Abin da ya faru lokacin Tsunami shekaru 20 da suka gabata

Jirgin mu - Ramanujam - a bakin ruwan Blair
Bayanan hoto, Yayin da muke fita daga wurin tsayawar jirgi, sai kawai jirgin ya yi ta juyawa inda nan da nan ya sake komawa inda muka fara hawa kafin ya faɗa cikin ruwa.
    • Marubuci, Geeta Pandey
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Delhi
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 7

Lokacin da girgizar ƙasar ta afku da misalin karfe 6:30, ina cikin jirgin ruwa, inda na doshi Havelock - wani tsibiri da ke yankunan Andaman da Nicobar na Indiya.

An fi sanin tsibirin da ruwansa mai launin shuɗi, kuma ba da daɗewa ba mujallar Times Magazine ta ayyana tsibirin a matsayin ''mafi kyawu''.

Babbar ƙawata da 'yan uwanta na rayuwa a tsibirin Blair, babban birnin yankin archipelago, sama da shekara goma da rabi da suka wuce, sai dai wannan ce ziyarar farko da na taba kai wa tsibirin, inda na isa ranar jajiberin Kirsimeti.

Mun tsara shafe kwanaki uku a Havelock, inda da safe muka tattara kayan makulashe da sauran abubuwan ci, muka tara yara cikin murna sannan muka nufi bakin teku domin shiga jirgin ruwa.

Ganin cewa ka da na rasa komai, ya sa na yi sauri wajen hawa gaban jirgin, inda na yi ta duba ko'ina kafin ibtila'in ya afku.

Yayin da muke fita daga mafaka, sai kawai jirgin ya yi ta juyawa inda nan da nan ya sake komawa inda muka fara hawa kafin ya fada cikin ruwa.

Gomman mutane da ke tsaye kusa da ni sun yi ta kallo baki a bude.

Cikin ikon Allah, aka samu nasarar shawo kan jirgin a lokacin ba tare da wani ya jikkata ba.

An tsara tashin jirgin ruwa a lokacin cikin sa'a ɗaya da rabi, sai dai masu tafiyar ba su samu isa ba a lokacin.

Wannan wani yanki ne a wani tsibiri a Indiya da tsunami ta lalata wanda aka dauka ranar 28 ga watan Febrairun 2005.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Gidaje da dama ne guguwar ta tsunami ta lalata
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wani ma'aikacin jirgin ruwan ya faɗa min cewa girgizar ƙasa aka yi. A lokacin ban sani ba, sai dai girgizar ƙasar mai maki 9.1 ta kasance ta uku mafi girma da aka taɓa samu a duniya - kuma ita ce mafi girma da ta lalata abubuwa a yankin Asiya.

Girgizar ƙasar ta afku daga tekun Indiya a arewacin Sumatra, inda ta janyo guguwa mai karfin gaske da ta janyo mutuwar aƙalla mutum 228,000 a faɗin gomman ƙasashe da lalata abubuwa a Indonesiya da Sri Lanka da Indiya da Maldives da kuma Thailand.

An samu gagarumar ɓarna a tsibirin Andaman da Nicobar, waɗanda ke nisan kilomita 100 daga arewacin wurin da lamarin ya afku, inda ruwa mai karfin gaske da ya kai mita 15 ya afka cikin gonaki, mintuna 15 bayan haka.

Hukumomi sun ce alkaluman mutanen da suka mutu sun kai 1,310 - sai dai sama da mutum 5,600 ne suka ɓace waɗanda ake tunanin sun mutu. An kuma yi imanin cewa ƴan tsibirin kusan 7,000 ne suka mutu.

Yayin da muke cikin jirgin, ba mu san irin ɓarnar da ke faruwa a kusa da mu ba.

Wayoyin mu ba sa aiki a cikin ruwa, kuma bayanai kaɗan muke samu daga ma'aikatan jirgin. Mun ji batun ɓarna da aka samu a Sri Lanka da Thailand da kuma Maldives - da kuma yankin Nagapattinam da ke kudancin tekun Indiya.

Wasu ƴan Indiya da Tsunami ta daidaita bayan neman 'yan uwansu da suka ɓata a Cuddalore.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wasu ƴan Indiya da Tsunami ta ɗaiɗaita bayan neman 'yan uwansu da suka ɓata a Cuddalore, ranar 27 ga Disamban 2024

Sai dai babu bayanai kan halin da tsibirin Andaman da Nicobar suke - bayan da mahaukaciyar guguwar ta tsunami ta ɗaiɗaita ɗaruruwan tsibirai a yankin Bengal, mai nisan kilomita 1,500 daga gabashin Indiya.

Tsibirai 38 ne kaɗai aka samu mutane da suke rayuwa a ciki. Mutum kusan 400,000 ne suka zauna a cikinsu, ciki har da kungiyoyin masu farauta guda shida, waɗanda suka yi rayuwa a wajen sama da dubban shekaru.

Hanya kaɗai da za ta kai mutum zuwa tsibiran shi ne jiragen ruwa, sai dai kamar yadda muka ji daga baya, an kiyasta cewa hanyoyi da ke ta cikin ruwa kusan kashi 94 ne aka lalata.

Wannan dalili ne ya sa, ranar 26 ga watan Disamban 2004, ba mu samu damar kai wa yankin Havelock ba. An lalata hanyoyi da ke can na karkashin ruwa.

Don haka ne jirgin mu ya juya tare da komawa inda muka fito. Zuwa wani lokaci, an faɗa mana cewa ba za mu samu damar tsayawa a Blair ba saboda dalilai na tsaro kuma za mu shafe dare a cikin ruwa.

Wannan ya sa fasinjoji - waɗanda yawanci masu yawon buɗe ido shiga zullumi.

Bayan sa'o'i da dama muna shawagi a cikin ruwa, mun koma tsibirin Blair.

Saboda an rufe tashar Phoenix Bay saboda lalacewa da aka samu a safiyar, inda aka kai mu Chattam, wani wurin mafaka a tsibirin Blair. Hanyar da muka bi na cike da ramuka.

Mun yi ta ganin alamomin ɓarna da tsunami ta haddasa a ko'ina yayin da muka nufi hanyar gida - gine-gine sun koma ɓaraguzai, ƙananan jirage sun jujjuya suna kwance kan tituna, hanyoyi kuma sun tsassage.

Dubban mutane sun rasa muhallansu lokacin da mahaukaciyar guguwa ta afka musu.

Na haɗu da wata ƴar shekara tara da ta ɗimauce wadda gidansu ya cika da ruwa, ta faɗa min cewa saura kaɗan ta nutse. Wata mata ta faɗa min cewa ta rasa dukkan abin da ta mallaka a ƙasa da kiftawar ido.

A tsibirin Blair, gine-gine sun koma baraguzai, kananan jirage sun jujjuya suna kwance kan tituna.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A tsibirin Blair, gine-gine sun koma ɓaraguzai, kananan jirage sun jujjuya suna kwance kan tituna, hanyoyi kuma sun tsatstsage

A cikin makonni uku a lokacin, na yi rahotanni kan ibtila'in da kuma tasirinsa kan al'umma.

Wannan ne karon farko da tsunami ta ɗaiɗaita tsibiran Andaman da Nicobar, kuma lamarin ya fi karfin mutane.

Ruwa mai karfi ya janyo lalacewar filaye da dama. Samun hanyar kai agaji tsibiran ya janyo wahala ganin cewa hanyoyin cikin ruwa da ake bi sun lalace.

Hukumomi sun kaddamar da gagarumin shirin agaji da kuma aikin ceto. An aika sojojin ƙasa da na ruwa da kuma na sama zuwa tsibiran, amma sun shafe tsawon kwanaki kafin kai wa yankin.

A kullu yaumin, sojojin ruwa da jami'an tsaron bakin teku na ɗauko mutane da dama waɗanda tsunami ta ɗaiɗaita daga wasu tsibirai zuwa tsibirin Blair, inda aka mayar da makarantu da kuma gine-ginen gwamnati zuwa wuraren tsugunar da mutane na wucin-gadi.

Sun bayar da labaran yadda ibtila'in ya afka wa yankunansu. Da yawa sun faɗa min cewa sun tsira ba tare da komai ba, illa tufafin da ke jikinsu.

Wata mata daga tsibirin Car Nicobar, ta faɗa min cewa lokacin da girgizar ƙasar ta afku, ƙasa ta fara fitar da ruwa yayin da guguwa mai karfi ta fara kaɗawa daga koguna.

Ita tare da ɗaruruwan mutane daga kauyensu sun jira masu aikin ceto ba tare da cin abinci ba ko kuma na tsawon sa'a 48. Ta ce ''an yi sa'a'' cewa ita da jaririyarta sun tsira.

Tsibirin Blair ya ci gaba da fuskantar bala'o'i, wasu sun kai karfin da ake hasashen cewa wata tsunami ce, abin da ya sanya fargaba a zukatan mutane har ta kai suna guduwa zuwa wurare masu kariya.

Kauyawa daga Indiya a wani sansani da aka tsugunar da su.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dubban mutane ne ibtila'in ya ɗaiɗaita

Kwanaki kaɗan bayan nan, sojojin Indiya sun ɗauki 'yan jarida zuwa tsibirin Car Nicobar, mai cike da bishiyoyi masu kyau da kuma ya kasance wurin da sojojin saman Indiya da dama ke zaune.

Guguwar ta tsunami ta ɗaiɗaita ɗaukacin tsibirin. Karfin ruwa ya kai mita 12 a nan. Mutane kusan 100 ne suka mutu a nan. Sama da rabinsu sun kasance sojojin sama da kuma iyalansu.

Mun ziyarci kauyukan Malacca da Kaakan a tsibirin, waɗanda su ma suka fuskanci ibtila'in, abin da ya janyo mazauna wurin suka koma zaman mafaka a tantuna a gefen tituna. Cikinsu akwai iyalai da suka rasa komai.

Wasu ma'aurata da al'amarin ya shafa, sun faɗa min cewa sun samu nasarar ceto jaririyarsu mai watanni biyar, sai dai ruwa ya tafi da sauran 'ya'yansu, masu shekara bakwai da kuma 12.

Gidaje a tsibirin mai ɗauke da itatuwan kwakwan manja, sun koma ɓaraguzai.

Cikin kayayyakin mutane da ibtila'in ya lalata sun haɗu da tufafi da takardu da takalman yara da kuma abin jin waka.

Abu guda da ya rage - wanda ya ba da mamaki - shi ne mutum-mutumi na Mahatma Gandhi, a wani shatale-tale.

Sojojin saman Indiya ke kokarin nemo wasu takardu a kauyen Malacca da ke tsibirin Car Nicobar, ranar 7 ga watan Janairun 2005.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sojojin saman Indiya da ke tsibirin Car Nicobar sun kaɗu da ibtila'in

Wani babban jami'in soja ya faɗa mana cewa tawagarsa ta gano gawawwaki bakwai a ranar, kuma mun ga yadda aka yi jana'izarsu daga nesa.

A sansanin sojin, mun ga yadda masu aikin ceto suka fito da gawar wata mata daga cikin ɓaraguzai.

Wani jami'in soja ya ce baya ga gawawwaki da aka gano a tsibirin Car Nicobar, akwai wasu da dama da ruwa ya tafi da su.

Bayan shafe waɗannan shekaru, a wasu lokutan ina tuna ranar da na shiga jirgin ruwa zuwa yankin Havelock.

Har yau ban san me zai faru ba da a ce igiyar ruwa ya daki jirgin mu lokacin da nake jiran ya tashi.

A ranar Boxing Day, shekara ta 2004, na samu kiran waya. Dubban mutane da suka mutu ba su taki sa'a ba.

Kauyawan Indiya ke duba jerin sunayen mutanen da suka bata a tsibirin Blair, ranar 31 ga watan Disamban 2004.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ba a gano dubban mutanen da suka ɓata lokacin Tsunami ba har kawo yanzu