Taliban ta zartar da hukuncin kisa kan wasu mutum uku

Asalin hoton, Reuters
Hukummin Taliban a Afghanistan sun zartar da hukuncin kisa a bainar jama'a kan wasu mutum uku a sassan ƙasar.
An harbe wasu maza biyu a lardin Badghis, yayin da aka kashe na ukun a garin zaranj na lardin Nimroz.
Cikin wata sanarwa da Taliban ɗin ta fitar ta ce an samu duka mutanen uku da laifin kisan kai sannan aka yanke musu hukuncin kisa.
Shaidu sun ce rahotonni sun tabbatar da cewa mutanen da aka kashe a Badghis an kashe su ne a gaban dandazon jama'a.
A watan Nuwamban da ya gabata ne aka aiwatar da hukuncin kisa na ƙarshe da aka aiwatar a Afghanistan.


