Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 11/04/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 11/04/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Isiyaku Muhammed da kuma Aisha Bappa

  1. Al'umma na son a ayyana fyaɗe a matsayin annobar da ta addabi jama'a a Afirka ta Kudu

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Daruruwan mutane ne suka yi maci a Afirka ta Kudu inda suke kira da a ayyana cin zarafin mata ta hanyar lalata da kuma kashe-kashen mata a matsayin annoba.

    Masu zanga-zangar na son a kara kaimi wajen dakile wannan matsala.

    A cewar 'yansandan Afirka ta Kudu, a kowacce rana su na samun rahoton aikata fyade fiye da 100.

    An gudanar da zanga-zanga da dama a sassan kasar.

    A Pretoria, mutane su je fadar gwamnatin kasar da kuma gine-ginen kungiyoyi da dama domin mika kokensu.

  2. Hukumar ayyukan jin kai ta MDD za ta rage ma'aikata a Najeriya da Pakistan da Iraqi

    Hukumar kula da ayyukan jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya, OCHA, ta sanar da cewa za ta rage ma'aikata fiye da 2000 a abin da ta kira rage ayyyukan yi.

    Hukumar na fuskantar karancin kudin tafiyar da ayyukanta inda a yanzu haka ta ke da gibin kusan dala miliyan 60, a don haka ta ce dole ne ta rage ayyukanta a wasu kasashe ciki har da Najeriya da Pakistan da kuma Iraqi.

    Yawancin kungiyoyi agaji na fuskantar karancin tafiyar da kungiyarsu tun bayan da shugaba Trump ya karbi mulki a Amurka.

    Bayan hawansa mulki ne shugaba Trump ya sanar da rage kudaden tafiyar da wasu shirye-shirye da hukumar USAID ke yi.

    Hukumar ta Amurka ita ce ke bayar da gudunmuwar kashi 40 cikin 100 na kudaden ayyukan tallafi a duniya.

  3. An kashe gwamman mutane a Sudan

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, .

    Rahotanni daga yammacin Sudan na cewa an kashe gwamman mutane a wani hari da dakarun RSF suka kai birnin El Fasher da wani sansani.

    Kungiyoyin agaji sun ce mayaƙan sun kai harin ne da manyan makamai na artilary da jirage marassa matuka, lamarin da ya yi sanadin rayuka sama da 30.

    Sojojin Sudan ne dai ke iko da birnin Darfur.

    Dakarun RSF sun kuma kai hari sansanin Zam Zam, inda ma'aikatan sa kai ke cewa an kashe mutum 25.

  4. Dalilanmu na haramta yaɗa waƙar 'Tell Your Papa' ta Eedris Abdulkareem - Gwamnati

    Abdulkareem

    Asalin hoton, abdulkareemeedris/Instagram

    Gwamnatin Najeriya ta haramta watsa waƙar 'Tell Your Papa' ta fitaccen mawaƙin kudancin Najeriya, Eedris Abdulkareem.

    A waƙar, mawaƙin ya yi kira ne ga ɗan shugaban ƙasar, Seyi Tinubu da ya faɗa wa mahaifinsa cewa, "mutane suna mutuwa" saboda ƙuncin rayuwa da rashin tsaro, sannan ya ƙara da cewa, "akwai yunwa" a ƙasar.

    A wata wasiƙa da hukumar kula da kafofin labarai ta Najeriya wato NBC ta fitar, ta buƙaci kafofin yaɗa labarai na ƙasar da su guji saka waƙar domin a cewarta, ta saɓa da dokokin yaɗa labarai na Najeriya.

  5. 'Yansandan Najeriya sun kashe 'yan bindiga biyar da ceto dalibin jami'a

    Kayode Egbetokun

    Asalin hoton, Nigeria Police

    Rundunar 'yan sandan Najeriya, ta ce ta samu nasarar kubutar da dalibin jami'ar Kebbi Augustine Madubiya, wanda aka sace tun a ranar 8 ga watan Afrilu a unguwar Jeji,da ke karamar hukumar Kalgo a jihar Kebbi.

    Aikin ceton da rundunar ta yi ya hada da jami'an 'yansanda da kuma 'yan banga a dajin Dakingari.

    Rundunar ta ce ta ceto dalibin ba tare da an ji masa rauni ko kodan ba kuma yanzu haka yana karbar magani kafin a hada shi da iyalansa.

    Kazalika rundunar 'yansandan ta ce ta kai samame maboyar 'yan bindiga a kauyen Dutsen Wori da ke karamar hukumar Dandume a jihar Katsina inda har ta yi nasarar kashe 'yan bindiga biyar tare da kwato babura 7 wanda suke amfani dasu wajen kai hare-hare.

    A bangare guda kuma rundunar 'yansandan ta ce wata tawagar jami'anta da ta yi amfani da bayanan da ta samu ta tare wasu 'yan bindiga da ta ke zargi a kauyukan unguwar Adam da unguwar Judo, a karamar hukumar Dan Musa inda har ta nasarar tisa keyar mutum uku da ake zargi da kai wa 'yan bindigar bayanai tare da kwace babura biyu.

    Rundunar 'yansandan ta ce tana wannan aiki ne domin kawar da bata garin da suke addabar mutane da kuma tabbatar da tsaro da rayukan al'umma.

  6. Gwamnan jihar Borno ya gana da manyan hafsoshin tsaron Najeriya kan matsalar tsaron jiharsa

    Farfesa Babagana Umara Zulum

    Asalin hoton, ZULUM/X

    Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi wata muhimmiyar ganawa da manyan hafsoshin tsaron kasar a Abuja a ranar Alhamis domin fito da wani sabon tsarin yaki da mayakan Boko Haram sa suka sake kunno kai a wasu sassan jiharsa.

    Taron dai na zuwane kwanaki biyu bayan da ya koka kan cewa wasu sassan jiharsa sun kubucewa ikon gwamnati sun koma karkashin ‘yan Boko Haram.

    Gwamnan dai ya yi ganawar ne tare da rakkiyar dukkani ‘yan majalisar dattawa uku dake wakiltar jihar da kuma wasu ‘yan majalisar wakilanta.

    Senata Mohammed Tahir Mungono, dan majalisar dattawa ne dake wakiltar Arewacin jihar ta Borno, wanda kuma ke cikin tawagar gwamnan ya shaida wa BBC cewa, sun je ne domin kira ga jami'an tsaro a kan kara mayar da hankali kan jihar saboda kada Boko Haram su sake yin karfi su yi ta'addanci irin na da.

    Ya ce," Manyan jami'an tsaron sun shaida musu cewa suma basu ji dadin abubuwan da ke faruwa a jihar ta Borno ba a kwanakin bayan nan, sannan kuma za su kara mayar da hankali a kan jihar inda za a kara yawan sojoji da kayan aiki.."

  7. Hukumar NAPTIP ta kaddamar da sabbin tsare-tsaren yaki da safarar mutane

    .

    Asalin hoton, NAPTIP

    Bayanan hoto, .

    A Najeriya, hukumar yaki da fataucin bil'adama ta NAPTIP ta kaddamar da wasu sabbin tsare-tsaren yaki da safarar mutane.

    Ya yin wani taron masu ruwa da tsaki da hukumar ta shirya a Abuja, ta bayyana cewa a yanzu suna amfani da sabbin dabarun yaki da matsalar ciki har da manhajojin dijital, don samun bayanai.

    Hukumar za ta kaddamar da shirye-shiryen wayar da kai da kuma kaddamar da jami'an tsaro masu yaki da fataucin mutane sama da 200.

    NAPTIP ta sanar da cewa sun kubutar da fiye da mutum dubu bakwai wadanda aka yi yunkurin fita da su da kuma wadanda aka yi safararsu daga Najeriya.

    Rahotanni sun ce matsalar safarar mutane na karuwa a sassan Najeriya,

    Kungiyoyin da ke kare hakkin dan adam da kuma masu yaki da fataucin bil adama, na jaddada cewa akwai bukatar NAPTIP ta kara hada kai da jami'an tsaro da kungiyoyi da kuma hukumomin kula da shige da fice, sannan kuma gwamnati ta samar da yanayin da zai sa mutane su daina ficewa daga kasarsu da kuma tabbatar da cewa ana hukunta mutanen da ke safarar mutane don ya zama darasi ga masu niyyar aikata laifin.

  8. Ambaliya ta ɓarnata sama da gidaje 300 a Kebbi

    Ambaliya

    Asalin hoton, Getty Images

    A Najeriya, jama'ar garin Kestu na yankin ƙaramar hukumar Shanga a jihar Kebbi, suna dakon ƙarin ɗauki, sakamakon wani gagarumin ruwan sama da guguwa mai ƙarfi da suka auka wa garin.

    Al'amarin dai ya ɓarnata gidaje kusan 300 da kayan abinci, sannan da hallaka dabbobi, amma babu asarar ran mutum ko ɗaya.

    Bayanai dai sun ce, ƙaramar hukumar ta Shanga da gwamnatin jihar Kebbin suna ƙoƙarin ganin an tallafa wa mutanen da wannan iftila'i ya shafa, baya ga agajin farko da matar gwamnan jihar ta aika da shi.

  9. Dala ta karye a kan manyan kuɗaɗen duniya

    Dala

    Asalin hoton, Getty Images

    Farashin dala ya karye a kan manyan kuɗaɗe a kasuwanni duniya, yayin da aka shiga rashin tabbas sakamakon manufofin Donald Trump na kasuwanci da ke haifar da fargaba tsakanin masu zuba jari.

    Farashin dala ya yi faɗuwar da ya jima ba a gani ba a shekaru kan kuɗin Switzerland.

    Haka ma ya yi ƙasa sosai kan kuɗin Yuro.

    Sannan wayewar garin Juma'a, farashin zinare ya kai matakin da aka jima ba a gani ba, yayin da ƴan kasuwa ke laluben neman kadarorin da za su siya domin kaucewa asara a wannan lokaci na rashin tabbas a kasuwanni hanayen jari na duniya.

  10. Gwamnatin Najeriya ta kafa kwamitin bincike kan kisan matafiya a Edo

    Kano

    Asalin hoton, KNSG

    Gwamnatin Najeriya tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar Edo ta kafa kwamitin bincike kan kisan matfiya guda 16 da aka kashe a Uromi a kan hanyarsu ta komawa jihar Kano.

    Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar gwamnatin jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar, Kwamrade Aminu Abdussalam Gwarzo, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

    Okpebholo ya ce Shugaba Tinubu bai ji daɗin abin da ya faru ba na kisan matafiyan a Uromi, kuma a shirye yake ya bi diddigin lamarin domin kare sake aukuwar lamarin.

    "Ina tabbatar muku cewa gwamnatin tarayya da ta Edo sun kafa kwamitin bincike domin gano haƙiƙanin abin da ya faru domin magance matsalar baki ɗaya.

    "Wannan rahoton da kuka kawo mana zai taimaka wajen sauƙaƙa mana bincike, don haka kada ku damu. Za mu yi abin da ya dace, kuma za mu fitar da sakamakon binciken domin kowa ya gani."

    Mataimakin gwamnan jihar Kano ya yi godiya ga gwamnan jihar Edo Monday Okpebholo bisa ƙoƙarinsa na tabbatar da adalci.

  11. Atiku da El-Rufa'i da Tambuwal sun ziyarci Buhari a Kaduna

    Tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar

    Asalin hoton, X/Atiku Abubakat

    Bayanan hoto, Tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar

    Tsohon ɗantakarar shugaban ƙasa a Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a Kaduna.

    Daga cikin waɗanda suka raka Atiku akwai tsofaffin gwamnonin jihohin Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da na Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da wasu jiga-jigan ƴansiyasa.

    Atiku ya wallafa bidiyon ziyarar a shafinsa na Facebook, sannan ya rubuta cewa sun ziyarci Buharin, kuma sun sha dariya.

    "A matsayina na Wazirin Adamawa, na tsaya domin gudanar da shagungulan Sallah a Adamawa, inda na wakilci Sarkin Adamawa, Lamiɗo Fombina a wasu shagulgulan.

    "Yau kuma na kai ziyarar gaisuwar Sallah ga Muhammadu Buhari wanda ya shugabanci ƙasar a tsakanin 2025 zuwa 2023. Na ji daɗin ziyarar, saboda kamar yadda ya saba, ya yi ta ba mu dariya sai da haƙarƙarina suka yi zafi."

    Sai dai Atikun bai yi ƙarin haske kan ko akwai wani abu mai alaƙa da siyasa da suka tattauna da tsohon shugaban ƙasar ba a lokacin ziyarar.

    A baya-bayan nan ƴansiyasa da manyan jami'an gwamnati na yawan kai wa tsohon shugaban ziyara tun bayan da ya koma gidansa na Kaduna daga Daura, inda ya shafe shekaru biyu tun bayan sauka daga mulki.

    Ziyara ta ƙarshe da ta fi ɗaukar hankalin al'umma ita ce wadda tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya kai wa tsohon shugaban ƙasar, inda jim kaɗan bayan hakan ya ayyana ficewa daga jam'iyyar APC mai mulki zuwa jam'\iyyar SDP, wani lamari da ake ganin zai sauya salon siyasar ƙasar gabanin babban zaɓen shekara ta 2027.

  12. 'Rasha na tarnaƙi kan kawo ƙarshen yaƙin Ukraine'

    Rasha

    Asalin hoton, Reuters

    Ministan tsaron Jamus ya ce cigaba da kai hare-hare da Rasha ke yi a kan Ukraine na nufin da wuya a cimma yarjejeniyar zaman lafiya a yanzu.

    Boris Pistorius na waɗannan kalamai ne a taron ministocin Turai da ake gudanarwa kan Ukraine a Brussels.

    Ya ce "mun yi duk abin da muke ganin za mu iya, da hakan nake sanar da ƙarin taimakon soji ga Ukraine daga Jamus, da suka haɗa da tsaron sararin samaniya da tankokin yaƙi."

    Sama da ƙasashe 50 suka halarci wannan taro - amma sakataren harkokin tsaron Amurka ya shiga taron ne ta intanet.

  13. 'Najeriya za ta ci gaba da matsawa har sai an saki Bazoum'

    Mohammed Bazoum

    Asalin hoton, Getty Images

    A ranar Juma'a ne Najeriya ta sake kiran da a sako hamɓararren shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum da matarsa.

    Mohammed Bazoum ya kasance a tsare tun bayan da sojoji suka yi juyin mulki a ƙasar a watan Yulin 2023.

    An hamɓarar da gwamnatin nasa ne a ranar 26 ga watan Yulin 2023, bayan ya shafe shekaru a kan mulki.

    Shugaban masu tsaron lafiyarsa Janar Abdourahamane Tiani, ne ya jagoranci hamɓarar da gwamnatin Bazoum ɗin bayan zarge-zargen gaza kare ƙasar daga hare-haren masu iƙirarin jihadi.

    Tun daga lokacin ne Bazoum da mai ɗakinsa Hadiza ke tsare a fadar gwamnatin ƙasar da ke Yamai.

    A don haka ne gwamnnatin Najeriya ta bakin ministan yaɗa labaran ƙasar Mohammed Idris, ya yi kiran ta kafar yaɗa labaran Faransa TV Network France 24 kan a sako Bazoum da mai ɗakinsa.

    Ministan ya ce,"Muna so a fito da shi. Muna ganin bai aikata wani laifi ba, shi ɗan siyasa ne, a don haka idan kuna son cire shi sai ku bi tsarin yadda dimokuraɗiyya ta tanada."

    Ƙungiyoyi da ƙasashe da dama ciki har da ECOWAS da Majalisar Ɗinkin Duniya ne sun sha yin kira kan a sako Bazoum.

  14. UNICEF ya yi Allah wadai da ƙaruwar fyaɗe kan ƙananan yara a DR Kongo

    UNICEF

    Asalin hoton, UNICEF

    Asusun Kula da Ƙananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah wadai da ƙaruwar fyaɗe kan ƙananan yara a gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo.

    UNICEF ya ce ƙananan yara ne kashi ɗaya bisa uku na kusan mutum 1,000 da aka yi wa fyaɗe da cin zarafin lalata, da ta samu rahoto cikin wata biyu da suka gabata.

    Asusun ya ce a baya rahoton in zarafin ƙananan yara ba shi da yawa a gabashin DR Kongo, tana mai alaƙanta hakan da rikice-rikicen da ake samu a baya-bayan nan a yankin.

    UNICEF ya ce a lokacin da yaƙin ya yi ƙamari a farkon shekarar nan ana yi wa yarinya guda fyaɗe a koane rabin sa'a.

    Asusun ya ƙara da cewa ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai na amfani da fyaɗe a matsayin makamin yaƙi, wanda kuma ƴan ta'adda ke amfani da si da gangan.

    Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama sun bayar da rahoton yawaitar fyaɗe kan ƙananan yara da mayaƙan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda suka aikata.

    Majalisar Dinkin Duniya na buƙatar haɗa kai domin ɗaukar matakan gaggawa don dakatar da hare-hare da kuma rage fyaɗe.

  15. Shin Iran na son ƙulla yarjejeniyar nukiliya da Amurka?

    Iran

    Asalin hoton, Getty Images

    A wani mataki da ya zo wa mutane da dama da mamaki Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana a makon nan cewa ƙasarsa za ta ''tattauna kai-tsaye'' da Iran kan shirin nukiliyarta.

    Duk da gargaɗin da ya yi cewa za a iya ɗaukar matakin soji idan diplomasiyyar ta gagara, matakin tattaunawar wani babban sauyi ne da aka samu kan alaƙar ƙasashen biyu.

    Musamman ga shugaban ƙasar da a baya ya janye daga yarejeniyar nukiliyar Iran ta 2015 da aka yi wa laƙabi da ''2015 Joint Comprehensive Plan of Action'' (JCPOA).

  16. Gwamnatin Legas ta rufe kasuwannin jihar 13

    Legas

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin jihar Legas ta sanar da rufe wasu kasuwannin jihar 13, sakamakon saɓa doka kan zubar da shara ba bisa ƙa'ida ba.

    Cikin wata sanarwa da kwamishinan Muhalli da albarkatun ruwan sha na jihar, Tokunbo Wahab ya wallafa a shafinsa na X, ranar Juma'a ya ce matakin ya zama wajibi domin tsaftace muhalli da inganta lafiyar al'ummar jihar.

    Kwamishinan ya ce an ɗauki matakin ne bisa la'akari da dokokin kare muhalli na jihar da aka yi wa gyaran fuska a 2017, da nufin tabbatar da zuba shara a wuraren da suka dace da bin dokokin gwamnati.

    Mafi yawan kasuwannin da aka rufe na yankunan Ketu da Mile 12 - waɗanda aka rufe jiya da daddare saboda ci gaba da saɓa doka, ciki har da zuba shara a kan hanyoyi da manyan titunan jihar.

    Ga jerin kasuwannin da gwamnatin ta rufe kamar yadda kwamishinan ya wallafa a shafin nasa

    • Kasuwar Erukan da ke Mile 12
    • Kasuwar Oja Oba da ke Ketu
    • Kasuwar Owoseni Tundas
    • Kasuwar Oba Ogunjobi da ke Mile 12
    • Kasuwar Shops Owners (BRT Terminal) da ke Mile 12
    • Kasuwar tashar motoci ta Mile 12
    • Kasuwar Ketu Terminal (6 plazas)
    • Kasuwar Ifesowapo da ke Mile 12
    • Rukunin shagunan Demurin St Plaza, Ketu
    • Kasuwar The Occupant, da ke kan titin Demurin, Ketu
    • Kasuwar Ifelodun da ke Ketu
    • Kasuwar tashar Ibadan (da ke tsakanin kasuwar Babajide Sanwo-Olu da ta kayan gwari ta Ikosi)
    • Kasuwar Tipper Garage da ke Ketu
  17. Ƴan majalisar arewa maso gabas sun koka 'kan ware su' a shirin noma da kiwo na gwamnatin Najeriya

    Kiwo

    Asalin hoton, Getty Images

    A Najeriya, sanatoci da ƴanmajalisar wakilai da suka fito daga arewa maso gabashin ƙasar sun koka dangane da yadda a cewarsu gwamnatin shugaba Bola Tinibu ta mayar da su saniyar ware a wani shirin noma da kiwo da gwamnatin ke yi da haɗin gwiwar bankin cigaban Afirka.

    Ƴan majalisar sun ce yankin arewa maso gabashin Najeriya na bayar da gudunmawa a ɓangaren noma da harkokin da suka shafi kiwo a Najeriya, amma ga mamakinsu, sai aka zaɓi jihohi biyu a kowane yankin ƙasar biyar don cin gajiyar shirin amma su aka yi burus da yankinsu.

    Sanata Danjuma Goje shi ne shugaban ƙungiyar yan majalisar yankin arewa maso gabashin Najeriyar, ya bayyana a zantawarsa da BBC cewa ba a kyauta musu.

    Ya ce an zaɓi jihohi takwas ne: Kano da Kaduna da Oyo da Kuros Riba da Abuja da Kwara da Ogun da Imo.

    "Ba mu fahimci abin da aka yi ba, idan ana maganar noma da kiwo ne, bai kamata a ce an manta da jihohi shida na arewa maso gabas ba . Kowa ya san rawar da muke takawa a noma da kiwo, musamman shanu. To ai akwai ɓangarori shida a Najeriya, amma an raba wa ɓangarorin ba tare da yankinmu ba," in ji shi.

    Da aka ce masa mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ne ya jagoranci ƙaddamar da shirin, Goje ya ce Kashim ya wakilci shugaban ƙasa ne wajen ƙaddamar da shirin,"kuma shi mataimakin shugaban ƙasa ne, ba wakilin arewa maso gabas ba. Mu ne wakilan al'umma, shi ya sa majalisa na hutu, amma muka dawo domin tattauna batun."

  18. China ta ƙara harajin kayayyakin Amurka zuwa kashi 125

    China

    Asalin hoton, Reuters

    China ta sanar da ƙara harajin kayayyakin Amurka zuwa kashi 125, daga kashi 84 da ta fara sanarwa a ranar Laraba da ta gabata.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasashen ke cigaba da tafka rikicin kasuwanci, inda ta ce yanzu aka fara.

    Beijing ta ce idan Amurka ta ƙara ɗaga harajin, ita ma za ta ƙara ɗaga nata.

    A cewarta, "ƙara harajin da Amurka ta yi mana ya saɓa da dokokin duniya da dokokin kasuwanci da cinikayya na duniya, ya kuma saɓa da tunani da hankali."

    "China ba za ta yi aminta da rainin hankali ba," in ji kakakin ma'aikatar harkokin wajen ƙasar, Lin Jian.

    Tun da farko, ma'aikatar kasuwanci ta China ta bayyana ƙara harajin na Amurka a matsayin "kuskure a kan wani kuskuren," lamarin da ta ce ba za ta lamunta ba.

    A nasa ɓangaren kuma, shugaban Amurka Donald Trump ya zargi China da rashim girmama ƙasarsa.

  19. Jihohi 30 da suke fuskantar barazanar ambaliya a Najeriya

    Ambaliya

    Asalin hoton, Weather monitor

    Gwamnatin Najeriya ta yi gargaɗin cewa za a samu mamakon ruwan sama a jihohi 30 da babban birnin tarayya A buja, wanda ambaliya za ta iya biyo bayansa.

    Jihohin da za su fi fuskantar barazana su ne: Abia da Adamawa da Akwa Ibom da Anambra da Bauchi da Bayelsa da Benue da Borno da Kuros Riba da Delta da Ebonyi da Edo da Gombe da Imo da Jigawa da Kebbi da Kogi da Kwara da Legas da Nasarawa da Neja da Ogun da Ondo da Osun da Oyo da Rivers da Sokoto da Taraba da Yobe da Zamfara da Abuja, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

    Ministan albarkatun ruwa da tsaftace muhalli, Joseph Utsev ya bayyana a ranar Alhamis cewa za a fara ne da fuskantar mamakon ruwan sama a jihohin.

    Ministan ya ce mamakon ruwan ne zai yi yawan gaske da zai jawo ambaliya a jihohin na Najeriya.

    Ya bayyana cewa garuruwa 1,249 a ƙananan hukumomin 176 a jihohi 30 da babban birnin tarayya Abuja ne suke cikin barazanar.

  20. Yau tsigaggen shugaban Koriya ta Kudu zai fice daga gidan gwamnati

    Koriya ta Kudu

    Asalin hoton, Getty Images

    Ana sa ran cikin ƴan sa'o'i masu zuwa ne tsohon shugaban Koriya ta Kudu Yoon Suk Yeol zai fice daga harabar fadar shugaban ƙasa tare da komawa gidansa na ƙashin kansa da zama bayan tsige shi daga muƙaminsa.

    A makon da ya gabata ne, Kotun Ƙolin ƙasar ta tabbatar da tsigewar da aka yi wa Mista Yoon saboda matakin da ya ɗauka na sanya dokar soji a Disamba.

    Tsohon shugaban ƙasar da mai ɗakinsa za su koma zama a wani gida da ke kudancin Seoul.

    Sai dai kafofin yaɗa labaran Koriya ta Kudu sun ruwaito cewa ma'auratan suna duba yiwuwar yin nesa daga tsakiyar birnin kasancewar tsaron da aka ba su da kuma dabbobinsu 11 da suke kiwo na iya damun maƙwabtansu.