Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wataƙil Onana ya je Inter Milan, Chelsea za ta ba da aron Sterling
Inter Milan na bibbiyar yadda lamaru ke kasancewa mai tsaron raga ɗan Kamaru, Andre Onana mai shekara 29, yayinda ake jita-jitar Manchester United za ta raba gari da shi. (Sun)
Chelsea ta shirya bada aron ɗan wasanta na Ingila, Raheem Sterling mai shekara 30, kuma tana son sayar da wasu 'yanwasa takwas kafin karshen kakar cinikin 'yanwasa.(Telegraph - subscription required)
Chelsea ta yi watsi da tayin da aka gabatar ma ta daga Bayern Munich kan ɗan wasan gaba a Faransa, Christopher Nkunku mai shekara 27. (Times - subscription required)
Newcastle za ta gabatar da tayin fam miliyan 35 kan ɗan wasan gaba a DR Congo, Yoane Wissa amma da alama Brentford ba za ta sayar da ɗan wasan mai shekara 28 ba, sai idan har ta samu mai maye gurbinsa. (Sun)
Crystal Palace na son cigaba da riƙe 'yan wasan Ingila biyu, Eberechi Eze mai shekara 27 da Marc Guehi mai shekara 25 - wayanda Tottenham da Liverpool rke hari. (Mirror)
Tottenham ta tuntuɓi Palace kan ko za ta sayar mata da Eze, kan kuɗin da ya kai fam miliyan 55. (Independent)
Ita kuma Palace na kokarin ganin ko za ta iya saye ɗan wasan Faransa mai shekara 20, Jeremy Jacquet domin ya maye gurbin Guehi. (Independent)
Aston Villa ta sa ɗan wasan gaba a Chelsea da Senegal, Nicolas Jackson mai shekara 24, cikin waɗanda take farauta amma za ta iya fuskantar kalubale daga Bayern Munich. (Florian Plettenberg)
Ɗan wasan Manchester United da Ingila, Jadon Sancho mai shekara 25, ya yi watsi da batun zuwa Roma, da ta shirya biyansa fam miliyan 20.(Talksport)
Kocin Arsenal Mikel Arteta na son sayen ɗan wasan gefe amma dole sai ya sayar da 'yanwasan sa kafin ya iya shiga wani ciniki. (Mirror)
Ɗan wasan Aston Villa da Jamaica, Leon Bailey mai shekara 28, na gab da tafiya Roma a matsayin aro. (Corriere dello Sport - in Italian)
Crystal Palace ta tuntuɓi Leicester kan cinikin ɗan wasan tsakiya a Moroko mai shekara 21, Bilal El Khannouss. (Athletic - subscription required)
Palace na duba yiwuwar saye ɗan wasan Wolves da Koriya ta Kudu, Hwang Hee-chan mai shekara 29. (Sun)
Napoli ta shirya shiga fafatawa a cikin ɗan wasan Manchester United da Denmark, Rasmus Hojlund mai shekara 22, wanda ke tattaunawa da AC Milan. (Sport Italia - in Italian),
Ɗan wasan tsakiya a Brazil, Douglas Luiz mai shekara 27, ya cimma yarjejeniya da Nottingham Forest amma yana jiran Juventus. (Corriere dello Sport - in Italian)
Tsohon ɗan wasan Liverpool da Arsenal, Alex Oxlade-Chamberlain ya kasance wanda Birmingham City ke hari daga Besiktas. (Mirror)
Leeds na gab da cimma yarjejeniya da AC Milan kan ɗan wasan gaba a Switzerland, Noah Okafor mai shekara 25, kan £17.2m (20m euros). (Florian Plettenberg)
Jamie Vardy mai shekara 38 na son zuwa Celtic kasancewa a yanzu ba shi da ƙungiya tun barowarsa Leicester a karshen kaka. (Sun), external
Haka zalika ɗan wasan na Ingila Vardy ya kasance wanda ƙungiyar Seria A Napoli ke farauta. (Mail)