya mai jiran gadon sarautar Norway da laifuka 32 da suka haɗa da laifuka huɗu na fyaɗe.

    Laifukan da ake tuhumar Marius Borg Høiby, mai shekaru 28 da aikatawa sun haɗa da cin zarafin wata tsohuwar abokiyar zamansa da kuma keta umarnin rashin kusantar wata tsohuwar abokiyar tasa.

    An haife shi ne kafin Gimbiya Mette-Marit ta auri Yarima Haakon, wanda shi ne sarkin Norway mai jiran gado.

    Mista Høiby ya musanta zarge-zargen da ake yi masa, amma yana shirin amsa wasu ƙananan laifuka idan aka fara shari'ar, kamar yadda lauyansa Petar Sekulic ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

    Zai iya fuskantar ɗaurin shekara 10 a gidan yari idan aka same shi da laifi a tuhume-tuhumen da ake yi masa na aikata manyan laifuka.

    An ce ana zarginsa da aikata fyaden ne har sau huɗu tsakanin shekarar 2018 zuwa 2024, inda ake zargin ɗaya daga cikinsu ya faru ne bayan kama shi, a cewar kafar yaɗa labarai ta NRK.

    Mai gabatar da ƙara ya ce za a iya gudanar da shari'ar a watan Janairu mai zuwa kuma za a shafe makonni shida ana yi.

  9. Rundunar ƴansandan Kano za ta ladabtar da jami'anta da aka gani a bidiyon karɓar kuɗi

    Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta yi ƙarin bayani kan wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke nuna jami’an wasu ƴan sanda biyar sanye da kayan sarki suna taimaka wa wani ɗan siyasa wajen shirya jama’a domin karɓar kuɗi.

    Wata sanarwa da ta fitio daga ofishin jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ta ce, bayan gudanar da cikakken bincike, rundunar ta tabbatar da aukuwar lamarin bayan wani biki da aka gudanar a ɗakin taro na Coronation dake fadar gwamnatin jihar Kano a ranar Alhamis 10 ga watan Yuli, 2025, wanda bai da alaƙa da zabukan cike gurbi da aka gudanar a ranar 16 ga watan Agustan 2025.

    Sanarwar ta ƙara da cewa binciken ya nuna cewa an tura jami’an wajen taron ne domin su tabbatar da tsaro, amma daga bisani bidiyonsu ya bayyana inda suke aikata abin da rundunar bayyana a matsayin rashin ɗa'a.

    Rundunar ƴan sandan ta tabbatar wa da cewa ana ɗaukar matakan ladabtar da jami’an domin kiyaye mutunci da ƙwarewar rundunar ƴan sandan Najeriya.

  10. Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta nemi da a riƙa mutunta shari'a a Najeriya

    Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'adam ta Duniya ta IHRC-RFT a Najeriya ta bayyana damuwarta kan yadda ake samun ƙaruwar amfani da umarnin kotu wajen ƙauce wa shari’a bayan aikata laifuka ko tauye haƙƙin mutane inda take neman a riƙa mutunta shari'a a ƙasar.

    Ƙungiyar ta lura cewa amfani da umarnin kotu a Najeriya wajen ba bisa ƙa'ida ba na neman ya zama ruwan dare wanda ke hana jami’an tsaro daga kama ko binciken masu aikata laifi..

    Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da daraktan ƙasa ta ƙungiyar Amb. Abdullahi Bakoji Adamu ya fitar.

    Sanarwar ta ce wannan dabi’a tana barazana ga amincin tsarin shari’a kuma tana rage ikon jami’an tsaro wajen gudanar da aikinsu.

    IHRC-RFT ta bayyana cewa ba ta kira a hana umarnin kotu ba. Sai dai tana buƙatar a tabbatar cewa shari’a da adalci da gaskiya su ne ke jagorantar yadda ake bayar da irin waɗannan umarni, domin kada wani ya yi amfani da dokoki wajen tauye haƙƙin wasu.

    "Amfani da tsarin shari’a ba bisa ƙa’ida ba ya saɓa wa dokokin kare hakkin dan adam na kasa da kasa wadda ta tanadi cewa kowa yana da daidaito a gaban doka da samun kariya ba tare da bambanci ba.

    A matsayin wani bangare na yaƙin neman adalci, IHRC-RFT ta aike da wasiƙu ga ministan shari’a da babban lauyan tarayya da kuma babban alƙalin Najeriya, tana kira da su su gudanar da bincike da duba yadda ake amfani da umarnin kotu a ƙasar.

    Ƙungiyar ta kuma buƙaci su ƙarfafa hanyoyin da ke tabbatar da cewa umarnin kotu ba za su zama kayan toshe shari’a ba sannan su haɗa kai da ɓangaren majalisa da na shari'a da na zartarwa da jami’an tsaro domin tabbatar da tsarkake tsarin shari’ar Najeriya bisa ƙa’idojin kare haƙƙin ɗan adam na duniya.

  11. Rasha ta kai mana hare-hare a daren jiya - Ukraine

    Ukraine ta ce Rasha ta ƙaddamar da wani mummunan hari a jiya da daddare kan cibiyar makakamashinta da ke tsakiyar yankin Poltava.

    Gwamnatin ƙasar ta ce an kai harin ne kan cibiyoyin tace mai da iskar gas.

    Hayaƙi ya kuma turnuƙe sararin samaniyar Kremenchuk, birni na biyu mafi girma a yankin Poltava, inda nan ma rahotannin suka ce harin ya lalata wata matatar mai.

    Wakilin BBC ya ce a yayin da ake tsaka da lalubo maslahar diflomasiyya, ana kuma ci gaba da kai hare hare. A gefe guda kuma ɓangarorin biyu sun yi musayar gawarwakin mutanen su, akasari sojoji.

  12. Trump ya ce ƙasashen turai za su tura dakaru Ukraine

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce manyan ƙasashen Turai kamar Faransa da Jamus da Birtaniya za su aika dakarunsu Ukraine domin tabbatar da an cimma duk wata yarjejeniyar zaman lafiya.

    Mista Trump ya kuma shaida wa gidan talibijin na Fox news cewa ya yi tunanin Vladimir Putin, zai yi yunƙurin ganin an kawo ƙarshen yaƙin saboda watakil ya gaji da yaƙin.

    Sai dai ya ce akwai yiwuwar shugaban na Rasha bai damu da wata yarjejeniya ba.

    Trump ya kuma sake nanata cewa Ukraine ba za ta shiga ƙungiyar NATO ba.

  13. Isra'ila na nazarin shiga yarjejeniyar tsagaita wuta da Hamas

    Gwamnatin Isra'ila ta ce tana nazarin daftarin sake shiga yarjejeniya da ƙungiyar Hamas domin tsagaita wuta a Zirin Gaza, bayan ƙungiyar ta amsa buƙatar hakan.

    Sabuwar yarjejeniyar za ta ƙunshi tsagaita wuta ta kwana 60, tare da musayar Isra'ilawa da Hamas ke garkuwa da su a Gaza da wasu fursunoni.

    Qatar ta tabbatar da ci gaban da ake samu game da tattaunawar, wadda Amurka ta shirya.

    Masar da Qatar na yunƙurin tabbatar da yarjejeniyar ne kafin Isra'ila ta ƙaddamar da yunƙurinta na mamaye Gaza.

    Hukumomi a Falasɗinu un ce daga cikin yarjejeniyar, Isra'ila za ta janye sojojinta da nisan kilomita daga bakin iyakar shiga ƙasar.

    Wakiliyar BBC ta ce ana sa ran cikin kwanaki sittin ɗin ƙarin kayan agaji za su sami shiga Gaza, kuma za a soma tattauna yadda za a kawo ƙarshen yaƙin.

  14. Da wahala Kwankwaso ya goyi bayan Tinubu a 2027 - Buba Galadima

    Jigo a jam'iyyar NNPP, kuma na hannun tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Buba Galadima ya ce zai yi wahalar gaske Kwankwaso ya haɗa hannu da jam'iyyar APC domin samun nasarar Bola Tinubu a babban zaɓen shekarar 2027.

    Buba Galadima ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da tashar Channels a shirinta na Politics Today wanda aka yi a ranar Litinin, inda ya ce gwamnatin Tinubu tana takalar Kwankwaso, musamman wajen goyon bayan Sarki Aminu Ado Bayero, duk da gwamnatin jihar ƙarƙashin Abba Kabir Yusuf ta cire shi.

  15. Yau ce ranar Ɗaukar hoto ta duniya

    A yau 19 ga watan Agusta ne ake bikin ranar hoto ta duniya, ranar da aka ware domin girmama tarihi da muhimmancin ɗaukar hoto.

    Ɗaukan hoto abu ne na tarihi da zai kasance tare da mu har abada.

    A wannan rana, ana ƙarfafa wa masu ɗaukan hoto su nuna basirarsu da raba ayyukansu na ɗaukan hotuna, kuma su fahimci girman ikon da hoto ke da shi wajen adana abubuwan da suka faru.

    Daga wayoyin hannu zuwa manyan kyamarori, ɗaukan hoto na ci gaba da zama hanya mai muhimmanci ta bayyana tunani da tarihi da kuma al’adun mutane.

    Ranar tana tunatar da mu cewa kowanne hoto yana da labari da ma'ana a tattare da shi.

  16. Ana takun-saƙa tsakanin manyan sarakunan Yarabawa biyu

    A ranar Litinin ne Alaafin na Oyo Oba Akeem Owoade ya bai wai Ooni na Ife Oba Enitan Adeyeye Ogunwusi wa'adin sa'o'i 48 domin soke muƙamin sarauta na masauratar Okanlomo da ake zargin ya bai wa wani attajiri a Ibadan mai suna Dotun Sanusi, duk a ƙasar Yarabawa

    Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan harkokin ƴada labarai na Alaafin, Bode Durojaiye ya fitar.

    Sanarwar ta ce: “Yanayin yanzu da ake ciki shi ne ya wajabta wa Alafin na Oyo ya bai wa Ooni na Ife wannan umarnin domin ya soke muƙamin sarautar da aka bai wa Injiniya Dotun Sanusi cikin sa'o'i 48 ko kuma ya fuskanci hukunci.”

    Sanarwar ta jaddada cewa, Alaafin ne kawai ke da ikon bai wa kowane mutum muƙamin sarauta da ya shafi duk fadin ƙasar Yarbawa wadda kotun ƙolin Najeriya ta tabbatar da hakan

    “Takardar muƙamin da aka gabatar wa Oba Ogunwusi lokacin da aka naɗa shi ya takaita ikon ƙarfinsa kawai ga ƙaramar hukumar Oranmiyan, wadda yanzu ta rabu zuwa ƙaramar hukuma uku da suka haɗa da Ife ta Tsakiya da Arewacin Ife da kuma Kudancin Ife.” sanarwar ta ƙara da cewa.

    Har yanzu dai fadar Ooni na Ife bata mayar da martani kan wannan sanarwar ba.

  17. An kashe ma’aikatan agaji 383 a 2024, adadin da ya ninka na 2023 - MDD

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce an kashe kashi mai yawa na ma'aikatan agaji a yaƙe-yaƙe a bara, kuma alƙaluman wannan shekarar na da tayar da hankali matuƙa.

    Yayin da yau take ranar agaji ta duniya, MDD ta ce ma'aikatan agaji 383 aka kashe a shekarar 2024, alƙaluman da ya ninka na shekarar baya, galibi a yaƙe-yaƙen Gaza da Sudan.

    Majalisar ta ce waɗanda ke rikici da juna galibi ke aikata kisan, sannan ga jikkata ma'aikata da kuma garkuwa da su.

    Ofishin jin-kai na MDD, ya ce waɗannan hare-hare kan jami'ansu abin tir da alla-wadai ne a idon duniya, musamman ganin ba a bi wa ma'aikatan hakkinsu.

  18. Tinubu ya umarci asibitocin tarayya su rage farashin wankin ƙoda

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya amince da rage farashin wankin ƙoda daga naira 50,000 zuwa naira 12,000 a manyan asibitocin tarayya a fadin ƙasar.

    Daniel Bwala, mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan Bayanan da suka shafi tsare-tsaren gwamnati ne ya bayyana hakan a shafin sada zumuntansa na X, inda ya ce matakin zai sauƙaƙa wa dubban marasa lafiya masu fama da ciwon ƙoda.

    An fara aiwatar da wannan mataki a manyan asibitoci kamar FMC Ebute-Metta da ke Lagos da FMC da ke Jabi a Abuja da UCH Ibadan da FMC Owerri da UMTH Maiduguri, yayin da za a ƙara wasu kafin ƙarshen shekara domin samun damar amfani da su a duk faɗin ƙasar.

    Shugaba Tinubu a baya ya amince da haihuwa ta hanyar tiyata kyauta a asibitocin gwamnati domin inganta lafiyar mata da rage mace-macen da za a iya hana faruwarsu.

  19. Hamas ta amince da sabon daftarin zaman lafiya kan Gaza, ana jiran martanin Isra’ila

    Ana dakon martanin Isra'ila a hukumance, bayan Hamas ta shaida cewa ta amince da sabon daftarin yarjejeniyar zaman lafiya da masu shiga tsakanin na ƙasashen Larabawa suka gabatar kan Gaza.

    Ƙasashen Qatar da Masar, na ƙoƙarin ganin sun samar da yarjejeniyar da za ta hana Isra'ila ƙaddamar da sabbin hare-hare na cikakken mamaya a Gaza.

    Majiyoyin Falasɗinawa sun tabbatar da cewa yarjejeniyar ta dawo da tsarin da Amurka ta gabatar na tsagaita wutan kwanaki 60, wanda a cikin kwanakin za a saki sauran 'yan Isra'ila da ke hannun Hamas -- sannan bangarorin biyu su cimma yarjejeniya ta kawo zaman lafiyar dindindin.

  20. Idan Jonathan ya tsaya takara a 2027 mutuncinsa zai zube - Shehu Sani

    Tsohon ɗan majalisar dattijan Najeriya, Sanata Shehu Sani ya ce rikicin da babbar jam'iyyar hamayya ta kasar, PDP ke fama da shi da ficewar wasu daga cikin 'yan majalisa da gwamnonin jam'iyyar zuwa APC, na daga cikin dalilan da suka sa, yake shawartar tsohon shugaban kasar Goodluck Ebele Jonatahan da kar ya tsaya takara a zaɓen 2027.

    Shehu Sani ya sheda wa BBC cewa shigar Jonatahn takarar na iya shafar mutunci da girmamawar da ya samu a ciki da wajen Najeriya.

    ''Na farko dai a shekarun baya kamar zaben 2019 da 2023 an yi irin wadannan kiraye-kiraye na jawo Jonathan ya sigo filin takara amma ya ja da baya, saboda ya hanga ya ga hadarin da ke tattare da hakan ta fuskar kare kimarsa,'' in ji Sani.