Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye - Juma'a, 06-12-2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammed da Ahmad Bawage

  1. Ƴan tawaye sun ce sun karɓe iko da babban birni na biyu a Syria

    Syria

    Asalin hoton, AFP

    Mayaƙan ƴan tawaye a Syria sun ce sun karɓe iko da babban birni na biyu, bayan da sojojin ƙasar suka janye daga Hama bayan an gwabza ƙazamin faɗa.

    Wannan dai shi ne karon farko da ƴan tawaye suka karɓe iko da birnin Hama tun bayan ɓarkewar yaƙin basasa a Syria kusan shekara goma sha huɗu da suka gabata - kuma wannan wani babban koma baya ne ga shugaba Bashar al-Assad.

    Ƴan tawayen sun ƙwace birnin Aleppo a makon da ya gabata, kuma sun ce a shirye suke su ƙara nausawa kudu zuwa Homs wanda shi ne babban birni na gaba.

  2. An harbe magoyin bayan Arsenal yayin murnar cin Man Utd

    Uganda

    Asalin hoton, Farish Magembe

    Bayanan hoto, Ana kula da Lawrence Mugejera a asibiti bayan harbinsa da aka yi

    Ana zargin cewa wani jami'in tsaro ya harbe wani magoyin bayan Arsenal a Uganda, lokacin da yake murnar nasarar da ƙungiyarsa ta samu kan Manchester United a gasar Firimiyar Ingila ranar Laraba.

    An kuma jikkata wani yayin da jami'in tsaron ya buɗe wuta kan dandazon muagoya bayan Arsenal da ke murna a wani wajen cin abinci a garin Lukaya, mai nisan kilomita 100 da Kampala babban birnin ƙasar.

    Lamarin ya faru ne ana daf da kammala buga wasan, wanda Arsenal ta samu nasara da 2-0.

    Wani ɗan jarida a yankin ya faɗa wa BBC cewa mai kula da wajen da ake kallon wasan ya fusata da irin hayaniyar da magoyan Arsenal ɗin ke yi, inda ya buƙaci jami'in tsaron da ya ɗauki mataki.

    Sai dai mutanen ba su saduda ba, inda suka ci gaba da murna da sowa.

    Wani shaida ya faɗa wa ɗan jaridar cewa, mai wajen cin abincin da kuma ake kallon wasan ya kashe injin da ke bayar da hasken wuta a wajen, abin da ya fusata masu kallon har ta kai suka ƙara ihu fiye da farko.

    A lokacin ne kuma ake zargin mai gadin wurin ya buɗe musu wuta.

    An ruwaito cewa wanda lamarin ya rutsa da shi John Ssenyonga, mai shekara 30, ya mutu nan take a wajen.

    An kuma garzaya da wani magoyin bayan Arsenal ɗin Lawrence Mugejera zuwa asibiti bayan samun raunuka.

    Mai gadin da kuma manajan da ke kula da wurin sun tsere bayan faruwar lamarin, inda jamin'an tsaron ke ci gaba da farautarsu.

  3. Shugaban ƙasar Koriya ta Kudu ya so a kama shugaban jam'iyyarsu

    Koriya ta Kudu

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban ƙasar Koriya ta Kudu, Yoon Sul Yeok ya bayar da umarnin a kama shugaban jam'iyyarsu mai mulki, Han Dong-hoon bayan ya sanar da fara mulkin soji a daren Talata.

    Daga cikin waɗanda ya umarci a kama har da shugaban babbar jam'iyyar hamayya, Lee Jae-myung, da wasu ƴan majalisar hamayya guda uku, kamar yadda hukumar leƙen asiri ta ƙasar ta bayyana.

    Shugaban ƙasar ya yi yunƙurin, "amfani da ƙarfin iko domin ya sa a kama su, a ɓoye su," in ji daraktan hukumar, Hong Jang-won.

    Wannan maganar ta fito ne a daidai lokacin da jagororin jam'iyyun ƙasar suka ta gudanar da taruka, sannan kuma ƴanmajalisar ƙasar suka yunƙursin kaɗa ƙuri'ar tsige shugaban ƙasar.

    Babbar jam'iyyar hamayyar ƙasar ya ce a ranar Asabar ne za a kaɗa ƙuri'ar.

    Jam'iyyar hamayya ce ke da mafi rinjaye a majalisar mai mambobi 300, amma tana buƙatar akalla ƴanmajalisa takwas na jam'iyya mai mulki domin samun ƙuri'a 200 da ake buƙata domin tsige shugaban ƙasar.

  4. Shugaban jam'iyya mai mulki a Koriya ta Kudu ya buƙaci shugaban ƙasar ya sauka

    Koriya ta Kudu

    Asalin hoton, AFP

    Shugaban jam'iyya mai mulki a Koriya ta Kudu ya buƙaci a gaggauta sauke shugaban ƙasar Yoon Suk Yeol daga karagar mulki, bayan ya yi yunƙurin ayyana dokar mulkin soja a ƙasar a farkon makon nan.

    Duk da dai an yi watsi da matakin Han Dong-hoon, ya yi gargaɗin cewa akwai haɗarin Mista Yoon na iya ƙoƙarin sake ɗaukar matakin da zai jefa ƙasar da ƴan ƙasar cikin tashin hankali.

    Wakiliyar BBC ta ce wannan ita ce alamar farko da ke nuna cewa jam'iyyar shugaban ƙasar na iya haɗa hannu da ƴan adawa domin kaɗa ƙuri'ar tsige shi.

  5. Yunwa ta kashe yara sama da 800 a Katsina - MSF

    MSF

    Asalin hoton, BBC World Service

    Ƙungiyar agaji ta likitoci ta Medecins Sans Frontieres MSF ta kaɗa ƙararrawa a game da abin da ta bayyana da matsananciyar yunwa da take ƙara ƙamari a yankin arewa maso yammacin Najeriya.

    Ƙungiyar ta ce sama da yara 800 ne suka rasu a asibitotin da take aiki a Katsina a cikin wata tara da ta yi tana tattara bayanai a bana.

    A wata ƙididdiga ta kwana-kwanan nan, an gano cewa sama da kashi na waɗanda ta duba a ƙananan hukumomi uku na jihar suna fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki.

    Masana sun ce matsalar za ta iya ta'azzara saboda rashin kai agaji, da ƙarancin samar da abinci da ma tsadarsa.

  6. Kwamitin Amintattun PDP ya buƙaci a kira taron majalisar ƙoli

    PDP

    Asalin hoton, PDP

    Kwamitin Amintantun jam’iyyar PDP ya nuna takaicinsa kan yadda shugabancin jam’iyyar ke ta ɗage taron ƙolin jam’iyyar, inda jama'iyyar ƴan kwamitin suka buƙaci a kira taron nan da watan Fabarerun 2025.

    Haka kuma kwamitin amintatun ya yi kira ga shugabancin jam’iyyar na yankin arewa maso tsakiya Najeriya da su gaggauta warware rikicin da ke tsakaninsu sannan su gabatarwa jam’iyyar wanda zai kammala wa’adin Iyorchia Ayu da aka dakatar, kasancewar wa'adin mulikinsu ne.

    Ambasada Aminu Suleiman Wali dwanda ɗaya ne daga ciki ƴan kwamitin amintatun na Jam’iyyar PDP ne ya bayyana wa BBC haka a tattaunawarsa da BBC.

  7. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Juma'atu babbar rana daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu riƙa kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sadarwa domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo.

    Ku kasance tare da mu.