Labaran wasannin BBC Hausa kai-tsaye na 12-18/07/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Asabar 12 zuwa18 ga watan Yulin 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu da Muhammad Annur Muhammad

  1. Liverpool ta daina amfani da riga mai lamba 20 don tunawa da Jota

    Jota

    Asalin hoton, PA Media

    Liverpool ta ajiye riga mai lamba 20, domin tunawa da Diego Jota, wanda ya yi haɗarin mota ya mutu a Sifaniya, tare da ɗan uwansa, Andre Silva.

    An cimma wannan matsaya ce, bayan da aka tuntuɓi matar Jota, Rute Cardoso da iayalansa, kenan riga mai lamba 20 ta zama mallakin Jota har abada a Liverpool.

    Kenan ba a sake saka riga mai lamba 20 a Liverpool tun daga matasa da babbar ƙungiya da ta mata.

    Jota ya koma Liverpool daga Wolverhampton a 2020, ya kuma ci wa ƙungiyar Anfield ƙwallo 65 a wasa 182 da ya buga mata.

    Ya taka rawar da ta kai Liverpool ta ɗauki FA Cup da League Cup a 2022 - da na 2024 - da kuma Premier League a kakar da ta wuce.

  2. Jama'a barkanmu da shiga shirin sharhi da bayanan labarin wasannin kai tsaye daga sassan duniya tun daga ranar Asabar 12 zuwa 18 ga watan Yulin 2025.

    Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper Tudun Wada zan kasance da ku.

    Za ku iya tafka muhawara a BBC Hausa Facebook da kuma x.