Labarin wasanni daga 4 zuwa 10 ga watan Oktoban 2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Asabar 4 zuwa 10 ga watan Oktoban 2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Premier

    Asalin hoton, Getty Images

    Manchester United ta kuduri aniyar ci gaba da rike kyaftin din ta Bruno Fernandes mai shekaru 31 a kasuwar musayar 'yan wasa ta watan Janairu, duk da cewa kungiyoyin Saudiyya na son yin zawarcin dan wasan tsakiyar na Portugal. (Manchester Evening News)

    Napoli ce kan gaba wajen sayen dan wasan tsakiya na Manchester United da Ingila Kobbie Mainoo, mai shekara 20, a watan Janairu. (Tuttomercatoweb)

    Barcelona na shirin yin hamayya da Liverpool don siyan dan wasan bayan Faransa Dayot Upamecano, mai shekara 26, lokacin da kwantiraginsa zai kare a Bayern Munich a bazara mai zuwa. (Fichajes)

    Arsenal za ta amince da tayin kusan fan miliyan 30 kan Gabriel Jesus, mai shekara 28, wanda Everton ke zawarci. (Teamtalk)

  2. Slot ya yi rashin nasara uku a jere tun fara horar da tamaula

    Slot

    Asalin hoton, Getty Images

    Liverpool ta yi rashin nasara karo na uku a jere a bana a dukkan karawa, bayan da Chelsea ta doke ta 2-1 ranar Asabar a Premier League a Stamford Bridge.

    Caicedo ne ya fara ci wa Chelsea daga baya Liverpool ta farke ta hannun Gakpo a zagaye na biyu.

    Sai dai daf da za a tashi ne Chelsea ta kara na biyu ta hannun matashi Estevao.

    Tun farko Liverpool ta yi rashin nasara a hannun Crystal Palace 2-1 a Premier League, sannan ta yi rashin nasara 1-0 a gidan Galatasaray a Champions League.

    Da wannan sakamakon Liverpool ta koma ta biyun teburi da tazarar maki ɗaya tsakani da Arsenal mai jan ragama mai maki 16.

    Liverpool za ta buga wasan gaba da Manchester United a Premier League da karawar Champions League da Eintrach Frankfurt.

  3. Kuwait za ta karɓi bakuncin French Cup tsakanin PSG da Marseille

    PSG

    Asalin hoton, Getty Images

    Kuwait za ta karɓi bakuncin French Super Cup tsakanin Paris St Germain da Olympique de Marseille a farkon watan baɗi, in ji hukumar ƙwallon kafa ta Kuwait.

    Tuni shugaba, Sheikh Ahmad Al-Yousef Al-Sabah ya saka hannu kan kwantiragi da mahukuntan Ligue 1, inda aka tsayar da ranar 8 ga watan Janairu domin buga fafatawar a filin Jaber Al-Ahmad.

    PSG ta lashe French Super Cup a kowacce kaka uku baya, mai 13 jimilla.

    Ita kuwa Marseille uku ne da ita na baya bayan nan da ta ɗauka shi ne a 2011.

  4. Premier League

    Asalin hoton, Getty Images

    Manchester City na sa ido kan yanayin dan wasan bayan Atletico Madrid da Argentina Nahuel Molina, mai shekara 27 ke ciki. (Teamtalk)

    Crystal Palace na nuna sha'awar siyan dan wasan tsakiya na AZ Alkmaar Kees Smit, mai shekaru 19, wanda ya bugawa Netherlands wasa a matakin 'yan kasa da shekaru 19 kuma ya ja hankalin 'yan kallo daga Real Madrid, Barcelona, ​​Chelsea da Manchester United. (Mail)

    Tsohon kociyan Manchester United Erik ten Hag na iya komawa bakin aiki don maye gurbin Johnny Heitinga a tsohon kulob dinsa na Ajax bayan barin Bayer Leverkusen. (De Telegraaf)

    Crystal Palace na son dan wasan tsakiya na Japan Daichi Kamada, mai shekara 29, ya tsawaita zamansa a Selhurst Park da kwantiraginsa zai kare a bazara mai zuwa. (Sky Sports)

    Bayern Munich na daya daga cikin kungiyoyin da ke zawarcin dan wasan baya na Arsenal dan kasar Holland Jurrien Timber, mai shekara 24, wanda ya bude tattaunawa kan sabunta kwantaraginsa. (Caughtoffside)

    Golan Bayern Munich dan kasar Jamus Manuel Neuer, mai shekara 39, yana tunanin tsawaita shekarunsa na murza leda fiye da 2026, inda ake tunanin zai tsawaita zamansa. (Bild)

  5. Tottenham ta doke Leeds ta kawo karshen wasa 23 da ba a doke ta ba agida, Leeds 1-2 Tottenham

    Premierleague

    Asalin hoton, Getty Images

    Tottenham ta je ta ci Leeds United 2-1 a Premier League ranar Asabar a wasan mako na bakwai.

    Tel ne ya fara ci wa Tottenham ƙwallo a minti na 23 da take leda daga baya Leeds ta farke ta hannun Okafor kafin hutu.

    Daga baya Kudus ya kara na biyu da ya bai wa Tottenham maki ukun da take bukata.

    Tottenham ta kawo karshen wasa 23 ba tare da an doke Leeds a gida ba.

    Da wannan sakamakon Tottenham ta koma ta biyun teburi da maki 14 da tazarar maki ɗaya tsakani da Liverpool ta ɗaya.

    Anjima ne Liverpool za ta ziyarci Chelsea a gasar Premier League a Stamford Bridge.

    Leeds tana mataki na 12 da maki takwas a babbar gasar tamaula ta Ingila ta kakar nan.

  6. Ya zama wajibi na kare lafiyar Yamal - Flick

    Yamal

    Asalin hoton, Getty Images

    Kociyan Barcelona, Hansi Flick ya sanar cewar yana da mahimmaci ya kare lafiyar Lamine Yamal, bayan da ya caccaki tawagar Sifaniya kan yadda ba su ɗauki batun lamarin matashin mai shekara 18 kamar yadda ya dace ba.

    Barcelona, wadda za ta je gidan Sevilla ranar Lahadi buga La Liga, ta sanar cewar Yamal zai yi jinyar mako biyu zuwa uku.

    Tawagar Sifaniya ta gayyaci Yalam wasan da za ta buga na neman shiga gasar kofin duniya da za ta yi da Georgia da kuma Bulgaria a makon gobe.

    Sai dai Yamal ba zai samu buga karawar ba, sakamakon raunin da ya ji a Champions League da Paris St Germain ta yi nasara 2-1.

    Matashin ya ji rauni a watan Satumba a lokacin da Sifaniya ta kara da Turkiya da Bulgaria daga nan aka samu rashin jituwa tsakanin Barcelona da Sifaniya, saboda caccakar da Flick ya yi.

    Mako uku da Yamal ya koma taka leda daga jinya ya bayar da gudunmuwar da Barcelona ta doke Real Sociedad da buga karawar da PSG ta yi nasara a gasar zakarun Turai.

    Wasa biyar Yamal ya buga a bana a Barcelona da cin ƙwallo biyu.

  7. Barkanmu da shiga sharhi da bayanan wasanni

    Jama'a barkanmu da shiga shirin sharhi da bayanan wasanni kai tsaye tare da ni Mohammed Abdu Mamman Skipper Tw.

    Za ku iya tafka muhawara a shirin ko bayar da gudunmuwa a BBCHausa Facebook.