Labarin wasanni daga 4 zuwa 10 ga watan Oktoban 2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Asabar 4 zuwa 10 ga watan Oktoban 2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Ansu Fati ya kafa tarihi a gasar Ligue 1 ta Faransa

    Ansu Fati

    Asalin hoton, Reuters

    Ɗanwasan Barcelona Ansu Fati ya dawo kan ganiya tare da kafa tarihin ɗanwasa mafi saurin cin ƙwallo biyar a gasar Ligue 1 ta Faransa.

    Ɗanƙwallon mai shekara 22 na buga wa AS Monaco wasan aro a kakar wasa ta bana, kuma ya ci ƙwallo biyar cikin mintuna 126 kacal da ya buga wa ƙungiyar zuwa yanzu.

    Hakan ya sa ya karya tarihin da Johan Audel’ ya kafa na cin ƙwallo biyar cikin mintuna 137 a ƙungiyar Valenciennes shekara 77 da suka wuce.

    Baya ga ƙwallo biyar da ya ci a Ligue 1, ya ci ɗaya a gasar zakarun Turai ta Champions League.

    Shi da Joaquín Panichelli ne kan gaba a matsayin waɗanda suka ci ƙwallaye mafiya yawa a babbar gasar ta Faransa.

  2. Ɗanwasan Togo Asamoah ya karya wuya a China

    Samuel Asamoah

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗanwasan tsakliya na ƙasar Togo Samuel Asamoah ya karya wuya sakamakon karo da ya yi da wani allon talla a China.

    Ƙungiyarsa ta Guangxi Pingguo mai buga gasar China mai daraja ta biyu ta ce lamarin zai iya jawo masa shanyewar ɓarin jiki.

    Asamoah mai shekara 31 ya yi karo da allon talla na gefen fili bayan wani ɗanwasan abokan karawarsu ya ture shi yayin wasansu a ranar Lahadi.

    A ranar Litinin ƙungiyar ta sanar cewa Asamoah na cikin háɗarin kamuwa da larurar paraplegia saboda karairaya da ya samu a wuyansa da kuma rauni a lakarsa.

    Kulob ɗin ya ce tuni aka yi masa tiyata, kuma za a sanar da jinyar da za iyi nan gaba.

  3. Saura ƙiris Ghana ta samu gurbi a gasar Kofin Duniya

    'Yanwasan Ghana

    Asalin hoton, Black Stars

    Tawagar ƙwallon ƙafa ta Ghna Black Stars na gab da samun gurbi a gasar Kofin Duniya ta 2026 bayan nasarar casa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya 5-0 ranar Laraba.

    Mohammed Salisu, da Thomas Partey, da Alexander Djiku, da Jordan Ayew, da Kamaldeen Suleimana ne suka ci wa Ghana ƙwallayen a wasansu na Rukunin I.

    Sakamakon ya sa Ghana ta haɗa maki 22 cikin wasa tara, kuma da zarar ta tashi wasan ƙarshe da Comoros ba tare da an doke ta ba za ta samu gurbin shiga gasar da ƙasashen Amurka da Mexico da Canada za su shirya.

    Madagascar ce ta biyu a teburin da maki 19, sai Mali ta uku mai maki 15.

  4. Fernandes ba shi da sha'awar komawa Saudiyya

    Bruno Fernandes

    Asalin hoton, Reuters

    Ɗanwasan tsakiyar Manchester United Bruno Fernandes ba shi da sha'awar komawa taka leda a Saudiyya a ƙarshen kakar wasa ta bana, kamar yadda BBC Sport ta fahimta.

    Ɗanwasan na Portugal ya ƙi amincewa da tayi masu gwaɓi daga Al-Hilal da Al-Ittihad a bazarar da ta gabata domin raba shi da filin wasa na Old Trafford.

    Majiyoyi na kusa da ɗanƙwallon sun yi watsi da raɗe-raɗi na baya-bayan nan da ke cewa ya shirya tsaf domin barin Manchester United bayan gasar Kofin Duniya a shekara mai zuwa.

    An faɗa wa BBC cewa ba haka abin yake ba, kuma Fernandes, wanda kwantaraginsa zai kai har 2027, ya fi son ci gaba da taka leda a nahiyar Turai.

    Mai horarawa Ruben Amorim na amfani da Fernandes mai shekara 31 a matakin baya-baya na tsakiyar fili a wannan kakar, yana mai cewa zai fi taimakawa a nan - kodayake wasu na cewa hakan zai raba shi da saurin cin ƙwalllon da ya saba yi.

  5. Ya kamata Rabiot ya martaba ƙungiyar da yake buga wa tamaula

    Rabiot

    Asalin hoton, Getty Images

    Babbab jami'in Serie A, Luigi de Siervo ya ce ya kamata Adrien Rabiot ya martaba ƙungiyarsa, bayan da ɗan ƙwallo ya caccaki AC Milan kan shirin da take na buga wasa a wajen kasar.

    A cikin watan Fabrairu AC Milan za ta buga gasar Serie A da za ta kara da Como a birnin Perth a Australia.

    Haka kuma a La Liga za a kece raini tsakanin Barcelona da Villareal a birnin Miamin Amurka a cikin Disamba.

    Ɗan wasan tawagar Faransa ya faɗa a wata hira da aka yi da shi cewar tsarin bai kamata ba, kuma wauta ne.

  6. Watakila Kane ba zai buga wa Ingila wasan sada zumunta da Wales ba

    Kane

    Asalin hoton, Getty Images

    Watakila ƙyaftin, Harry Kane ba zai buga wa Ingila wasan sada zumunta ba da Wales ranar Alhamis, bayan da bai yi atisaye ba ranar Laraba.

    Mai taka leda a Bayern Munich ya motsa jiki a gefen fili tare da Jarell Quansah.

    Kane na taka rawar gani a bana, wanda ya ci ƙwallo 11 da fara kakar nan da bayar da uku aka zura a raga a Bayern Munich a dukkan fafatawa.

    Shi ne kan gaba a yawan ci wa Ingila kwallaye a tarihi mai 74 a wasa 109.

    Ingila za ta je ta kara da Latvia ranar 14 ga watan Oktoba, kuma da zarar ta yi nasara a karawar, ta samu tikitin kai wa gasar kofin duniya kai tsaye da za a yi a Amurka da Canada da kuma Mexico a 2026.

  7. Al-Ahly ta naɗa Jess Thorup sabon kociyanta

    Ƙungiyar Al-Ahly ta dauki sabon koci ɗan kasar Denmark, Jess Thorup kan yarjejeniyar kaka biyu da rabi, kamar yadda ta sanar ranar Laraba, bayan da ta sallami ɗan kasar Sifaniya, Jose Riveiro.

    Thorup, mai shekara 55, ya koma ƙungiyar Masar, bayan barin FC Augsburg mai buga Bundesliga a cikin watan Mayu.

    Ya horar da FC Copenhagen da Genk da Gent da matasan Denmark ƴan kasa da shekara 21.

    Al-Ahly ta ce Thorup zai je Cairo ranar Alhamis tare da waɗanda za su taimaka masa mutum biyu da mai kula da mota jiki da masanin tsefe wasa da mai horar da masu tsare raga.

    Ana sa ran zai fara aiki daga ranar Juma'a.

    Al-Ahly ta fara kokari karkashin kociyan rikon ƙwarya, Emad Al Nahhas, inda ƙungiyar take da maki 18 iri daya da wadda ke jan ragama Zamalek da El-Masry da kwantan wasa.

  8. Tarkowski ya tsawaita ƙwantiragi da Everton

    Tarkowski

    Asalin hoton, Getty Images

    Mai tsaron bayan Everton, James Tarkowski ya tsawaita yarjejeniyar ci gaba da taka leda a ƙungiyar zuwa karshen kakar 2028.

    Mai shekara 32, ya koma ƙungiyar daga Burnley a 2022, ya kuma buga mata wasa 128 kawo yanzu.

    Tarkowski, ya buga wa tawagar Ingila wasa biyu, an kuma naɗa shi mataimakin ƙyaftin ɗin Everton a 2023.

    Tarkowski ya yi wa Everton wasa bakwai da fara Premier League ta bana karkashin David Moyes da ƙungiyar take mataki na takwas.

  9. Watford ta kori Pezzolano ta sake ɗaukar Gracia

    Watford

    Asalin hoton, Getty Images

    Watford ta kori kociyanta, Paulo Pezzolano bayan jan ragama wasa 10 a gasar Championship, ta sake ɗaukar Javi Gracia.

    Pezzolano, mai shekara 42, ya karɓi aikin a cikin watan Mayu, bayan da ta sallami Tom Cleverly na 12 da ta kora tun bayan da Gracia ya ajiye aikin a 2019.

    Watford ta sayo ƴan wasa 13 kan fara kakar nan domin ta taka rawar gani, bayan da ta kare a mataki na 14 a bara.

    Ta fara kakar bana da rashin kokari daga baya abubuwa suka inganta, ta samu maki bakwai daga karawa uku baya har da cin Oxford 2-1 ranar Asabar - hakan ya sa ta koma ta 11 teburi.

    Pezzolano shi ne kociyan da bai daɗe ba kan aikin, bayan Rob Edwards da ya yi wasa 11 a 2022 - yanzu yana horar da Middlesbrough wadda take ta biyu a kan teburin Championship..

  10. Gossip

    Asalin hoton, Getty Images

    Leeds za ta nemi sayen ɗan wasan gefe a watan Janairu bayan da ta fuskanci cikas a yunkurunta na ɗaukar ɗa wasan Fulham da Wales Harry Wilson, mai shekara 28, a bazarar da ta gabata. (Sky Sports)

    Tsohon ɗan wasan Leeds Raphinha yana cikin ƴan wasan da Manchester United ke sha'awa bayan da ya taka rawar gani a Barcelona amma farashin ɗan wasan na Brazil, mai shekara 28, zai iya kai wa fam miliyan 120. (Fichajes)

    Tsohon kocin Everton Sean Dyche ba ya sha'awar zama kocin Rangers bayan da ƙungiyar ta raba gari da Russell Martin. (Sky Sports)

  11. An bai wa Amorim shekara uku ya mayar da Man United kan ganiya

    Amorim

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗaya daga cikin mafiya yawan hannun jari a Manchester United, Sir Jim Ratcliffe ya bai koci, Ruben Amorim shekara uku ya mayar da ƙungiyar kan ganiya.

    Ɗan kasar Portugal, wanda zai cika shekara ɗaya da karɓar aikin horar da United, ya yi wasa 50 da cin 19 da canjaras 12 aka doke shi 12 tun bayan da ya karbi aikin cikin Nuwambar 2024.

    Tun da ya fara jan ragamar ƙungiyar Old Traffor, Amorim bai taɓa cin wasa biyu ba a jere a Premier League, wanda ya kare a mataki na 15 a kasan teburi a bara - rashin ƙwazo mafi muni tun bayan 1974.

    Ko a bana abubuwa ba su sauya ba, domin tuni aka yi waje da United a Carabao Cup a hannun wata karamar ƙungiya mai buga League Two, Grimsby.

    Kawo yanzu bayan da aka buga wasa bakwai da fara babbar gasar tamaula ta Ingila, United mai maki 10 tana ta 10 teburi.

  12. Man United

    Asalin hoton, Reuters

    Ɗan wasan gaban Manchester United Joshua Zirkzee, mai shekara 24, na ganin ficewa daga ƙungiyar a watan Janairu yana da matuƙar muhimmanci idan har zai samu damar shiga tawagar ƴan wasan ƙasar Netherlands a gasar cin kofin duniya da za a yi a bazara mai zuwa. (Mail Plus)

    Kocin Chelsea Enzo Maresca ba zai dawo da ɗan wasan baya na Faransa Axel Disasi, mai shekara 27, cikin ƴan wasansa ba, duk da matsalar raunin da masu tsaron bayan ƙungiyar ke fuskanta. (Sun)

    West Ham na sha'awar ɗaukar Joshua Zirkzee daga Manchester United, inda sabon kocinta Nuno Espirito Santo ke neman karfafa yanjwasansa na gaba. (Football Insider)

    Ɗan wasan tsakiya na Ingila Kobbie Mainoo, mai shekara 20, shi ma yana neman barin Old Trafford a watan Janairu bayan rahotanni sun bayyana cewa Napoli na Zawarcinsa. (Mirror)

    Shi kuwa Harry Maguire, mai shekara 32, yana son ci gaba da zama a Manchester United amma dole ne a rage masa albashi domin tsawaita zamansa a ƙungiyar zuwa bayan ƙarshen kakar wasa ta bana. (Talksport)

  13. Ronaldo ya zama biloniya na farko tsakanin ƴan ƙwallon kafa

    Ronaldo

    Asalin hoton, ge

    Cristiano Ronaldo ya zama biloniya na farko tsakanin ƴan wasan ƙwallon kafa a duniya in ji Bloomberg.

    Bloomberg mai sharhi da ƙididdiga tarin dukiya tsakanin attajiran duniya, ta fayyace tarin ƙuɗin da mai shekara 40 ɗan ƙwallon tawagar Portugal mai taka leda a Al-Nassr ta Saudiya keda shi.

    Ta ce yana da dalar Amurka biliyan ɗaya da miliyan 400 daga ƙuɗin da yake samu na albashi da ladan wasa da tallace-tallace da zuba hannun jari.

    Ya samu albashin sama da dalar Amurka miliyan 550 tsakanin 2002 zuwa 2023 da ƙwantiragin da yake da Nike ta dalar Amurka miliya 18.

    Lokacin da Ronaldo ya koma Al-Nassr ta Saudiyya a 2022, ya zama wanda ke kan gaba da ake biya albashi mafi tsoka a tarihi da ake biya fam miliyan 177 duk shekara.

    Ƙwantiraginsa zai kare a karshen Yunin 2025, amma ya tsawaitata zuwa kaka biyu kan dalar Amurka miliyan 400.

  14. Kane ya zaɓi ci gaba da wasa a Bundesliga maimakon ya koma Premier

    Kane

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗan wasan tawagar Ingila, Harry Kane ya ce a shirye yake ya tsawaita yarjejeniyarsa a Bayern Munich ta wuce 2027, ya kuma ce batun ya sake komawa buga Premier League ya dusashe.

    Kane sai kafa tarihi yake tun bayan da ya koma Bayern daga Tottenham a 2023, ya ci ƙwallo 103 a wasa 106 a dukkan fafatawa da lashe Bundesliga da German Super Cup.

    A watan jiya sabon kociyan Tottenham, Thomas Frank ya ce wasu magoya bayan ƙungiyar na fatan Kane zai koma musu buga Premier League, wanda ya ci ƙwallo 213 da tazarar 47 tsakaninsa da Alan Shearer, wanda ke kan gaba a yawan cin ƙwallaye a tarihi a babbar gasar tamaula ta Ingila.

    Ƙyaftin Kane yana cikin tawagar Ingila da za ta yi wasan sada zumunta da Wales ranar Alhamis a Wembley daga nan ta je ta fafata da Latvia a wasan neman shiga gasar kofin duniya ranar 14 ga watan Oktoba.

  15. Emery

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayern Munich na zawarcin dan wasan bayan Crystal Palace Marc Guehi mai shekara 25, wanda kwantiraginsa zai kare a karshen kakar wasa ta bana. (Sky Gemany)

    Crystal Palace na shirin bai wa Adam Wharton sabon kwantiragi don kokarin hana shi komawa Liverpool, ko Chelsea da Manchester City, da dukkansu ke neman dan wasan tsakiyar na Ingila mai shekara 21. (Mail)

    Napoli tana kan gaba cikin masu son daukar dan wasan tsakiya na Manchester United da Ingila Kobbie Mainoo, mai shekara 20, a matsayin aro a watan Janairu bayan da ta ci gaba da tuntubar kungiyar ta Premier tun lokacin bazara. (Sky Switzerland)

    Eintracht Frankfurt na zawarcin dan wasan Newcastle da Denmark William Osula, mai shekara 22, a matsayin aro a watan Janairu.(Mail)

    Nottingham Forest ta jima tana sha'awar mai horar da Fulham Marco Silva idan ta kori Ange Postecoglou, duk da cewa ba za ta iya tunkarar kocin dan Portugal kafin karshen kakar wasa ta bana ba. (Mail)

  16. Stone ya kusan yin ritaya a bara, saboda fama da jinya

    Stone

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗan wasan tawagar Ingila da Manchester City, John Stone ya ce ya kusan yanke shawarar yin ritaya, sababoda rauni da ya hana shi sakat a bara.

    Wasa 11 Stone ya buga a Premier League a kakar da ta wuce, bayan jinya, daga baya ya hakura da wasannin tun cikin Fabrairu.

    Mai shekara 31 ya wakilci Ingila a manyan gasa biyar, amma rabon da ya buga wa tawagar tamaula tun Oktoban 2024, Thomas Tuchel ya karbi aikin horarwa a watan Janairu.

    Stone yana cikin ƴan wasan Ingila da za su buga wasan sada zumunta da Wales ranar Alhamis a Wembley daga nan ta kara da Latvia ranar 10 ga watan Oktoba.

    Da zarar Ingila ta yi nasara a gidan Latvia ta samu tikitin shiga gasar kofin duniya kenan da za a yi a Amurka da Canada da Mexico a baɗi.

  17. Tawagar Faransa ta gayyaci Mateta saboda ƙyawawan halinsa da cin ƙwallaye

    Mateta

    Asalin hoton, Getty Images

    Tawagar Faransa ta gayyaci ɗan wasan Crystal Palace, Jean-Philippe Mateta, saboda ƙyawawan halinsa da cin ƙwallaye, amma sai ya nuna kansa in ji koci, Didier Deschamps.

    Mateta ya ci ƙwallo 17 a dukkan karawa a bara da Palace da lashe FA Cup, babban kofi da ta ɗauka a shekara 164 a tarihi.

    Ya buga wa tawagar Faransa ta matasa tamaula da wasannin Olympic a bara da kasar ta lashe azurfa.

    Faransa za ta kara da Azerbaijan da kuma Iceland a wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya a cikin watan nan.

    Faransa, wadda ke jan ragamar rukuni na huɗu za ta karɓi bakuncin Azerbaijan a the Parc des Princes ranar 10 ga watan Oktoba daga nan ta fafata da Iceland kwana uku tsakani.

  18. Gossip

    Asalin hoton, Getty Images

    Manchester United ta yi imanin cewa dan wasan baya Lisandro Martinez, mai shekara 27, zai iya dawowa daga raunin da ya ji kafin karshen shekara. Dan kasar Argentinan dai bai buga wa kungiyar wasa ba cikin watanni takwas. (Sun)

    Barcelona za ta iya zawarcin dan wasan gaban Borussia Dortmund da Jamus Karim Adeyemi, mai shekara 23, wanda kwantiraginsa a Bundesliga zai kare a shekara ta 2027. (Sky Switzerland)

    Manchester City ba ta da niyyar siyar da dan wasan tsakiyar Spain Rodri, mai shekara 2`9, ga Real Madrid kan kowane farashi. (Teamtalk)

    Manchester United na ganin kocin Aston Villa Unai Emery a matsayin wanda zai maye gurbin Ruben Amorim idan har ta sallami kocin dan kasar Portugal. (Fichajes)

    Da wuya Real Madrid za ta sanya hannu kan daukar dan wasan tsakiyar Turkiyya Arda Guler, mai shekara 20, a watan Janairu, duk da sha'awar da Arsenal da Newcastle ke nunawa kansa. (Football Insider)

    Barcelona da Juventus na da kwakkwaran shiri na sayen dan wasan tsakiya na Manchester City dan kasar Portugal Bernardo Silva, mai shekara 31, yayin da kungiyoyin Saudi Arabiya, Al-Ahli, da Al-Qadsiah da Al-Nassr ke shirya zuba makudan kudade kan dan wasan da kwantiraginsa zai kare a shekarar 2026. (Caught Offside)

  19. Arsenal ta saka wa Raya da ƙunshin kwantiragi

    Raya

    Asalin hoton, Getty Images

    Arsenal ta tsawaita yarjejeniyar Raya zuwa karshen kakar 2028, tuni kuma Gunners ta kara masa albashi kan wanda ya karɓa a baya tun bayan da ta mallake shi a 2024.

    Raya na karɓar fam 100,000 a duk mako a Emirates, amma yanzu ya samu kari bayan cimma ƙwantiragi.

    Yarjejeniyarsa za ta kare a karshen 2028, amma wata majiya na cewa za a iya kara masa kaka ɗaya idan ya ci gaba da sa ƙwazo.

    Tun bayan da ya koma Arsenal daga Brentford, wanda ya fara daga wasannin aro a 2023, daga lokacin ya nuna ƙwarewarsa a Gunners.

    Ya lashe takalmin zinare a matakin wanda ya kama wasa da yawa ba tare da ƙwallo ya shiga raga ba a 2023/24, ya kuma kari yin wannan bajintar a bara tare da golan Nottingham Forest, Mats Sels.

  20. Gossip

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon dan wasan baya na Tottenham da Manchester United Sergio Reguilon yana tattaunawa kan komawarsa Inter Miami don hadewa da Lionel Messi a gasar (MLS) bayan kwantiraginsa da Spurs ya kare a bazara. (Mail)

    Chelsea ba za ta yi yunkurin dauko dan wasan bayan Crystal Palace Marc Guehi, mai shekara 25 ba, duk da cewa dan wasan na Ingila zai bar kungiyar a kyauta a bazara mai zuwa. (Express)

    Chelsea dai tana sha'awar sayen dan wasan gaban Bournemouth Antoine Semenyo kuma tana son biyan kusan fam miliyan 78 kan dan wasan Ghana mai shekaru 25. (Fichajes)

    Juventus ta ki amincewa da tayin kusan fam miliyan 58 daga Chelsea kan dan wasan gaban Turkiyya Kenan Yildiz mai shekaru 20. (TuttoJuve)

    Har ila yau Arsenal ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen zawarcin Yildiz inda ta aika da wakilai domin kallonsa a wasan da Juventus ta buga da AC Milan a gasar Seria A ranar Lahadi. (Tuttosport)