Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 30/12/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail da Haruna Kakangi

  1. Kamfanonin sadarwa sun yi barazanar mayar da sabis karɓa-karɓa

    Ƙungiyar masu kamfanonin sadarwa a Najeriya ta yi gargadin cewa za a iya fuskantar katsewar network matuƙar ba a sauya tsarin yadda suke cajar kuɗaɗe a fannin sadarwa ba duk da yadda suke gudanar da ayyukansu ke ƙara tsada.

    Shugaban ƙungiyar masu kamfanonin sadarwa da ke da lasisi a Najeriya Gbenga Adebayo ne ya bayyana hakan a yau Litinin cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce ɓangaren sadarwa na tsaka maki wuya saboda tashin gauron zabi da ake fuskanta sakamakon tashin farashin kayayyaki, da rashin tabbas a kasuwar musayar kudi da kuma tashin farashin makamashi.

    Cikin sanarwar Mista Adebayo yace duk da ƙalubalen da ake fuskanta na gudanarwa, har yanzu ba su ƙara kuɗaɗen da suke cajar mutane ba, wani abu da yake barin masu kamfanonin cikin mawuyacin hali wajen kiyaye ingancin aikin da suke gudanarwa.

    Shugaban ƙungiyar ya ce matuƙar ba a dauki mataki kan kudaden da suke cajar mutane ba a ƙara su, to za a iya fuskantar taƙaitar sabis a wasu yankuna.

    Ya ce yayin da ake shirin shiga sabuwar shekara masu kamfanoni na shirin taƙaita bayar da sabis a wasu yankuna duk kuwa da cewa sun san hakan zai iya haifar da koma bayan tattalin arziƙi da katsewar kasuwancin da suka dogara kacokan kan intanet.

    A 2025, wuraren gwamnati irinsu Bangaren tsaro da ilimi da lafiya da kuma kasuwanci da suka dogara kan kamfanonin sadarwa wajen aikinsu za su fuskanci katsewar network.

    Za a mayar da sabis tamkar yadda ake yi wa wutar lantarki a bayar a wannan yankin a ɗauke a wannan yankin, matuƙar ba a yi wa tufkar hanci ba.

    Ya ce nauyin da ke wuyar kamfanonin sadarwa na neman durƙusar da su, don haka an kai matuƙar da ba za su iya ɗauka ba, wanda hakan ya sa ba za su iya gudanar da aikinsu ba a zamanance saboda tsadar lamura.

    A watan Afrilun wannan shekarar ne kamfanonin suka fara kuka kan a ba su damar ƙara kudaden da suke caji, amma har ya zuwa yanzu ba a samu wani ci gaba ba.

    A wani mataki na nuna damuwa kan matsalar tattalin arziki da fannin yake fuskanta, ALTON ta nemi gwamnatin tarayya ta yi zaman tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkokin sadarwa.

    Kungiyar ta ce akwai buƙatar fitar da wani tsari da zai daidaita yadda za su riƙa caji da kuma yadda abokan hulɗarsu za su iya biyan abin da za a caje su domin fanni ya ci gaba da ɗorewa. Bayan shekaru 11 da aka yi da tsarin cajin kuɗi guda.

  2. WHO ta nemi China ta bayar da bahasi kan cutar korona

    Hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi kira ga ƙasar China ta bada bayanan salsalar ɓarkewar annobar cutar korona, shekaru biyar bayan bullarta a birnin Wuhan.

    WHO ta ce bayanan za su taimaka wajen gano yadda annobar ta fara musamman ga fannin lafiya, kuma rashin samun bayanan babbar illa ce ga fannin lafiya da kokarin kare afkuwar wata annobar nan gaba.

    Yawancin masana kimiyya sun haƙiƙance cewa an samo cutar ne daga jikin dabbobi sakamakon yada ta ga bil'adama, wasu kuma na zargin cutar ta fantsama ne daga dakin gwaje-gwaje na birnin Wuhan.

  3. Russia da Ukraine sun yi musayar fursunoni

    Kasashen Rasha da Ukraine sun yi musayar fursunonin yaki mafi girma tsakaninsu.

    Moscow ta ce musayar da Hadaddiyar Daular Larabawa ta shiga tsakani ta shafi fursunoni 150 daga kowanne ɓangare.

    Sai dai wakilin BBC ya ce motocin bas-bas sun sauke fursunonin a wajen asibiti, wasu naɗe da tutar ƙasar Ukraine, sannan 'yanuwan fursunonin sun shaida masa an sako 180 maimakon 150.

    Ya bayyana yadda 'yanuwa ke ta kuka da rungume juna da zarar sun ga nasu na cikin waɗanda suka shaki iskar 'yanci.

    Wakilin BBC ya ce yawancin mutanen ba sa cikin koshin lafiya, yayin da wasu ke dauke da munanan raunuka jikinsu.

  4. Kotu a Mali ta kama aminin shugaban ƙasa kan ɓatanci ga shugaban Burkina Faso

    Wata kotu a Mali ta yanke wa wani fitaccen dan siyasa hukuncin zaman kaso na shekaru 2, kan sukar gwamnatin mulkin soja ta Burkina Faso.

    An zargi Issa Kaou N’Djim wanda tsohon aminin shugaban mulkin sojin Mali ne, da laifin cin mutuncin shugaban wata ƙasa.

    Wannan ya biyo bayan wata hira da aka yi da shi a gidan talbijin din Mali a watan Nuwamba, inda yake tababa kan sahihancin kitsa juyin mulkin da aka ce an yi a Burkina Faso.

    Gwamnatocin mulkin soji a Mali da Burkina Faso na kara ƙaimi wajen rufe bakin 'yan adawa da masu sukar su ciki har da ƴan jarida na ciki da wajen ƙasashen.

  5. Gwamnatin Taliban ta ƙara gargaɗar ƙungiyoyi masu aikin agaji a Afghanistan

    Gwamnatin Taliban a Afghanistan ta ƙara gargaɗi da jaddada haramcin ayyukan ƙungiyoyin agaji na ƙasashen waje, inda suka ce waɗanda ba su bi umarnin ba za a rufe su nan take.

    Shekaru biyu da suka gabata ne aka sanya haramcin ayyukan ƙungiyoyin.

    A wata sanarwa da ma'aikatar tattalin arziƙi ta aikewa wasu daga cikin irin ƙungiyoyin da ake kyautata zaton har yanzu akwai mata da ke aiki a wuraren.

    Sai dai haramcin bai shafi ƙungiyoyin da suka shafi na ilimi da lafiya ba, matukar ma'aikata matan na bin dokokin da Taliban ta gindaya mu su.

    Sai dai ƙungiyoyin sun yi ƙorafin ba za su iya ci gaba da taimakon mata da ƙananan yara ba tare da ma'aikata mata ba.

  6. Gwamnan jihar Rivers ya gabatar da kasafin kuɗin 2025 ga ƴan majalisa biyar

    Gwamnan Jihar Rivers Siminalayi Fubara ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2025 na naira triliyan ɗaya da biliyan ɗari takwas a gaban ƴan majalisu guda biyar domin dubawa da kuma amincewa.

    Fubara ya ce za a aiwatar da kasafin kudin shekara mai zuwa domin tabbatar da samun cigaba a tattalin arziki mai ɗorewa, da kawo cigaba ga jihar, a lokaci guda kuma zai inganta rayuwar ƴan jihar.

    Gwamnan ya ce an ware sama da biliyan 30 a fannin noma, yayin da ya ce an ware naira biliyan 63 a fannin samar da ilimi, sai kuma fannin kiwon lafiya da zai laƙumi sama da naira biliyan 97.

    Kasafin kuɗin bana ya haura na bara inda aka gabatar da maira biliyan 800 a matsayin kasafin kudin 2024.

  7. Duniya ta jure wa zafi mai tsanani tsawon shekara 10 - MDD

    Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta ce duniya ta jure wa tsananin zafin da ba a taɓa gani ba har na shekara 10 babu ƙaƙƙautawa.

    Babban sakataren MDD, Antonio Guterres, ya bayyana lamarin da ''bayani dalla-dalla kan sahihin sauyin yanayi".

    A cewarsa: "A hukumance, a yau zan sanar da ku irin matsanancin zafin da duniya ta samu kan ta a ciki shekara 10 babu ƙaƙƙautawa, ciki har da shekarar nan mai ƙarewa. Ya kamata mu ɗauki matakan gaggawa na rage yawan gurɓataccen hayakin da ake fitarwa da rungumar makamashi mai inganci".

    Masu hasasshen yanayi sun ce sauyin yanayi ne ya haddasa ambaliyar ruwa da guguwa da fari a sassa daban-daban na duniya da aka gani a baya-bayan nan.

  8. Abubuwan da suka sa ƴan Najeriya farin ciki a 2024

    A yayin da shekarar 2024 ke bankwana, shekarar ta kasance mai cike da ƙalubale a Najeriya, daga matsalar rashin tsaro zuwa matsin tattalin arziki.

    Sai dai duk da cewa ko a rahoton ƙasashen da ƴan ƙasarsu suka fi farin ciki a duniya Najeriya ba ta cikin 10 ko 20 na farko, akwai abubuwa da dama da suka faru a shekarar waɗanda aƙalla suka sanya wasu ƴan ƙasar farin ciki.

    Ga wasu daga cikin abubuwan da muka zaƙulo >>>>>>

  9. Yadda Amurka ta mayar da mashigar ruwa ga al'ummar Panama

    Ranar 31 ga watan Disamban 1999. Tutar Amurka ta sauka, inda ita kuma ta Panama ta ɗaga ta kuma filfila a matsayin alama ɗaya tilo ta yankin mashigar ruwan a karon farko. Ƴan Panama da ke wurin sun yi murna.

    Faruwar hakan ce ta kawo ƙarshen tashin hankali da kisa da zanga-zanga.

    "Abun sha'awa ne ganin yadda al'ummar Panama suka mayar da martani a lokacin," in ji Roberto Aleman Zubieta wanda shi ne kantoman mulki a mashigar ruwan ta Panama na shekaru da dama, kamar yadda ya shaida wa BBC.

    Shekaru 25 bayan nan, cin gashin kan yankin da ya zamo wata hanyar ruwa ga al'ummar duniya ya kankane manyan kafafen watsa labarai bayan wasu maganganu masu cike da taƙaddama da zaɓaɓɓen shugaban Amurka, Donald Trump ya yi.

  10. Kotun ɗaukaka ƙara ta jaddada hukuncin kama Trump da laifin cin zarafin 'yarjarida Jean Caroll

    Wata kotun ɗaukaka ƙara a Amurka ta jaddada hukuncin kama shugaban Amurka mai jiran gado, Doald Trump, da laifin cin zarafi da kuma ɓata sunan 'yarjarida E. Jean Carroll.

    Kotun ta ci tarar Trump dala miliyan biyar game da tuhumar.

    Shari'ar ta ji bahasi kan wani hari da ya faru a shekarar 1990 a New York, da kuma yunƙurin da Trump ya yi na yin watsi da batun a matsayin ƙarya.

    A wani lamari mai kama da wannan, an umarce shi ya biya Ms Caroll sama da dala miliyan 80 saboda ɓata suna, da kuma kimarta.

    Shugaban ya ɗaukaka ƙara a kan wannan ma.

  11. Ni da 'yan Najeriya muna cikin farin cikin gyara matatar mai ta Warri - Tinubu

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce "shi da 'yan ƙasar suna cike da farin ciki" sakamakon gyara matatar mai ta garin Warri da kamfanin mai na NNPCL ya yi.

    Wani saƙo da shugaban ya wallafa a shafinsa na X ya ce "hakan zai ƙara wa 'yan Najeriya ƙwarin gwiwa kan fatan da suke da shi game da alƙawuran da muka yi".

    Ya ƙara da cewa labarin "hanya ce mai kyau ta kammala shekarar 2024 idan aka ƙara da nasarar da aka samu kan matatar mai ta Fatakwal".

    Yayin wani taron manema labarai a yau Litinin, shugaabn kamfanin NNPCL Mele Kyari ya bayar da sanarwar cewa sun gyara matatar kuma ta ci gaba da aiki a matakin kashi 60 cikin 100 na ƙarfinta.

    A cewar Tinubu: "Tun da yanzu matatar Warri na aiki bisa kashi 60 cikin 100, tsarin gwamnatina na samar da tabbataccen makamashi yana kan hanya.

    "Ina shawartar NNCPL ya hanzarta gyara matatar mai ta Kaduna da ɗaya matatar ta Fatakwal domin tabbatar da matsayin Najeriya wajen samar da makamashi a duniya."

  12. Bidiyoyin BBC Hausa da aka fi kallo a shafin Facebook a 2024

    A shekarar 2024, mun wallafa muku bidiyoyi masu yawa na faɗakarwa, ilimantarwa, da nishaɗantarwa, domin jin daɗin ku masu bibiyarmu.

    Ko kun san wane bidiyon BBC Hausa kuka fi kallo a shanfinmu na Facebook a 2024?

  13. Mutumin da aka ɗaure bayan ya sa maza 50 sun yi wa matarsa fyaɗe ba zai ɗaukaka ƙara ba

    Dominique Pelicot - mutumin nan da aka ɗaure bisa laifin tattaro maza domin yi wa matarsa fyaɗe a Faransa - ya ce ba zai ɗaukaka ƙara ba.

    Lauyoyinsa sun ce mutumin ba shi son matar tasa Gisele Pelicot ta sake shiga wani sabon ƙuncin. Sai dai kuma wasu daga cikin mazan da aka ɗaure su tare za su ɗaukaka ƙara.

    Lamarin ya girgiza Faransawa da duniya baki ɗaya, amma kuma Gisele ta sha yabo saboda jajircewar da ta nuna wajen bayyana kanta domin ganin ta kunyata miyagun.

  14. Babu yarjejeniyar yin karɓa-karɓa tsakanina da Atiku - Kwankwaso

    Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya musanta raɗe-raɗin da ke cewa an cimma yarjejeniya tsakaninsa da tsofaffin ƴan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyun hamayyar ƙasar - Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP - kan cewa kowannensu zai yi mulki na wani wa'adi.

    A hirarsa da BBC, Kwankwaso ya ce bai san da maganar ba, amma ya samu labarin cewa ɓangaren Atikun na ta "yin taruka da shugabannin yankin ciki har da malamai, suna faɗa masu wannan magana".

  15. Gwamnatin Nijar ta kori kamfanonin sadarwa na Faransa

    A Jamhuriyar Nijar, gwamnatin mulkin sojan kasar ta sanar da korar kamfanonin sadarwa na ƙasar Faransa na Camusat da Aktivko a duk faɗin ƙasar.

    Camusat na ɗaya daga cikin manyan kamfanonin sadarwa a Nijar, da kuma Aktivko wanda ya ƙware wajen samar da makamashi ga turakun sadarwa na wayoyin salula.

    Wannan na zuwa ne a loƙacin da hukumomin mulkin sojan Nijar ke ci gaba da korar kamfanonin Faransa daga Nijar a ƙoƙarin raba gari da ita baki daya.

    Wata sanarwa da Ministan Sadarwa Sidi Muhammad ya fitar ta ce an haramta wa dukkan 'yan ƙasa yin aiki tare da kamfanonin, amma babu wani cikakken bayanin dalilin da ya sa gwamnatin ta ɗauki matakin a yanzu.

    Sai dai masu lura da al'amuran yau da kullum a Nijar na cewa matakin ba zai rasa nasaba da tsaron ƙasa ba.

    A gefe guda kuma, masu adawa da gwamnatin mulkin sojan na cewa haramcin yunƙuri ne kawai na kafa kamfanin da sojojin ke so.

  16. Waƙoƙin Kannywood da suka fi jan hankali a 2024

    Kamar kowane fanni, fagen waƙoƙin Kannywood sun yi tashe a 2024, inda mawaƙan Hausa suka baje-kolin fasaharsu wajen fito da saƙonni daban-daban a ciin waƙoƙin nasu.

    An rera waƙoƙi masu yawan gaske a wannan shekara, inda wasu da dama suka yi tashen da ba a yi hasashen za su yi ba.

    Shafukan sada zumunta kan taimaka wajen fahimtar waƙoƙin da suka fi farin jini tsakanin masu sauraro, ta hanyar sanya su a gajerun bidiyoyin da ake wallafawa a shafukan, kamar TikTok da Instagarm da Facebok.

    Kan haka ne BBC Hausa ta bibiyi shafukan, ta kuma rairayo biyar daga cikin waƙoƙin da suka fi samun samun kallo, tun bayan da aka ɗora su a cikin shekarar.

  17. Shugaban Amurka Biden ya bai wa Ukraine ƙarin dala biliyan 2.5 na tallafin soji

    Shugaba Biden na Amurka ya sanar da ƙarin tallafin soji da tsaro ga Ukraine da ya kai kusan dala biliyan biyu da rabi.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ya rage mako ɗaya Mista Biden ya kammala wa'adin mulkinsa.

    Sai dai ana nuna damuwa kan yiwuwar sabon shugaban Amurka Donald Trump ka iya rage tallafin ƙasar ga Ukraine.

    Biden ya ce samar da tallafin ga Ukraine domin kare kai daga mamayar Rasha na ɗaya daga cikin muhimman abubuwa ga gwamnatinsa.

    Ya ƙara da cewa tuni ma'aikatar tsaron Amurka ta fara ƙoƙarin kai wa Ukraine ɗin dubun-dubatar makaman atilare da rokoko da motoci masu sulke.

  18. NNPCL ya ce matatar mai ta Warri ta koma aiki

    Kamfanin mai na gwamnatin Najeriya NNPCL ya ce matatar mai ta garin Warri na jihar Delta ta ci gaba da aiki.

    Shugaban NNPCL Mele Kyari ne ya bayyana hakan a yau Litinin yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a matatar mai ƙarfin tace gangar mai 125,000 a kullum.

    "Duk da cewa ba 100 bisa 100 take aiki ba, muna kan aikin gyaran," in ji shi yayin da shugaban hukumar kula da harkokin mai na kamfanin Farouk Ahmed ke yi masa rakiya.

    "Mutane da yawa na tunanin yunƙurin namu ba gaskiya ba ne. Suna tunanin ba zai yiwu a aiwatar da abubuwa na ƙwarai a Najeriya ba, amma muna so ku gani da idonku."

    Matatar da ke yankin Ekpan na Warri, an ƙaddamar da ita a shekarar 1978 domin samar da mai ga jihohin kudancin Najeriya bisa kulawar kamfanin NNPCL .

    A cewar mai magana da yawun NNPCL, Olufemi Soneye, an tsara kammala aikin ne tun cikin wata ukun farko na 2024.

    A watan Nuwamban da ya gabata ne NNPCL ya ce ya kammala gyaran tsohuwar matatar mai ta Fatakwal.

  19. Ana ƙirga ƙuri'un zaɓen 'yanmajalisa a Chadi

    Ana ci gaba da ƙirga ƙuri'u a zaɓen 'yanmajlisar Chadi da aka gudanar ranar Lahadi, wanda shi ne na farko cikin shekara 13.

    Sai dai wasu jam'iyyun adawa sun ƙaurace wa zaɓen saboda zargin rashin sahihanci.

    Sakamakon zaɓen zai zama wani cikamako ne da zai tabbatar da nasarar gwamnatin Shugaba Mahamat Idriss Deby wajen komawa kan turbar dimokuradiyya.

    An fara buɗe rumfunan zaɓen ne ga makiyaya da kuma dakarun sojin ƙasar a ranar Asabar, inda sauran al'umma suka ci gaba da kaɗa ƙuri'ar da misalin ƙarfe 7:00 na safiyar Lahadi.

    Sama da mutum miliyan takwas ne suka yi rajistar zaɓen a Chadi da ke yankin Afirka ta Tsakiya.

    Sai nan da 15 ga watan Janairu ake sa ran samun sakamakon zaɓen na farko-farko, sai kuma cikakken sakamako mako biyu bayan haka.

    Ana fafatawa ne kan kujeru 188 a majalisar ƙasar da za su fito daga yankuna 22 da kuma babban birni N'Djamena.

    Jam'iyya na buƙatar kujera 95 kafin ta samu rinjaye.

  20. Mutum 71 sun mutu bayan motarsu ta afka cikin kogi a Habasha

    Aƙalla mutum 71 ne suka mutu a ƙasar Habasha ko kuma Ethiopia bayan babbar motar da suke ciki ta kauce hanya tare da afkawa cikin kogi.

    Cikin wata sanarwa a dandalin Facebook a daren Lahadi, rundunar 'yansandan jihar Sidama ta ce akwai maza 68 da mata uku cikin waɗanda suka mutu a hastarin, a cewar babban sufeton 'yansanda Daniel Sankura.

    Rundunar ta ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:30 na yammacin ƙasar lokacin da motar ta afka ruwan kogin.

    Sanarwar ta ƙara da cewa "wasu mutum biyu sun ji munanan raunika", amma ba ta ƙara wani bayani ba game da yawan fasinjojin da ke cikinta a lokacin hatsarin.

    Hatsarin ya faru ne a jihar Sidama mai nisan kilomita 300 daga Addis Ababa babban birnin ƙasar.