Labarin wasanni daga 4 zuwa 10 ga watan Oktoban 2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Asabar 4 zuwa 10 ga watan Oktoban 2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Depay bai je Netherlands ba, saboda an sace masa fasfo a Brazil

    Depay

    Asalin hoton, Getty Images

    Memphis Depay bai samu halartar sansanin Netherlands ba, bayan da ya bayar da rahoton an sace masa fasfo a Brazil, wanda ke taka leda a Corinthians.

    Tun a ranar Lahadi ake sa ran ɗan wasan zai isa kasar, amma bai samu damar yin tafiya ba.

    Tawagar da Roland Koeman ke jan ragama za ta buga wasan neman shiga gasar cin kofin duniya da Malta ranar Alhamis, sannan ta fafata da Finland ranar Lahadi.

    A watan jiya Depay ya zama kan gaba a ciwa kasarsa ƙwallaye da 52 a karawa 104, bayan da ya ci Lithuania biyu.

    Kenan yana gaban Robin van Persie, wanda ke rike da tarihin.

    Netherlands tana jan ragamar teburin rukuni na bakwai da tazarar ƙwallaye tsakani da Poland mai ƙwantan wasa.

  2. Newcastle za ta cika shekara huɗu karkashin masu zuba hannun jari

    Newcastle

    Asalin hoton, Getty Images

    Kyaftin ɗin Newcastle United, Bruno Guimaraes yace suna kan turbar ci gaba a ƙungiyar, wadda ke shirin bikin cika shekara huɗu karkashin masu zuba hannun jari da Saudiyya ke marawa baya.

    Tun bayan da masu zuba hannun jarin suka mallaki Newcastle United ranar 7 ga watan Oktoba, ƙungiyar ta samu shiga Champions League karo biyu har da wanda take buga wa a bana.

    Sannan a kakar da ta wuce ne Newcastle ta lashe Carabao Cup, bayan cin Liverpool, kofin farko da ta ɗauka a shekara 70.

    Sai dai a kakar nan ƙungiyar St James Park ba ta kokari tun bayan da ta sayar da Alexander Isak ga Liverpool.

    Ranar Lahadi Newcastle ta doke Nottingham Forest 2-0 a wasan mako na bakwai a Premier League, kenan tana ta 11 a kan teburin da maki tara.

  3. Rodri ba zai buga wa Sifaniya wasannin neman shiga kofin duniya ba

    Rodri

    Asalin hoton, Getty Images

    Tawagar Sifaniya ta tabbatar cewar Rodri ba zai buga mata wasa biyu ba na neman shiga gasar kofin duniya, bayan da ya ji rauni a karawar da Manchester City ta je ta doke Brentford 1-0 a Premier League ranar Lahadi.

    An sauya Rodri a minti na 22, bayan da tuni City ta ci ƙwallo ta hannun Erling Haaland a filin wasa na Gtech Community.

    Tawagar Sifaniya za ta kece raini da Georgia ranar Asabar, sannan ta fuskanci Bulgaria ranar Talata.

  4. Gossip

    Asalin hoton, Getty Images

    James Ward-Prowse, mai shekara 30, yana shirin barin West Ham na dindindin a lokacin bazara, inda dan wasan tsakiyar na Ingila ya rasa damar taka leda tun da Nuno Espirito Santo ya karbi ragamar kungiyar. (FootballInsider)

    Dan wasan bayan Uruguay Ronald Araujo ya ki amincewa da damar barin Barcelona a bazara, dan wasan mai shekaru 26 ya shaidawa Chelsea, da Liverpool, da Tottenham da Juventus cewa yana son ci gaba da zama a kulob dinsa. (Sports Espanya)

    Amma Barcelona na iya siyar da Araujo a watan Janairu, bayan da ta sanya masa farashin kusan fam miliyan 35 don siyan mai tsaron baya. (Fichajes)

    West Ham na sha'awar daukar dan wasan gaba na Real Madrid, Endrick a matsayin aro, amma za ta fuskanci hamayya daga Valencia da Real Sociedad kan sayen dan wasan na Brazil mai shekara 19 a watan Janairu. (Fichajes)

    Arsenal na fatan za ta amince da sabuwar yarjejeniya da Bukayo Saka, mai shekara 24, a lokacin hutun kasa da kasa domin ci gaba da rike dan wasan na Ingila na dogon lokaci. (TBR Football)

    Liverpool na ci gaba da tattaunawa da Ibrahima Konate, mai shekara 26, domin neman tsawaita kwantiraginsa, yayin da Real Madrid ke zawarcin dan wasan na Faransa. (FootballInsider)

  5. Har yanzu Postecoglou bai ci wasa ba a Nottingham Forest

    Postecoglou

    Asalin hoton, Getty Images

    Har yanzu Ange Postecoglou ya kasa cin wasa a Nottingham Forest tun bayan da ya maye gurbin Nuno Espirito Santo a farko farkon watan Satumba.

    Newcastle United ta doke Forest 2-0 a wasan mako na bakwai a Premier a St James Park ranar Lahadi.

    Kenan a wasa bakwai da Postecoglou ya já ragama ya yi canjaras biyu da rashin nasara biyar aka zura musu kwallo 15 kawo yanzu, suna na 17 a kasan teburi da maki biyar.

    Daya wasan Premier tsakanin Wolverhampton da Brighton tashi suka yi 1-1 kunnen doki a Molineux a ranar ta Lahadi.

    Kenan har yanzu Wolverhampton ba ta ci wasa ba daga karawa bakwai da fara kakar nan a babbar gasar tamaula ta Ingila,

    Ta kuma maimaita irin wanan rashin kwazon da ta yi a kakar da ta wuce a gasar ta Premier League.

    Tun da fari Aston Villa ta yi nasarar cin Burnley 2-1 daga fafatawa biyar da aka yi a Premier a jiya Lahadi.

  6. Everton ta kawo karshen wasa 19 a jere ba a doke Crystal Palace ba

    Grealish

    Asalin hoton, Getty Images

    Everton ta kawo karshen wasa 19 a jere ba a doke Crystal Palace ba.

    Kungiyar da David Moyes ke jan ragama ta yi nasarar cin Palace 2-1 a sabon filinta na Hill Dickinson.

    Kuma golan Everton, Jordan Pickford ya tsare raga karo na 300 a ƙungiyar a ranar

    Kenan shi ne na biyu ɗan kasar Ingila da ya tsare raga a Premier League da yawa, bayan David Seaman na Arsenal da ya yi karawa 325.

    Da wannan sakamakon Everton tana mataki na takwai da maki 11, Palace kuma mai maki 12 tana ta shidan teburin Premier League.

  7. Guardiola ya zama kociya na 16 da ya ci wasa 250 a Premier League

    Pep Guardiola

    Asalin hoton, Getty Images

    Pep Guardiola ya ci wasa na 250 a Premier League, bayan da Manchester City ta je ta ci Brentford 1-0 ranar Lahadi a wasan mako na bakwai.

    Erling Haaland ne ya ci kwallo na tara a Premier League na 18 a Norway da City da fara kakar nan..

    Guardiola ya zama kociya na 16 da ya ci wasa 250 a babbar gasar tamaula ta Ingila a wasa na 349.

    Kenan kungiyar Etihad ta koma ta biyar din teburi da maki 13.

  8. Zazu ya buge Shagon Audun Tunga a damben gargajiya

    Damben gargajiya

    An buga wasannin damben gargajiya da yawa a gidan wasa dake Ado Bayero Square a Kano, Nigeria ranar Lahadi.

    Ga sakamakon wasannin da aka yi canjaras:

    • Bahagon Ramadan da Shagon Auwalu
    • Dan Alin bata isarka da Shagon Bahagon yan Sanda

    Damben da ya yi kisa:

    • Karfe maci karafa ya buge Bahaushe
    • Gaba bakwai baya bakwai ya yi nasara a kan Dogon Bahagon zayyanu
    • Zazu ya barar da Shagon Audun Tunga
  9. Barau FC ta yi rashin nasara a gida a hannun Warri Wolves

    Barau FC

    Asalin hoton, Barau FC

    Barau FC ta yi rashin nasara a filin wasa na Sani Abacha a karon farko a bana, sakamakon da Warri Wolves ta doke ta da cin 1-0 ranar Lahadi.

    Sai dai kungiyar Barau FC mai kwantan wasa ta karasa wasan da yan kwallo 10 a cikin fili.

    Sauran sakamakon wasannin da aka buga:

    • Enyimba 0-0 Rivers United
    • Niger Tornadoes 1-1 Kun Khalifam,
    • Shooting Stars 1-0 Plateau United
    • Kwara United 0-1 Abia Warriors
    • Bayelsa United 1-1 Ikorodu City.

    Sai aka ɗage wasan Enugu Rangers da Katsina United

    Barau FC mai kwantan wasa tana ta 18 a kasan teburi da maki biyar, Kano Pillars mai kwantai biyu ta 19 da Kun Khalifa ta karshe ta 20.

    Nasarawa United ce ta ɗaya a kan teburin Premier ta Najeriya, sai Enyimba ta biyu da kuma Abia Warriors ta uku.

  10. Haaland ya ci ƙwallo 18 kawo yanzu da fara kakar bana

    Haaland

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗan wasan Manchester City, Erling Haaland ya zura ƙwallo 18 a raga a tawagarsa ta Norway da Manchester City a bana.

    City ta je ta ci Brenford 1-0 a wasan mako na bakwai a Premier League, kuma Haaland ne ya ci ƙwallo na tara jimilla a babbar gasar tamaula ta Ingila.

  11. Sevilla ta ragargaji Barcelona a mako na takwas a La Liga

    Barcelona

    Asalin hoton, Getty Images

    Sevilla ta ragargaji Barcelona da cin 4-1 a wasan mako na takwas a gasar La Liga da suka kara ranar Lahadi.

    Da wannan sakamakon Barcelona mai rike da kofin La Liga ta koma ta biyu da tazarar maki biyu tsakani da Real Madrid mai jan ragama.

    Karo na biyu a jere da Barcelona ta yi rashin nasara, bayan da Paris St Germain ta doke ta 2-1 a Champions League.

    Waɗanda suka buga wasan da waɗandfa suka ci ƙwallaye:

    Sevilla: Vlachodimos; Carmona, Azpilicueta, Marcão, Suazo; Agoumé, Mendy ( canji Peque); Alexis ( canji Ejuke), Sow (canji Gudelj ), Vargas (canji Januzaj); Romero (canji Adams )

    Cin ƙwallaye: Alexis (fenariti a minti na 14), Romero (a minti na 37), Carmona (a minti na 90), Adams (a minti na 90+7’)

    Barcelona: Szczesny; Kounde, Araujo (canji Eric), Cubarsí, Martín (canji Balde); De Jong (canji Christensen), Pedri; Rashford, Olmo, Ferran (canji Roony); Lewandowski

    Cin ƙwallo: Rashford (45+7’)

  12. Kewell ya karɓi aikin horar da Hanoi FC

    Tsohon ɗan wasan Liverpool da Leeds United, Harry Kewell ya karɓi aikin kociyan ƙungiyar da ke buga gasar Vietnam, Hanoi FC.

    Ƙungiyar ta sanar da hakan a kafarta ta sada zumunta, cewar ɗan kasar Australia, mai shekara 47, zai maye gurbin ɗan kasar Japan, Makoto Teguramori.

    Aikin karshe da Kewell ya yi shi ne kocin Yokohama F Marinos a babbar gasar tamaula ta Japan da kai ƙungiyar wasan karshe a gasar zakarun Asia a 2024.

    Marinos ta yi rashin nasara a bugun fenariti a hannun Al Ain daga Haɗadɗiyar Daulal Larabawa, sai kuma aka kori Kewell bayan fara kakar tamaula da kafar hagu wata biyu tsakani.

  13. Za a kammala ginin da zai maye filin San Siro kan 2030/31

    San Siro

    Asalin hoton, Getty Images

    Za a kammala gina sabon katafaren filin wasan Milan da za a fara amfani da shi a gasar Serie A 2030/31, domin maye San Siro, in ji shugaban AC Milan, Paolo Scaroni.

    AC Milan ce ke jan ragamar aikin tare da Inter Mikan, bayan da mahukunta suka amince da bukatar ƙungiyoyin biyu na gina sabon filin da zai yi daidai da zamani.

    Ana sa ran fara aiki a farkon kakar 2027, sannan a kammala komai da fara taka leda a filin a kakar Serie A ta 2030/31.

    An dade ana caccakar Italiya kan tsoffin filayen tamaula da take da su, inda masu zuba jari ke fatan a gina sabbi ko yin kwaskwarima domin karɓar bakuncin gasar cin kofin nahiyar Turai a 2032 da za ta yi haɗaka da Turkiya.

    Haka kuma sabon filin da za a gina a Milan zai taimakawa ƙungiyoyin biyu, wajen samun karin kuɗin shiga da zarar an faɗaɗa ginin.

    To sai dai ƴan siyasa da masu ruwa da tsaki da masu bibiyar tamaula, sun bukaci a bar San Siro, domin ƴan baya su riski tarihi a fannin ƙwallon kafar Italiya.

  14. Henry ya aike min da sakon ƙwarin gwiwa kafin wasan West Ham - Saka

    Saka

    Asalin hoton, Getty Images

    Bukayo Saka ya ce ya samu sako daga Thierry Henry, wanda ya kara masa kwarin gwiwa da cewar kada su bari tarihi ya maimata kansa a Emirates a wasan Premier League da West Ham.

    Gunners ta doke West Ham 2-0 a wasan mako na bakwai ranar Asabar karo na 300 da Mikel Arteta ya ja ragamar Arsenal.

    Saka ne ya ci ƙwallo na biyu a zagaye na biyu, hakan ya sa Gunners ta haɗa maki ukun da take bukata da ta kai ta koma ta ɗaya a kan teburin Premier League.

    A ranar Saka ya buga wasa na 200 a Arsenal da cin ƙwallo na 55, ya kuma bayar da 45 aka zura a raga.

    Arsenal tana matakin farko a kan teburin Premier League da maki 16 da tazarar ɗaya tsakani da Liverpool, wadda ta koma ta biyu, sakamakon da Chelsea ta doke ta ranar Asabar a Stamford Bridge.

  15. Everton ta taka wa Palace burki, bayan wasa 19 a jere ba tare da an doke ta ba, Everton 2-1 Crystal Palace

    Premier

    Asalin hoton, Getty Images

    Everton ta doke Crystal Palace 2-1 a wasan mako na bakwai a Premier League ranar Lahadi.

    Hakan ya kawo karshen wasa 19 da Palace ta buga a jere ba tare da rashin nasara ba a dukkan fafatawa.

    Mai tsaron ragar Everton, Jordan Pickford ya tsare raga karo na 300 ranar Lahadi a ƙungiyar, kuma shi ne gola ɗan kasar Ingila na biyu da ya buga Premier League da yawa, bayan David Seaman na Arsenal da ya yi karawa 325.

    Da wannan sakamakon Everton tana mataki na bakwai da maki 11, Palace kuma mai maki 12 tana ta biyar ɗin teburin Premier League.

  16. Gasar Premier ta Najeriya ranar Lahadi mako na takwas, Nigerian Premier League

    Barau FC

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasannin mako na takwas:

    • Barau da Warri Wolves
    • Bayelsa United da Ikorodu City
    • Enugu Rangers da Katsina United
    • Enyimba da Rivers United
    • Kwara United da Abia Warriors
    • Niger Tornadoes da Kun Khalifat
    • Shooting Stars da Plateau United
  17. An kara yawan tawaga a Wafcon daga 12 zuwa 16 a 2026

    Wafcon

    Asalin hoton, Getty Images

    An kara yawan tawagar mata da za ta buga gasar cin kofin nahiyar Afirka daga 12 za su koma 16 daga wasannin da Morocco za ta karɓi bakunci a 2026, kamar yadda hukumar ƙwallon kafar Afirka ta sanar.

    Hakan ya biyo bayan taron da hukumar ƙwallon kafar Afirka, Caf ta gudanar a birnin Kinshasa.

    Caf za ta yi karin bayani nan gaba kan yadda za a buga wasannin cike gurbin shiga gasar da za a yi a baɗi.

    An fara da tawaga takwas a gasar cin kofin Afirka ta mata a 1998 har zuwa wanda Ghana ta gudanar a 2018.

    Ba a buga wasannin ba a 2020, saboda ɓullar cutar Corona, amma an ci gaba da gasar a 2022 da tawaga 12.

    Najeriya ce ta lashe kofin bana, an kuma bata ladan dalar Amurka 750,000, kuma na 10 da take da shi jimilla.

  18. Rodri na bukatar lokaci kafin ya koma kan ganiya - Guardiola

    Premier League

    Asalin hoton, Getty Images

    Kociyan Manchester City, Pep Guardiola ya ce Rodri na bukatar lokaci kafin ya koma kan ganiya, bayan da yake fatan Nico Gonzalez zai kara sa ƙwazo, wanda ke buga gurbin Rodri.

    Rodri ya buga wasan da City ta tashi 2-2 da Monaco a Champions League, yayin da Guardiola ya ajiye shi a wasanni biyu baya domin kada ya fama raunin.

    Guardiol ya ce Rodri mai shekara 29 zai bisu wasan da City za ta buga da Brentford ranar Lahadi a Premier League, amma dai yana taka tsantsan wajen saurin saka shi a wasa.

  19. Estevao ya zama matashin Brazil na biyu da ya ci ƙwallo a Premier

    Ɗan wasan Chelsea, Esteva, wanda ya ci Liverpool ƙwallo na biyu ya zama matashi daga Brazil da ya zura ƙwallo a raga a Premier League a tarihi, mai shekara 18 da kwana 163.

    Mai rike da tarihin shi ne Rafael na Manchester United mai shekara 18 da kwana 122 a Nuwambar 2008.

  20. Moyes ya ce yana sa ran kammala kakar nan cikin ƴan 10 farko

    Moyes

    Asalin hoton, Getty Images

    Mai horar da Everton, David Moyes ya ce yana sa ran zai kammala kakar bana ta Premier League cikin ƴan 10 farko.

    Everton tana da maki takwas daga wasa shida da fara kakar bana.

    A irin wannan lokacin karkashin Sean Dyche a bara, Everton tana mataki na 16 a kasan teburi.

    Daga baya aka bai wa Moyes aikin, wanda ya kare a mataki na 13 teburi da ya sa ƙungiyar ta ci gaba da zama a Premier League.