Man United da City na gogayya kan Olmo, Liverpool na fatan tsawaita zaman Van Dijk

Dani Olmo

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Wakilin Dani Olmo ya isa birnin Manchester a daidai lokacin da ƙungiyoyin Premier da suka haɗa da Manchester United da Manchester City, ke neman cin gajiyar fafutukar da Barcelona ke yi na yin rijistar ɗan wasan tsakiyan na Sifaniyan, mai shekara 26, kafin wa'adin watan Janairu. (Mail)

Liverpool na da ƙwarin gwiwar cewa ɗan wasan baya na Netherlands Virgil van Dijk, mai shekara 33, wanda kwantiraginsa zai ƙare a bazara, zai rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniya ta shekara biyu da ƙungiyar. (Team talk)

Real Madrid ba ta da sha'awar ɗaukar Van Dijk a bazara, duk da rahotannin da ke alaƙanta ta da ɗan wasan na ƙasar Holland.(Marca)

Ɗan wasan baya na Bayern Munich Alphonso Davies, mai shekara 24, a shirye yake ya koma gasar Premier a bazara, inda Manchester United da Liverpool ke cikin ƙungiyoyin da ke sha'awar ɗan wasan na ƙasar Canada. (TBR Football)

Manchester United ta sanya farashin kusan fam miliyan 50 kan dan wasan gaban Ingila Marcus Rashford mai shekaru 27. (Caughtoffside)

Arsenal na sanya ido kan ɗan wasan Wolves da Brazil Matheus Cunha, mai shekara 25, wanda zai iya tafiya idan kulob ɗin na yankin Midlands ya koma gasar Championship. (Athletic)

Dan wasan Brazil Antony ya samu tayin barin Manchester United a watan Janairu amma wakilinsa ya ce ƙungiyar ba ta son ɗan wasan mai shekara 24 ya tafi. (Give me sport)

Babu wata alamar da ke nuna cewa ɗan wasan Paris St-Germain da Faransa Randal Kolo Muani mai shekara 26, wanda ke jan hankalin Manchester United da Liverpool, zai koma gasar Premier a watan Janairu. (Football Transfers)

Mataimakin kocin Liverpool John Heitinga ne ke kan gaba a jerin sunayen waɗanda za su iya maye gurbin Carlos Corberan a matsayin kocin West Brom. (Football Insider)

Sporting Lisbon na shirin maye gurbin Joao Pereira, wanda aka kora ranar Kirsimeti, da kocin Vitoria Guimaraes Rui Borges. (Sky Sports)

Fiorentina na sha'awar ɗaukar ɗan wasan bayan Parma da Faransa Woyo Coulibaly, mai shekara 25. (Matteo Moretto)