Masu bin shafin BBC Hausa kai-tseye a nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.
Amma kafin nan muke cewa mu kwana lafiya
Mutum 370,000 ne suka rasa muhallansu a Syria - MDD
Asalin hoton, Reuters
Aƙalla mutum 370,000 aka tilasta wa barin gidanjensu a Syria tun bayan da 'yantawaye suka fara ƙaddamar da manyan hare-hare a makon da ya gabata.
Majalisar Duniya ta ce ana fargabar adadin ka iya kai wa miliyan 1.5
"Tun bayan ɓarkewar rikicin, aƙalla mutum 370,000, maza ta mata da ƙananna yara ne aka tilasta wa barin muhallansu, ciki har da mutum 100,000 da aka raba da muhallansu har sau biyu'', a cewa kakakin babban sakataren Majalisar, Stéphane Dujarric.
Tun da farko, shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta majalisar, Samer AbdelJaber ya bayyana a taron shirin samar da abinci na Majalisar Dinki Duniyar cewa adadin mutanen da suka rasa muhallansu ya kai 280,000.
Idan yanayin ya ci gaba a haka ''kusan mutum miliyan 1.5 za su rasa muhallansu, tare da buƙatar tallafinmu'', in ji Samer AbdelJaber.
'An kashe mutum 20 a hare-haren da syria da Rasha suka ƙaddamar a kusa da Homs'
Ƙungiyar kare haƙƙi bil-adama ta Syria, wato 'Syrian Observatory for Human Rights' mai lura da yaƙin syraia ta ce mutum 20 aka kashe ciki har da ƙananan yara, a wani harin haɗi gwiwa da Rasha da Syria suka ƙaddamar a kusa da birnin Homs.
Homs shi ne birni na uku mafi girma a Syria, kuma a nan ne ƙungiyar 'yantawaye - ta 'Hayat Tahrir al-Sham' ke jagorantar hare-hare, a birnin bayan ƙwace iko da biranen Aleppo and Hama.
Daraktan ƙungiyar, Rami Abdel Rahman, ya ce biyar daga cikin waɗanda aka kashen 'yan gida ɗaya ne.
Rundunar sojin Ghana ta baza jami'anta a ƙasar don tabbatar da tsaro a lokacin zaɓe
Asalin hoton, Ghana Armed Forces/X
Rundunar sojin Ghana ta baza jami'anta a sassan ƙasar domin tabbatar da tsaro a lokacin zaɓen shugaban ƙasar da za a gudanar ranar Asabar.
Cikin wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na rundunar sojin ƙasar, Birgediya Janar E Aggrey-Quashie ya fitar, ya ce an tura sojojin ne domin taimaka wa 'yansanda wajen samar da tsaro a lokacin zaɓen.
''Babu ko sajanmu guda da zai kasance a rumfar zaɓe, za dai su riƙa sintiri a gari domin tabbatar da tsaro a faɗin ƙasar'', in ji sanarwar.
Janar E Aggrey-Quashie ya ce an aike da dakarun sojin ne bisa buƙatar hakan daga rundunar 'yansandan ƙasar.
Ya ƙara da cewa rundunonin biyu za su yi aiki tare don tabbatar da tsaro a lokacin zuɓukan na ranar Asabar.
Jordan ta rufe kan iyakarta da Syria yayin da 'yantawaye ke ci gaba da nausawa
Ƙasar Jordan ta ce ta rufe kan iyakarta da Syria, yayin da sojojin Syria suka ce 'yantawayen sun kai hari kan mashigar kan iyakar.
Ita ma Isra'ila ta ce tana ƙarfafa dakarun tsaronta a tuddan Golan da aka mamaye, kuma tana cewa ba za ta ''ƙyale duk wata takala ba''.
Ministocin harkokin wajen ƙasashe uku masu ƙarfin faɗa a ji a Syria - Turkiyya da Iran da kuma Rasha - za su gana a gobe Asabar domin tattauna yadda yaƙin ke bazuwa cikin sauri a ƙasar.
Wani babban jami'i a Iran ya ce Tehran na shirin aikewa da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa da kuma mashawartan soji domin taimaka wa shugaba Assad.
A nasa ɓangare shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan ya ce yana fatan 'yantawayen Syria za su ci gaba da dannawa a yaƙin da suke yi da gwamnatin ƙasar.
Tinubu ya naɗa sabon shugaban hukumar kula da jami'o'i ta Najeriya
Asalin hoton, Bayo Onanuga/X
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya naɗa Farfesa Abdullahi Yusuf Ribadu, a matsayin sabon shugaban hukumar kula da jami'o'in ƙasar, NUC.
Naɗin na ƙunshe cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar a ranar Juma'a.
Farfesa Ribadu - wanda ƙwararren masanin lafiyar dabbobi ne - ya taɓa riƙe shugaban jami'ar fasaha ta tarayya da ke Yola da kuma jami'ar Sule Lamido da ke jihar Jigawa.
Haka kuma shugaba Tinubu ya naɗa shugaban jami'ar Al-Istiqamah da ke Kano, Farfesa Salisu Shehu a matsayin shugaban majalisar binciken ilimi da ci gaba ta Najeriya, NERDC.
Ghana ta rufe iyakokinta kafin fara kaɗa ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasa
Ma'aikatar lura da shige da fice ta Ghana ta sanar da rufe iyakokin ƙasar na ƙasa saboda shirin zaɓen shugaban ƙasa da za a gudanar a gobe Asabar.
Wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar a yau ta ce matakin na ɗan lokaci ne kuma an ɗauke shi ne "domin tabbatar da sahihancin sakamakon zaɓen".
Ta ce matakin ya fara aiki nan take kuma zai gama aiki zuwa ƙarfe 6:00 na yammacin Lahadi.
A jiya Alhamis ne aka kammala gangamin yaƙin neman zaɓe, inda ake ganin fafatawar za ta fi zafi tsakanin Mahamudu Bawumia na jam'iyyar NPP mai mulki, da John Mahama na NDC mai adawa.
Darajar naira ta ɗan farfaɗo a ranar Juma'a
Asalin hoton, Getty Images
Darajar kuɗin Najeriya naira ta ɗan ƙaru a ranar Juma'a a kasuwar bayan fage bayan kaddamar da sabon tsari da akayi a makon da ya gabata da ke lura da yawan buƙatar kuɗaɗen ƙasar waje.
Kuɗin na naira ya samu ƙarin tagomashin naira 100 a kan dala, lamarin da ya sa dalar ta koma naira 1,580, saɓanin 1,680 da take a ranar alhamis.
A kasuwar hukuma kuwa, an sayar da dalar kan naira 1,575.
A makon da ya gabata ne Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi watsi da tsarin cinikayyar canjin kuɗi hannu da aka shafe kusan shekara 10 ana amfani da shi, domin ya bunƙasa hada-hadar kuɗin da kuma cire abubuwan da ke kawo cikas a hada hadar kuɗin.
Darajar Naira ta riƙa karyewa a baya bayan nan, sakamakon ƙaruwar buƙatar da akeyi na kuɗaɗen ƙasar waje bayan ƙasar ta ɗage wasu ƙa'idojin hada hadar kuɗi
'Yantawayen Syria na dab da ƙwace birni na uku mafi girma a ƙasar
Rahotanni daga Syria sun ce 'yantawayen ƙasar na dab da shiga Homs, birni na uku mafi girma a Syria, a yayin da suke ci gaba da dannawa bayan kwace birnin Hama a ranar Alhamis.
Dubban mutane ne ke tserewa daga birnin a yau Juma'a.
Wani jami'i a hukumar kula da 'yan gudun hijira a Syria da ya bar birnin Homs a safiyar yau ya ce ana cikin yanayi da fargaba da kuma tserewa.
''Mutane da dama sun tsere yayin da ƙalilan ɗin da suka rage kuma ke cikin fargaba, a duk lokacin da aka ji kara mutane na tsorata'', in ji shi.
Kwace birnin Homs zai rusa babbar hanyar da ke kai wa Damascus babban birnin ƙasar.
Dakarun Syria sun ce sun kai wa matattarar 'yantawayen hari da jirage sama na yaƙi.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan mutum 300,000 sun rasa muhallansu a Syria tun bayan sake ɓarkewar yaƙin basasar a makon daya gabata.
Shugabanni a Najeriya na alhinin rasuwar Sheikh Muyideen Bello
Asalin hoton, Babajide Sanwo-Olu
Shugabanni da manyan 'yan siyasa a Najeriya na ci gaba da alhinin rasuwar fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Najeriya, Sheikh Muyideen Ajani Bello da ya rasu a ranar Juma'a.
Shugaban ƙasar, BolaTinubu ya ce ya kaɗu da jin labarin rasuwar malamin addinin.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Tinubu ya bayyana malamin da mai basira - wanda Allah ya huwace masa fikirar karantar da addinin, da ya ce ya taimaka wa rayuwar mutane da dama a ƙasar.
Shi ma jagoran adawar ƙasar, Atiku Abubakar, ya ce malamin ya sadaukar da rayuwarsa wajen karantar da mutane addini a ciki da wajen ƙasar.
''Ya kasance mai koyar da tarbiyya da zaman lafiya, kodayaushe huɗubarsa na mayar da hankali wajen ƙara haɗin kai da kyautatuwar al'umarmu,'' in ji Atiku Abubkar.
A nasa ɓangare, gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya ce za a riƙa tuna marigayin da irin jajircewarsa wajen yaɗa da'awar Musulunci da riƙon gaskiya da amana da mutuntawa da kuma ƙoƙarin ingantar tarbiyyar al'umma.
Daga ƙarshe dukkansu sun yi addu'ar neman gafarar ubangiji ga marigayin tare da jajanta wa iyalansa.
Sojojin Najeriya sun musanta zargin Amnesty na mutuwar fararen hula 10,000 a hannunsu
Asalin hoton, Defence HQ/X
Shalkwatar tsaron Nsjeriya ta musanta zargin da ƙungiyar kare haƙƙin bil-adama ta Amnesty International, ta yi cewa mutum 10,000 ne suka mutu a hannun sojojin, tun bayan ɓarkewa rikicin Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya.
Daraktan ƙungiyar Amnesty a Najeriya, Mallam Isa Sanusi ne bayyana zargin sojojin da hannu a mutuwar mutanen da sauran nau'ikan cin zarafi, a wani jawabi da ya yi a tarin manema labarai a birnin Maiduguri.
Isa Sanusi a ce tuni ƙungiyarsu ta shigar da ƙara gaban kotun hukunta manyan laifuka ta ICC da ke birnin Hague kan zarge-zarge take haƙƙin ɗan'adam da take yi wa sojojin a yankin arewa maso gabashin ƙasar.
To sai dai yayin da take mayar da martani shalkwatar tsaron ƙasar, cikin wata sanarwa da kakakinta, Manjo Janar Edward Buba ya fitar ranar Juma'a ya bayyana zarge-zargen da masu tayar da hankali, kuma marasa tushe, kuma marasa hujja'.
''Duk da cewa yaƙin da sojoji ke yi a yankin Arewa maso gabashin Najeriya mai sarƙaƙiya ne cike da ƙalubale, muna bin ƙa'idojin da suka kamata. A duk lokacin da muka kama waɗanda ake zargi bayan ɗaukar bayanansu, mukan miƙa su hannun hukumomin da ya kamata domin a sake su ko a gurfanar da su a gaban kotu,'' in ji Manjo Janar Edward Buba.
Sanarwar ta kuma ce shalkwatar tsaron ta gayyaci ƙungiyar ta Amesty zuwa ofishinta domin tabbatar da zarge-zargen.
Malamin addinin Musulunci a Najeriya Sheikh Muyideen Bello ya rasu
Asalin hoton, BABAJIDE SANWO-OLU/FACEBOOK
Fitaccen malamin addini Musulunci nan na Najeriya, Alhaji Muyideen Ajani Bello, ya rasu.
Wani makusancinsa, Alhaji Taofeeq Akeugbagold ya shaida wa BBC cewa malamin ya rasu ne a yau Juma'a a gidansa.
An haifi fitaccen malamin a shekarar 1940 a birnin Ibadan na Jihar Oyo.
Sheikh Ajani Bello ya rasu yana da shekara 84.
Cutar Lassa ta kashe mutum 23 a jihar Ebonyi
Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin jihar Ebonyi da ke kudu maso gabashin Najeriya ta ce cutar Lassa ta kashe mutum 23 a faɗin jihar.
Gwamna Francis Nwifuru ne ya bayyana haka ranar Alhamis yayin wani biki da ma'aikatar lafiya a jihar ta shirya a Abakaliki babban birnin jihar.
Gwamnan ya ce wasu mutum 48 sun kamu da cutar cikin 394 da aka yi wa gwaji a faɗin jihar daga watan Janairu zuwa Disamban 2024, a wani yunkuri na inganta harkokin lafiya a yankunan karkara.
Nwifuru ya bayyana cewa jihar na shirye-shiryen gina asibiti guda a mazaɓun jihar guda uku domin bunƙasa aikin kiwon lafiya.
Sojoji kaɗai ba za su iya samar da tsaro a ƙasa ba - Janar Chris Musa
Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya ce karfin soji kaɗai ba zai samar da tsaron da ake buƙata ba a Najeriya.
Ya ce amfani da karfin soji na bayar da gudummawar kashi 30 cikin ɗari ne kacal na tsaron ƙasa, yayin da kashi 70 ya dogara kan siyasa da kuma tallafi ga walwala da na tattalin arzikin al’umma.
Janar Musa ya bayyana haka ne a wani taro kan tsaron ƙasa da cibiyar daƙile ayyukan ta'addanci karkashin ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro ya shirya a Abuja.
Babban hafsan ya buƙaci haɗin gwiwa wajen daƙile matsalar rashin tsaro a Najeriya.
"Dole ne a haɗa karfi da karfe wajen magance matsalar tsaro, musamman ganin rikice-rikice da kuma rashin tabbas da ya dabaibaye mutane," in ji shi.
Ya ce mutane sun ɗauka cewa sojoji ne kaɗai za su samar da tsaro ba tare da la'akari kan irin gudummawar da kowane ɓangare zai bayar ba wajen tabbatuwar hakan.
Ya ƙara da cewa ƴan jarida ma na da rawar da za su taka wajen tabbatar da tsaro a faɗin Najeriya.
An tilasta wa wasu Musulmai sayar da gidansu bayan zanga-zangar ƴan Hindu
Asalin hoton, Shahbaz Anwar
Wasu mabiya addinin Hindu sun tilastawa makwabtansu Musulmai a Indiya tashi daga sabon gidansu.
Ƴan Hindu da dama da ke zama a wani yanki a arewacin
birnin Moradabad da ke jihar Uttar Pradesh ne, ke gudanar da zanga-zanga tun
bayan samun labarin sayar da gidan ga hannun Musulmi ranar Talata.
Yanzu dai ma'auratan sun sayar da gidan.
Masu
gwagwarmaya sun ce bambancin da ake nuna wa tsirarun kabilu musamman Musulmai, ya
zamo ruwan dare gama duniya a yawancin biranen ƙasar ta India.
Masu
suka sun ce ana yawan musgunawa Musulmi a India a karkashin gwamnatin Narendra
Modi, abin da magoya bayansa ke musanta wa.
An jinkirta komawar ɗan'adam duniyar wata
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kula da sararin samaniyar ta Amurka NASA, ta sanar da jinkirta shirye-shiryen komawa duniyar wata.
Shugaban hukumar, Bill Nelson, ya ce a yanzu an tsara komawa duniyar ta wata ne watan Afrilun 2026.
Dama dai an tsara aika ƴan sama jannati zuwa wata, amma ba za su sauka ba sai watan Satumban 2025.
Hakan dai na nufin cewa babu wani ɗan sama jannati da zai sauka a duniyar wata har sai aƙalla 2027.
An ɗauki matakin ne domin gyara wata matsala a kumbon da aka yi amfani da shi wajen gwajin tafiyar a baya sakamakon lalacewa da kuma tsagewa har ma wasu sassan shi suka karye.
"An jinkirta tafiyar har sai an shirya tsaf," in ji Bill.
Ya shaida wa wani taron manema labarai cewa kare lafiyar ƴan sama jannatinsu na da muhimmanci.
Fararen hula 10,000 ne suka mutu a hannun sojojin Najeriya - Amnesty
Asalin hoton, AMNESTY INTERNATIONAL
Ƙungiyar kare hakkin ɗan'adam ta Amnesty International ta yi zargin cewa fararen hula kusan 10,000 ne suka mutu a hannun sojojin Najeriya, tun bayan fara yaƙi da ƙungiyar Boko Haram a arewa maso gabas.
Shugaban ƙungiyar ta Amnesty a Najeriya, Isa Sanusi, wanda ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Maiduguri, ya kuma zargi Boko Haram da sojoji da laifukan take ƴancin ɗan'adam.
A cewarsa, dakarun soji sun take ƴancin bil'adama yayin gudanar da ayyukansu a yankin na arewa maso gabas.
Ya nuna takaicinsa kan yadda sojoji suka musanta hannunsu a lamarin bayan gabatar musu da rahoton da Amnesty ta yi kafin ta fitar da shi ga jama'a.
Sanusi ya ce tuni ƙungiyar ta shigar da ƙara gaban Kotun Duniya da ke Hague, kan zargin take ƴancin ɗan'adam a arewa maso gabas.
Iran za ta tura makamai da jirage marasa matuƙa zuwa Syria
Asalin hoton, Getty Images
Iran na shirin tura makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa zuwa Syria, kamar yadda wani jami'i ya shaida wa kafar yaɗa labaru ta Reuters.
Haka nan kuma Iran ɗin za ta ƙara yawan masu bayar da shawara kan tsaro waɗanda za su taimaka wa shugaban na Syria, Bashar al-Asad.
Yanzu haka dai Iran na taimaka wa gwamnatin Syria da bayanai da kuma tattara bayanai da tauraron ɗan'adam, kamar yadda hukumomi suka tabbatar.
Ku San Malamanku tare da Gwani Yahuza Gwani Danzarga
Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyon
Gwani Yahuza, ɗaya ne daga cikin 'ya'yan Gwani Salihu Danzarga, wanda ya shahara wajen karantar da Alƙur'ani mai girma a ƙwaryar birnin Kano.
Ya gaji mahaifinsa wajen karantar da littafin mai tsarki, kuma shi ne shugaban makarantar Gwani Zanzarga a birnin na Kano, wadda ta yaye dubban mahaddata Ƙur'ani.
Ya shugabanci rukunin alƙalan musabaƙar Ƙur'ani ta Najeriya, sannan ya wakilci ƙasar a matsayin alƙali musabaƙar ta duniya da aka yi a Saudiyya.
Kafin haka, ya yi karatu a wurare da dama ciki har da jami'ar Azhar da ke ƙasar Masar.
An jibge jami'an tsaro a fadar masarautar Kano, Abubakar Macciɗo
Bayanan hoto, Fadar Kano da ke Ƙofar Kudu ita ce gidan sarkin Kano a hukumance, inda Sarki Muhammadu Sanusi II ke da zama
An ga ƙarin jami'an tsaro a fadar sarkin Kano da ke Ƙofar Kudu a yau Juma'a.
Hakan ya kawo cikas ga zirga-zirga da shige da fice a cikin fadar mai ɗimbin tarihi, inda Sarki Muhammadu Sanusi II ke da zama.
Za a iya ganin jami'an tsaro da kuma motocin tarwatsa masu zanga-zanga waɗanda aka jibge a fadar.
Bayanai sun nuna cewa a yau ne aka tsara cewa Sarki Muhammadu Sanusi II zai yi wa ɗaya daga cikin masu riƙe da sarauta mafi girma a masarautar, Wamban Kano, Mannir Sanusi rakiya zuwa Bichi domin kama aiki a matsayin hakimi.
Sai dai jibge jami'an tsaron ya janyo cikas ga faruwar hakan.