Labaran wasannin BBC Hausa kai-tsaye na 12-18/07/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Asabar 12 zuwa18 ga watan Yulin 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu da Muhammad Annur Muhammad

  1. An girmama Jota da Silva a wasan sada zumunta na Liverpool

    'Yanwasan Liverpool

    Asalin hoton, Getty Images

    An girmama Diogo Jota da ƙaninsa Andre Silva a wasan farko na sada zumunta na Liverpool tun bayan rasuwar 'yanwasan biyu.

    Tun kafin a take leda a wasan na shirin tunkarar kaka mai kamawa a Preston North End, an riƙa rera waƙar Elvis Presley ta 'Can't Help Falling in Love' wadda waƙa ce mai ratsa zuciya, da kuma waƙar taken Liverpool ta - You'll Never Walk Alone'.

    Ɓanagren magoya bayan Liverpool ya cika da tutoci da kyallaye na tunawa da tsohon ɗanwasan na Porto da Wolves, inda suka riƙa rera waƙar Jota, yayin da su kuma 'yanwasan suka yi shiru na minti ɗaya domin tunawa da shi.

    Liverpool ta yi nasara a wasan da ci 3-1, inda Conor Bradley ya fara ɗaga raga, sai Darwin Nunez ya ci ta biyu tare yin irin murnar da Jota ke yi idan ya ci ƙwallo har sau biyu, sai kuma Cody Gakpo, ya zura ta uku, tare da murna da yin alamu na lamba 20 - wato lambar Jota a ƙungiyar

  2. Tsohon ɗanbayan Man Utd Tuanzebe ya kai ƙarar ƙungiyar

    Axel Tuanzebe

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon ɗan wasan baya na Manchester United Axel Tuanzebe ya kai ƙarar ƙungiyar bisa zargin ba shi shawarar da ba ta dace ba a kan lafiyarsa.

    A makon da ya wuce ne ɗanwasan mai shekara 27, wanda ya koma Burnley daga Ipswich a bazaran nan, ya shigar da ƙara ne a kan United.

    Ƙarar da danganci wani lokaci ne daga watan Yuli na shekara ta 2022, wanda ya danganci wani rauni da ba a sani ba - wanda kuma ake ganin zai iya cin har sama da fam miliyan 1.

    A shekararsa ta ƙarshe a United Tuanzebe, ya tafi jinya tsawon kwana 195, kafin ƙungiyar ta bayar da aronsa ga Stoke a watan Janairun 2023, inda ya yi wasa biyar kawai.

    Ya bar Old Trafford a 2023, inda ya koma Ipswich a watan Satumba na wannan shekara inda ya yi wasa 45 har ma ya taimaka wa ƙungioyar ta tsallaka zuwa gasar Premier a 2024.

    A lokacin da BBC ta yi ƙoƙarin jin ta bakin lauyan ɗanwasan da kuma Manchester United dukkanninsu sun ƙi cewa komai a kan lamarin.

  3. Forest na barazanar kai ƙarar Tottenham a kan Gibbs-White

    Morgan Gibbs-White

    Asalin hoton, Getty Images

    Nottingham Forest na duba yuwuwar ɗaukar matakin shari'a a kan Tottenham saboda sha'awar da Spurs ɗin ta nuna a kan ɗanwasan tsakiya na Forst ɗin Morgan Gibbs-White, ba bisa ƙa'ida ba.

    A ƙa'ida ƙungiya ba za ta yi wa duk wani ɗanwasa da yake da kwantiragi da wata ƙungiya ba, har sai ta samu izinin yin hakan daga ƙungiyar ɗanwasan.

    Ana ganin Forest na dubawa ta ga ko akwai wata ƙa'ida ta sirrin yarjejeniyar da ke tsakani a kan siɗirar damar sayar da ɗanwasan ta fam miliyan 60 a kwantiraginsa da aka saɓa.

    BBC ta fahimci cewa Forest ta kafe lalle cewa Tottenham ba ta nemi izininta ba ta je ta yi magana da Gibbs-White, saboda haka za ta ɗauki duk matakin da za ta iya na ganin ta hana tafiyarsa.

    Tottenham dai ta san da duka wannan halin da ake ciki amma har yanzu tana da ƙwarin gwiwa cewa za a yi cinikin.

    A ranar Alhamis BBC ta bayar da rahoton cewa ɗanwasan zai je a gwada lafiyarsa a Tottenhma kafin a kammala cinikinsa a kan fam miliyan 60.

    To amma kuma kwatsam washegari sai wasu majiyoyi suka sheda wa BBC cewa Nottingham Forest na tunanin kai ƙarar Tottenham saboda sha'awar da ta nuna a kan ɗanwasan na tawagar Ingila.

    Yanzu dai makomar Morgan Gibbs-White a Nottingham Forest na nan zaman ƙila-wa-ƙala.

    Kasancewar akwai damar ɗanwasan ya bar ƙungiyar idan an saye shi fam miliyan 60 a yarjejeniyarsa, kuma yanzu an saye shi hakan amma Forest na neman yin ƙafar-ungulu - wasu na ganin Forest ɗin ce za ta iya kwana a ciki idan ɗanwasan ya kai ƙara.

    Kuma ana ganin hakan zai iya sa nan gaba 'yanwasa su yi shayin zuwa ƙungiyar saboda saɓa wannan yarjejeniyar.

  4. Kun san kuɗin da aka bai wa ƙungiyoyin da suka shiga gasar Club World Cup?

    KLambin gasar Club World Cup

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗaya daga cikin manyan batutuwan da aka riƙa yi a tsawon gasar cin kofin duniya ta ƙungiyoyi - wato Clup World Cup, shi ne kuɗin da za a bayar ga waɗanda suka yi nasara a gasar.

    An ware dala miliyan 1000 kwatankwacin fam miliyan 726 da za a bai wa ƙungiyoyi 32 da suka shiga sabuwar gasar, inda za a raba dala miliyan 525 a tsakanin dukkanin ƙungiyoyin da suka fafata, sannan za a bayar da dala miliyan 475 da za a bayar daidai da ƙoƙarin da ƙungiya ta yi.

    An bai wa ƙungiyoyin Turai tsakanin dala miliyan 12.81 da miliyan 38.19 saboda zuwa gasar kawai, yayin ƙungiyoyin da suka je daga Latin Amurka aka ba su dala miliyan 15.21, su kuwa ƙungiyoyin nahiyar Amurka ta Arewa da ta tsakiya da Asia da kuma Afirka - miliyan 9.55, su kuwa ƙungiyoyin Oceania aka ba su dala miliyan 3.58.

    Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya Fifa ba ta tabbatar da ainahin kuɗin da ta bai wa ɗaiɗaikun ƙungiyoyin Turai ba na shiga gasar, illa an yi amfanbi da ƙididdigar shafin intanet da ke bayar da bayanan kuɗaɗe na wasan ƙwallon ƙafa- The Swiss Ramble aka fitar da alƙaluman.

    Ƙungiyar gasar Premier ta Ingila Chelsea ce ta yi nasara a wasan ƙarshe na gasar inda ta doke PSG da ci 3-0.

    Ladan kuɗin da ƙungiyoyin suka samu ya taimaka musu sosai musamman ma Chelsea da Manchester City.

    Chelsea ta kashe fam miliyan 198 wajen sayen 'yanwasa zuwa yanzu a wannan bazarar, wajen sayen irin su Joao Pedro da Liam Delap, kuma ta mayar da fam miliyan 84 daga cikin wannan kuɗin a sakamakon kuɗin da aka ba ta a gasar.

    Haka ita ma Manchester City duk da ƙungiyar Al-Hilal ta Saudiyya ta yi waje da ita daga gasar tun da farko-farko, to amma ta samu kuɗin da ta mayar da kusan kashi 35 cikin ɗari na kuɗin da ta kashe a bazara - wato ta mayar da fam miliyan 31 da ta kashe wajen sayen Rayan Ait-Nouri daga Wolves.

  5. Luis Enrique zai iya fuskantar hukunci kan marin Pedro

    Luis Enrique da 'yanwasan Chelsea da PSg ana hatsaniya

    Asalin hoton, Getty Images

    Bisa ga dukkan alamu kociyan PSG Luis Enrique zai iya fuskantar hukunci saboda 'yar hatsaniyar da ta barke tsakanin 'yan wasa bayan da Chelsea ta casa kungiyarsa ta PSG da ci 3-0 a wasan karshe na gasar cin kofin duniya na kungiyoyi - Club World Cup a jiya Lahadi.

    Bayan tashi daga wasan da aka yi a New Jersey, an samu hatsaniya a tsakanin 'yan wasan inda aka ga kociyan na PSG dan Sifaniya ya mari Joao Pedro, wanda ya ci kwallo ta uku a wasan, a minti na 43, bayan da Palmer ya zura biyu a minti na 20 da kuma 30.

    To amma kuma tsohon kociyan na Barcelona ya ce yana kokarin raba 'yan wasan ne da suke hatsaniya kawai.

    Ya ce :"Ba ni da wata matsala kan bayyana yadda na ji a karshen wasan a yadda ya kasance. Abin takaici ne ga dukkaninmu, saboda haka abu ne mawuyaci a iya kauce wa irin wannan abu."

    Ya kara da cewa, ''kowa yana da hanu. Ba abu ne da ya dace ba da kuma yadda sakamakon wasan ya haifar da haka.

    "Na ga yadda Maresca, yake ture sauran 'yanwasan to kuma dole ne mu raba su, na san abin da ya sa ransu ya baci,'' in ji kociyan na PSG.

    Ya ce: ''Kowa yana son ya yi nasara a wasa, kuma a karshe ransu ya baci saboda yadda ya kasance.''

    Bayan 'yanwasan PSg sun janye kociyan nasu, an ga Pedro ya hakura shi ma.

    An ji danwasan na Brazil na cewa 'yan kungiyar ta Faransa sun harzuka ne. Ba na bukatar in yi wata magana a kansu.''

  6. Arsenal na dab da kammala cinikin Gyokeres

    Viktor Gyokeres

    Asalin hoton, Getty Images

    Ana sa ran nan da 'yan wasu sa'o'i Arsenal za ta kammala cinikin Viktor Gyokeres na Sporting a kan kudi yuro miliyan 73.5 kwatankwacin fam miliyan 63.5m.

    Wasu majiyoyi sun tabbatar wa da BBC cewa cinikin danwasan gaban na Sweden ya kusa kammala in banda wasu 'yan bayanai da suka rage a cimma matsaya a kansu.

    Dukkanin bangarorin da ke cikin maganar na so a kammala komai ta yadda Gyokeres zai tafi da Arsenal wasannin shirin tunkarar kaka mai kamawa a Asia a karshen makon da muke ciki.

    Da farko dai Arsdenal ta taya danwasan ne a kan yuro miliyan 70 amma daga baya ta kara da 'yan wasu tsarabe-tsarabe.

    Tuni danwasan mai shekara 27 ya amince da yarjejeniya zama a Gunners din ta tsawon shekara biyar.

    A farkon watan nan BBC ta ruwaito cewa Arsenal ta karkata ga Gyokeres ne bayan da ta kasa cimma matsaya a cinikin Benjamin Sesko na RB Leipzig.

  7. Cristhian Mosquera ya cimma matsaya da Arsenal

    Cristhian Mosquera

    Asalin hoton, Getty Images

    Babban ɗanbayan Valencia Cristhian Mosquera ya cimma yarjejeniya da Arsenal, a ƙoƙarin da ƙungiyar ke yi na sayenshi.

    Tun a baya daman BBC ta ruwaito cewa Arsenal na tattaunawa da ɗanwasan mai shekara 21 - yanzu kuma sun yi nasarar ƙara cimma wata matsaya tsakaninsu.

    Gunners na ƙoƙarin ganin sun ƙara wani matashin ɗanbaya a tawagar domin gogayya da William Saliba da Gabriel Magalhaes.

    Mosquera wanda ɗan tawagar Sifaniya ne ta 'yan ƙasa da shekara 21, wanda kuma ɗan Colombia ne, zai iya wasa a tsakiyar baya da kuma gefen dama kuma zai cike gurbin da Takehiro Tomiyasu, ya bari.

    Ya yi wa Valencia wasa 90, kuma a kakar da ta wuce kusan a kodayaushe yana wasa inda ya buga wasa 37 daga cikin 38 da ƙungiyar ta yi a La Liga.

  8. Arsenal ta kusan kammala ɗaukar Madueke daga Chelsea

    Madueke

    Asalin hoton, Getty Images

    Noni Madueke ya kusan zama ɗan wasan Arsenal, zai zama na huɗu da Mikel Arteta zai ɗauka kan fara kakar bana, kuma kan £50million.

    Ana sa ran Madueke ɗan wasan tawagar Ingila, zai yi takara a gurbin da Bukayo Saka ko kuma Gabriel Martinelli ke bugawa a Gunners..

    Madueke, mai shekara 23, wanda yake tare da Chelsea a Amurka a Club World Cup, bai yi atisaye ba ranar Juma'a, domin zuwa a auna koshin lafiyarsa a Emirates.

    Ranar Lahadi Chelsea za ta buga wasan karshe a Club World Cup, inda za ta fuskanci Paris St Germain mai riƙe da Champions League da za su kece raini a birnin New York.

    Arsenal za ta kammala ɗaukar Madueke ne wanda ya koma Stamford Bridge daga PSV Eindhoven a 2023, bayan da tuni ta sayi Martin Zubimendi da mai tsaron raga, Kepa Arrizabalaga da kuma Christian Norgaard.

    Madueke ya ci wa Chelsea ƙwallo 11 a dukkan fafatawa a kakar da ta wuce, wanda hakan ya sa kociyan tawagar Ingila na riƙon kwarya, Lee Carsley ya gayyace shi har da Thomas Tuchel da shima ya mika masa goron gayyata.

    Har yanzu Arsenal tana kasuwa, wadda ke zawarcin gurbin mai cin ƙwallaye, an ce tana ta kokarin sayen ɗan wasan Sporting Lisbon, Viktor Gyokeres.

  9. Mun samu nasarar gudanar da Club World Cup - Infantino

    Infantino

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban hukumar ƙwallon kafa ta duniya, Gianni Infantino ya ce sun yi nasarar gudanar da Fifa Club World Cup, kuma sun ɗauki darasa kan yadda za su shirya gasar kofin duniya a Amurka a 2026.

    Infantino ya ce Fifa, wadda ta tsara wasannin a Amurka tun daga watan jiya tsakanin ƙungiya 32 ta samu ƙudin da ya kusan kai £1.5billion.

    Za a rufe labulen gasar ranar Lahadi da karawar karshe tsakanin mai rike da Champions League, Paris St Germain da Chelsea mai buga Premier League.

    Ana kuma sa ran shugaban Amurka, Donald Trump zai halarcin karawar karshe.

  10. Wimbledon Open: Za a buga wasan karshe tsakanin Sinner da Alcaraz

    Wimbledon Open final 2025

    Asalin hoton, Getty Images

    Carlos Alcaraz da Jannik Sinner za su buga wasan karshe a Wimbledon Open ranar Lahadi.

    Ƴan wasan biyu sun lashe Grand Slam kofi bakwai a tsakaninsu daga Grand Slam takwas baya tun daga 2024.

    Wannan karawar ta gabace da take bin sawun kamar yadda aka yi a baya tsakanin fitattun ƴan wasa uku wato Roger Federer da Rafael Nadal da kuma Novak Djokovic.

    Alcaraz ne ke rike da kofin karo biyu a jere, wanda ake sa ran zai iya lashe na uku, amma ya kwan da sanin zai fuskanci gagarumin kalubale.

    Alcaraz ɗan kasar Sifaniya ya yi nasara a kan Sinner karo takwas daga fafatawa 12 a tsakaninsu, har da nasara a haɗuwa biyar baya.

    Wasan bayan nan da suka fuskanci juna shi ne a French Open gasar kan taɓo, inda Alcaraz ya lashe kofin.

    Alcaraz mai shekara 22 mai manyan kofi biyar ya yi wasa 24 ba tare da rashin nasara ba, kuma rabon da aka doke shi a wasannin All England Club tun bayan 2022.

    Shi kuwa Sinner mai babban kofi uku, ya kai wasan karshe a Wimbledon Open a karon farko, kuma ya taɓa doke Alcaraz a Wimbledon Open a zagaye na huɗu a kaka uku baya.

  11. Jackson

    Asalin hoton, Ge

    Chelsea ta ƙayyade farashin fam miliyan 100 kan ɗanwasan Senegal Nicolas Jackson mai shekara 24 wanda yanzu haka AC Milan ke zawarcin sa. (Mail)

    Ɗanwasan Manchester United da Ingila Marcus Rashford mai shekara 27 ya zama wanda a yanzu Barcelona za ta fi bai wa fifiko a ƙoƙarinta na kawo ɗan wasan gaba na gefe bayan kulob ɗin na Sifaniya ya yi rashin nasara a ƙoƙarin ɗaukan ɗanwasan Liverpool Luis Diaz mai shekara 28 da Nico Williams na Athletic Bilbao mai shekara 22. (Sky Sports)

    Juventus ta amince da ƙulla yarjejeniyar euro miliyan 20 da Manchester United kan ɗanwasan Ingila Jadon Sancho wanda yake tattaunawa da ƙungiyar ta Old Trafford game da kuɗin sallama kafin ya yi bankwana. (La Stampa - in Italian)

    Tottenham na ci gaba da zawarcin ɗanwasan Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo Yoane Wissa duk da rashin tuntuɓar Brentford bayan samun labarin yi wa ɗanwasan farashin fam miliyan 50 a farkon wannan bazarar. (Standard)

  12. Iga Swiatek ta lashe Wimbledon Open a karon farko a tarihi

    Swiatek

    Asalin hoton, Getty Images

    Iga Swiatek ta doke ƴar Amurka, Amanda Anisimova da cin 6-0 6-0 ta zama ta farko ƴar kasar Poland da ta lashe Wimbledon Open ranar Asabar kuma cikin minti 57.

    Matashiya Anisimova ta zama ta farko da ta sha kashi a wasan karshe a Wimbledon Open da ci 6-0 6-0 tun bayan da Steffi Graf ta caskara Natasha Zvereva a French Open a 1988.

    Tun a baya can Swiatek ba ta taɓa haura zagayen kwata fainal ba a Wimbledon duk da lashe French Open.

    Wannan shi ne kofin da ta ɗauka tun bayan Roland Garros wata 13, kuma ita ce matashiya da ta ɗauka kofi a gasar kan ciyawa da tabo da tsandauri tun bayan Serena Williams a 2002.

  13. Onana ba zai yi wa Man United wasannin sada zumunta a Amurka ba

    Onana

    Asalin hoton, Getty Images

    Andre Onana ba zai buga wa Manchester United wasannin tunkarar kakar bana ba a Amurka, sakamakon raunin da ya ji a lokacin atisaye.

    Ɗan wasan tawagar Kamaru, mai shekara 29, ba zai buga wa United wasa uku da za ta buga a Amurka ba, wanda zai yi jinya, amma zai bi ta wasannin.

    Kenan Altay Bayindir, mai shekara 27, shi ne zai maye gurbinsa a wasannin sada zumuntar.

    Watakila United ta shiga kasuwa, wajen sayo mai tsaron raga, inda tun kan a karkare kakar da ta wuce ake ta jitar-jitar cewar ƙungiyar Old Trafford za ta sayo sabon gola, domin maye gurbin Onana.

    To sai dai Amorim ya ce ya amince da inganci Onana, kuma shi ne zai ci gaba da tsare ragar United a kakar da za a fara daga watan Agusta,

    Tsohon ɗan wasan Ingila, Tom Heaton, mai shekara 39 ya tsawaita yarjejeniyar kaka ɗaya a ƙungiyar a makon nan..

    United za ta fara wasan sada zumunta da Leeds United ranar 19 ga watan Yuli.

    Daga nan za ta fafata da West Ham ranar 27 ga watan nan da kuma Everton ranar 3 ga watan Agusta daga nan ta kece raini da Fiorentina ranar 9 ga watan Agusta a Old Trafford.

    United za ta fara wasannin gasar Premier League ta bana da Arsenal ranar 17 ga watan Agusta.

  14. Gossip

    Asalin hoton, Getty Images

    Nottingham Forest na duba yiwuwar ƙara wani abu kan tayin da ta yi da zai kai fam miliyan 25 kan ɗanwasan Ingila na ƴan ƙasa da shekara 21 James McAtee sai dai Manchester City ta yi wa mai shekara 22 ɗin farashin kusan fam miliyan 40. (Mail)

    Atalanta na son tayin aƙalla fam miliyan 50 kafin ta duba yiwuwar cefanar da ɗanwasanta ɗan asalin Italiya Giorgio Scalvini wanda Newcastle United da Manchester United ke zawarci. (i paper)

    Aston Villa na dab da kammala ƙulla yarjejeniyar sayen golan Netherlands mai shekara 34 Marco Bizot daga Brest da ke Faransa. (Athletic - subscription required)

  15. Fiorentina ta sanar da ɗaukar Stefano Pioli

    Pioli

    Asalin hoton, Getty Images

    Fiorentina ta ɗauki Stefano Pioli a matakin sabon kociyanta kan yarjejeniyar kaka uku, bayan da ya bar Al-Nassr ta Saudiyya a makon jiya, zai sake horar da ƙungiyar karo na biyu.

    Tun da fari, Fiorentina ta tsawaita ƙwantiragin Raffaele Palladino a watan mayu, sai dai ya ajiye aikin mako uku tsakani, hakan ya sa Pioli ya samu damar komawa Fiorentina bayan raga gari da Al-Nassr.

    Pioli, wanda ya taka leda a Fiorentina daga 1989 zuwa 1995 ya horar da ƙungiyar daga 2017 zuwa 2019.

    Daga nan ya ja ragamar AC Milan, winning da lashe Serie A a 2021-22 daga nan ya koma horar da tamaula a babbar gasar Saudiyya.

    Fiorentina ta kare kakar da ta wuce a mataki na shida a teburin Serie A, kenan za ta buga Europa Conference League a kakar da za a fara nan gaba.

    Ƙungiyoyin Serie A sai canja kociyoyi suke yi tun kan shiga kakar 2005/26, na kwana-kwanan ne ya haɗa da Inter Milan da AC Milan da AS Roma da Atalanta da kuma Lazio.

  16. Vinicius Jr ya cika shekara 25 da haihuwa ya lashe kofi 14 a Real Madrid

    Vinicius

    Asalin hoton, Getty Images

    Vinicius Junior dan wasan tawagar Brazil, an haife shi ranar 12 ga watan Yulin 2000.

    Kawo yanzu yana kaka ta bakwai a Real Madrid tun da ya fara buga mata tamuala a karawa da Atletico Madrid ranar 29 ga watan Satumbar 2018.

    Vinicius ya yi wa Real Madrid wasa 332 da cin ƙwallo 106.

    Ɗan wasan tawagar Brazil ya lashe kofi 14 a Real Madrid da ya haɗa da Champions League biyu da Uefa Super Cup biyu da La Liga uku da Copa del Rey da Spanish Super Cup uku.

  17. An dakatar da tattaunawa kan sabunta kwantiragin babbar gasar tamaula ta Indiya

    Hukumar ƙwallon kafar India ta dakatar da babbar gasar kasar kamar yadda ta sanar ranar Asabar da cewar an samu tsaiko kan sabuta yarjejeniya da kamfanin da yake tallata gasar mai suna Football Sports Development Limited (FSDL).

    Tun a 2010 suka kulla yarjejeniya, yanzu kuma wata babbar kotu a Indiya ta ce da hukumar kwallon kafar kasar da kada ta saka hannu kan yaejejeniya har sai an cike ka'ida.

    Haka kuma kotun na tsara sabbin dokokin da za a ke gudanar da hukumar ƙwallon kafar kasar.

    Tun farko a cikin watan Disamba ƙwantiragin da aka ƙulla tsakanin hukumar ƙwallon kafar Indiya da FSDL zai cika.

    Za a fara babbar gasar tamaula ta Indiya, ISL a cikin watan Satumba da ƙungiya 13.

  18. Gossip

    Asalin hoton, Getty Images

    Arsenal na ci gaba da zawarcin ɗanwasan Real Madrid Rodrygo mai shekara 24 duk da cewa suna dab da cimma yarjejeniyar ɗaukan ɗanwasan Chelsea Noni Madueke mai shekara 23. (GiveMeSport)

    Ɗanwasan Colombia Daniel Munoz mai shekara 29 na fatan yin bankwana da Crystal Palace a wannan bazarar duk da cewa a watan Afrilu ya sabunta kwantiraginsa da ƙungiyar. (Mirror)

    Fenerbahce da ke Turkiyya ta kusa ƙulla yarjejeniyar sayen ɗanwasan Sifaniya Marco Asensio mai shekara 29 daga Paris St-Germain. (Football Italia)

  19. Van Gaal zai koma horar da tamaula bayan jinyar ciwon daji

    Van Gaal

    Asalin hoton, Getty Images

    Fitatcen koci, Louis van Gaal ya ce ya sami lafiya, bayan jinyar ciwon daji, kuma a shirye yake ya koma horar da tamaula.

    Mai shekara 73 ya sanar a shekara uku da ta wuce cewar yana fama da ciwon daji.

    Van Gaal shi ne kociyan tawagar Netherlands, amma rabon da ya ja ragamar kasar tun bayan gasar kofin duniya da aka kammala a Qatar a 2022.

    Wanda ya horar da Ajax Amsterdam da Barcelona da Bayern Munich da Manchester United ya ce zai so kociyan wata kasar, maimakon ƙungiya, abin da zai sa ya koma fagen daga kenan.

    Van Gaal shi ne mai bayar da shawara na musamman ga Ajax.

  20. Newcastle United ta ɗauki Elanga £55m

    Elanga

    Asalin hoton, Getty Images

    Newcastle ta kammala sayen ɗan wasan Nottingham Forest, Anthony Elanga kan £55m.

    Mai shekara 23 ɗan kasar Sweden, zai kara karfin gurbin masu cin ƙwallaye a kokarin da Eddie Howe ke yi na taka rawar gani a Champions League da za su buga, sakamakon karewa a mataki na biyar a tenurin Premier League da ta wuce.

    Elanga ya ci ƙwallo shida ya bayar da 11 aka zura a raga a ƙungiyar da Nuno Espirito Santos ke jan ragama, wadda ta taka rawar gani a 2024/25.

    Ya koma Forest a 2023 kan £15m daga Manchester United kan yarjejeniyar kaka biyar.

    Elanga ya je Old Trafford yana da shekara 12, wanda ya yi mata karawa 55 daga baya ya koma Forest da taka leda.