Sai mun fatattaki ƴan Houthi za mu tsagaita wuta a Yemen - Netanyahu

Asalin hoton, EPA
Isra'ila ta yi gargaɗin cewa yanzu ta fara ɗaukar mataki kan ƴan Houthi a Yemen, waɗanda ke kai hare-hare kan Isra'ila da kuma jiragen ruwan dakon kaya a tekun Bahar Maliya.
Gargaɗin ya fito ne daga Firaminista Benjamin Netanyahu, bayan da Isra'ila ta ƙaddamar da wasu hare-hare ta sama kan wasu wurare a ƙasar Yemen, wanda rahotanni suka sun kashe aƙalla mutum shida.
Netanyahu ya ce, "mun ƙuduri aniyar kawar da wannan ɓangaren ta'addancin na ƙasar Iran. Za mu dage har sai mun cimma nasarar kammala aikin."
A nasa ɓangaren, da yake bayyana yadda ya sha tsallake rijiya da baya, Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce tazarar mitoci kaɗan ne tsakaninsa da harin da aka kai a babban filin jirgin saman Sanaa, babban birnin ƙasar.
