Afcon 2025: Mali 0-1 Senegal, Kamaru 0-2 Moroko

Wannan shafi ne da ya kawo muku bayani kai-tsaye kan wasan Mali da Senegal da kuma Kamaru da Moroko a zagayen kwata-fainal na gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2025 a Moroko.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Mohammed Abdu, Isiyaku Muhammad da Ahmad Bawage

Barka da zuwa!

Barka da kasancewa tare da BBC inda za mu kawo muku bayanai kai-tsaye kan karon-battan ranar farko na matakin kwata-fainal a gasar cin kofin nahiyar Afirka da ke gudana a Moroko.

Da farko za a yi karawa mai zafi ta hamayya tsakanin Mali da Senegal.

Senegal na cikin ƙasashe biyar da tun farko aka yi hasashen cewa za su iya lashe kofin, haka nan ma ita ma Mali ba kanwar lasa ba ce.

Sai kuma wasan Kamaru da Moroko mai masaukin baƙi.

Wannan ne wasan da ake ganin zai fi zafi a zagayen kwata-fainal saboda irin ƙwararrun ƴan wasa da ƙasashen biyu ke da su.

Da fatan za ku kasance tare da mu!