Ƴan wasa sun shiga filin wasa
Ƴan wasa daga duka tawagogin sun shiga flin wasa. Ana rera taƙen ƙasa kafin fara gwabzawa.
Wannan shafi ne da ya kawo muku bayani kai-tsaye kan wasan Mali da Senegal da kuma Kamaru da Moroko a zagayen kwata-fainal na gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2025 a Moroko.
Haruna Kakangi, Mohammed Abdu, Isiyaku Muhammad da Ahmad Bawage
Ƴan wasa daga duka tawagogin sun shiga flin wasa. Ana rera taƙen ƙasa kafin fara gwabzawa.
Tawagar Kamaru: Devis Epassy - Che Malone, Samuel Kotto, Nouhou Tolo, Danny Namaso, Carlos Baleba, Arthur Avom, Junior Tchamadeu, Bryan Mbeumo, Christian Kofane, Mahamadou Nagida.
Tawagar Moroko: Bounou - Hakimi, Aguerd, Masina, Mazraoui, El Khannouss, El Aynaoui, Saibari, Díaz, El Kaabi, Ezzalzouli.
Moroko wadda ke karɓar bakuncin gasar za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta kai zagayen daf da karshe - har ma da lashe gasar.
Tana buga wasa ne a gida gaban dubban magoya bayanta - hakan zai iya ƙarfafa mata gwiwa.
Sai dai za mu gani ko Kamaru za ta iya taka mata burki a burinta na son lashe gasar ta Cin Kofin Afirka.
Jim kaɗan za mu kawo muku bayanai kan karon-batta tsakanin Kamaru da Moroko mai masaukin baki.
Senegal ta samu damar kai wasan daf da karshe na wasan Cin Kofin Afirka, bayan doke Mali da 1-0.
Kwallon da Iliman Ndiaye ya zura a minti 27 ne ya bai wa Lions na Teranga nasara.
Ita ce ƙasa ta farko da ta kai wannan mataki.
Senegal ta samu dama mai kyau na ƙara kwallo ta hannun Sadio Mane, sai dai mai tsaron ragar Mali ya tare kwallon da hana ta shiga raga.
An yi ƙarin mintoci bakwai kafin tashi daga wannan wasa.
Wankin hula na son kai Mali dare.
Senegal na ci gaba da riƙe kwallo tana sarrafa ta yanda take so.
Hakan yana tunzura ƴan Mali saboda ƙasa samun kwallon.
Lokaci na ƙure wa Mali a fafutukar da take yi na farke kwallon da Senegal ta jefa mata.
Minti takwas da ƴan ƙari ya rage alkalin wasa ya busa tashi.
Idan aka tashi kunnen doki za a tafi ƙarin lokaci, idan babu ƙungiyar ta yi nasara sai a raba ƙarfi a bugun fenariti.
Duka tawagogin biyu sun yi sauyin ƴan wasa:
Mali: Amadou Haidara ya fita - Nene Dorgeles ya shiga.
Senegal: Habi Diarra da Pape Gueye sun fita - Pathé Ciss da Lamine Camara sun shiga filin wasa.
Mali na ci gaba da ƙoƙarin ganin ta farke kwallo, amma Senegal ta ƙasa ba ta wannan dama.

Asalin hoton, Getty Images
An koma zagaye na biyu na wasan Senegal da Mali.
Duk tawagar da ta samu nasara za ta wuce zuwa wasan daf da karshe.
Shin Mali za ta iya yin bajinta na farke kwallo ganin cewa tana buga wasan ne da ƴan kwallo goma kaɗai bayan ƙorar Bissouma?
Ko kuma Senegal ce za ta zama ta farko da za ta kai zagayen daf da karshe?
An tafi hutun rabin lokaci Senegal na gaban Mali da ci 1-0.
Senegal ce ta fi taka rawar gani inda ta riƙe kwallo kusan kashi 60.5 yayin da Mali kuma ke da kashi 39.5.
Magoya bayan Senegal sun yi ta sowa da murna da kuma rera waƙoƙi lokacin da alkalin wasa ya busa tafiya hutun rabin lokaci.
An bai wa ɗan wasan Mali Yves Bissouma jan kati bayan keta mai muni da ya yi wa Idrissa Gana Gueye.
Ɗan wasan Senegal Pape Gueye ya kai wani kwallo mai ƙarfi zuwa gidan Mali, sai dai kwallon ta yi saman raga sannan ta fita waje.
Iliman Ndiaye ya zura wa Senegal kwallonta na farko a wasan da suke fafatawa da Mali.
Senegal ta fara wasan da zafi-zafi inda take kai hare-hare ragar Mali.
Ƴan wasan na Senegal suna bai buga kwallo daga gefe zuwa gefe a tsakaninsu.
Mali na cikin matsi a halin yanzu, suna wahala kafin samun damar taɓa kwallo.
Senegal da Mali sun fara ɓarje gumi a wasan zagayen kwata-fainal na Gasar Cin Kofin Afirka.
Wannan na ɗaya daga cikin wasannin da zai ja ƴan kallo, a cewar masu sharhi kan kwallon kafa.

Asalin hoton, Getty Images
Tawagar Mali ta haɗa da: Diarra - H. Traoré, Camara, Diaby, Gassama - Haidara, Bissouma, Coulibaly, Dieng, Sangaré – Sinayoko.
Tawagar Senegal: Édouard Mendy - Diatta, Koulibaly, Niakhaté, El Hadji Malick Diouf, Diarra, Idrissa Gueye, Pape Gueye, Iliman Ndiaye, Diallo, Mané.

Magoya baya sun hallara, inda suke sanye da kayan launukan ƙasashensu.

Asalin hoton, Getty Images
Za a buga wasan ne a wani filin wasa da ke birnin Tangier a ƙasar ta Moroko.