Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 19/08/2025.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Isiyaku Muhammed da Aisha Babangida

  1. Shugabannin Turai sun nemi tsagaita wuta a Ukraine tare da jaddada tabbacin tsaronta

    Shugabanni Turai sun bada kyakyawan shaida kan tattaunawarsu da shugaba Trump, yayinda suke jadadda alfannun tsagaita wuta cikin gaggawa a Ukraine.

    Ƙasar Jamus, ta ce za ta bai wa Ukraine duk wata gudunmawa mafi dacewa, kuma za ta soma tattaunawa da Amurka kan tabbacin tsaron ƙasar.

    Sannan babu batun Ukraine ta sadaukar da wani yanki nata.

    Firaministan Burtaniya Keir Starmer ya nuna buƙatar ganin an bai wa Ukraine tabbacin tsaro.

    Ita ma ƙasar Faransa, a ta bakin shugabanta Macron, na cewa Vladimir Putin bai nuna alamar dagaske yake yana son yaƙin ya zo ƙarshe ba, don haka dole Turai su tabbatar da tsaron Ukraine saboda gaba.

  2. 'Ya kamata China da Indiya su zama abokan hulɗa, ba maƙiya ba'

    Ministan harkokin wajen China, Wang Yi, ya ce ya kamata ƙasarsa da Indiya su mutunta juna a matsayin abokan hulda ba maƙiya ba.

    Wang Yi na waɗannan kamalai ne a birnin Delhi na Indiya lokacin ganawarsa da takwaransa na ƙasar, S. Jaishankar.

    Mista Wang ya kuma ce akwai buatar ƙasashen biyu su gina alaƙa ta fahimtar juna.

    Mista Jaishankar shi kuma ya ce dole a ɗau matakan sararawa juna kan iyaƙar da ke haifar da saɓanni a tsakaninsu.

    Ana kuma sa ran ganawar Wang da firaministan Indiya, Nerandra Modi nan gaba kaɗan, wanda ake saran shima zai je China ƙarshen wata.

    Kusan shekara huɗu yanzu dakarun China da Indiya ke rigima da juna a kan iyakar Ladakh.

  3. An kama ɗan tsohon shugaban Boko Haram Muhammad Yusuf a Chadi - AFP

    Hukumomi a ƙasar Chadi sun kama yaron shugaban ƙungiyar Boko Haram Muhamad Yusuf a ƙasar Chadi mai suna Muslim Mohammed Yusuf kamar yadda kamfanin dillanci labarai na AFP ya ruwaito

    An kama shi ne tare da wasu mutum biyar da ake zargin ƴan Boko Haram ne, ƙungiyar da mahaifinsa ya assasa a Najeriya a shekarun baya.

    Rundunar ƴansandan Chadi ta tabbatar da kama ƴan Boko Haram shida, amma ba ta iya tantance kasancewar ɗan Muhammad Yusuf a ciki ba, kamar yadda AFP ɗin ya ruwaito.

    Amma wata majiyar tsaro da kafar AFP ta zanta da su inda suka tabbatar mata da kama ƴan Boko Haram shida, ciki har da shi yaron shugaban ƙungiyar Boko Haram ɗin.

    "Ƴan Boko Haram shida aka kama, kuma ɗan tsohon shugaban Boko Haram na farko ne jagoransu."

    An fi sanin Muslim da sunan Abdrahman Mahamat Abdoulaye, kuma ƙani ne ga jagoran ISWAP Habib Yusuf, wanda aka fi sani da Abu Mus’ab Al-Barnawi.

    Haka kuma wani tsohon ɗan Boko Haram ya tabbatar wa AFP cewa lallai an kama Muslim a Chadi.

  4. Buɗewa

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Talata daga nan sashen Hausa na BBC inda za mu ci gaba da kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta irin su Facebook da Instagram da X da ma zaurenmu na Whatsapp domin karanta wasu labaran da tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.