Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 30/12/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail da Haruna Kakangi

  1. Ba za mu gama aiki kan kasafin 2025 ba kafin sabuwar shekara - Majalisar Dattawan Najeriya

    Majalisar Dattawan Najeriya ta gargaɗi 'yan ƙasar da kada su tsammaci za ta kammala tantance kasafin kuɗin 2025 da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya gabatar mata kafin sabuwar shekara.

    A ranar 18 ga watan Disamba ne Tinubu ya gabatar da kasafin naira tiriliyan 49.7 a zaman haɗin gwiwa tsakanin 'yanmajalisar dattawa da na wakilai, kuma ya neme su da su gaggauta amincewa da dokar.

    Shugaban kwamatin yaɗa labarai na majalisar, Sanata Yemi Adaramodu (APC a jihar Ekiti) ya faɗa wa manema labarai jiya Lahadi cewa sai a ranar 7 ga watan Janairu ma za su fara sauraron jawabin kare kasafi na hukumomi da ma'aikatun gwamnatin tarayya.

    Ya ƙara da cewa kwamatin kula da harkokin kuɗi na majalisun zai gabatar da rahotonsa na ƙarshe ne a ranar 31 ga watan na Janairu.

  2. Gwamnatin Tinubu ta karɓi bashin Bankin Duniya bayan cika sharaɗin cire tallafin mai

    Bankin Duniya ya danƙa wa Najeriya bashin dala biliyan ɗaya da rabi bayan gwamnatin Bola Tinubu ta aiwatar da wasu daga cikin tsare-tsaren tattalin arziki, kamar yadda rahoton Channels TV ya bayyana.

    Matakin na zuwa ne bayan bankin ya amince da bai wa Najeriyar bashi kashi biyu na jimillar dala biliyan 1.5 kan gyaran tattalin arziki (Reforms for Economic Stabilization to Enable Transformation) da kuma dala miliyan 750 domin ayyukan cigaba (Development Policy Financing Program).

    Daga cikin tsare-tsaren da gwamnatin ta aiwatar akwai cire tallafin man fetur, da kuma bijiro da sabuwar dokar gyaran haraji da ke gaban majalisar dokoki.

    An raba bashin ne gida biyu zuwa miliyan 750 kowanne, inda tun ranar 2 ga watan Yulin 2024 aka bai wa gwamnatin Najeriya kason farko, kamar yadda wani ƙunshin takardu da bankin ya fitar ya nuna.

    Amma kuma sai a watan Nuwamba aka ba ta kaso na biyun saboda sharuɗɗan bayar da shi na ɗamfare da aiwatar da tsare-tsaren tattalin arzikin da gwamnatin ta Bola Tinubu ke yi a yanzu.

  3. Gwamnatin Najeriya ta jajanta wa Koriya ta Kudu kan hatsarin jirgin da ya kashe mutum 179

    Gwamnatin Najeriya ta jajanta wa Koriya ta Kudu game da hatsarin jigrin sama da ya kashe mutum 179 ranar Lahadi.

    Cikin wata sanarwa, Ma'aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta bayyana alhininta ga iyalan waɗanda hatsarin ya shafa, tare da tausaya wa gwamnatinn ƙasar.

    Lamarin ya faru ne lokacin da jirgin ƙirar Boeing 737-800, wanda ke komawa ƙasar daga birnin Bangkok na Thailand, ya yi ƙoƙarin sauka a filin jirgi na Muan International Airport da ke kudancin Koriya ta Kudu.

    Jirgin ya zarce tare da sauka daga titinsa kuma ya tunkuyi wani bango, abin da ya sa ya kama da wuta nan take. Mutum 179 ne suka mutu cikin 181 da ke cikinsa, inda biyu suka tsira da raunuka.

    Tuni hukumomi suka ayyana makokin kwana bakwai.

  4. Wane ne tsohon Shugaban Ƙasa Jimmy Carter da ya mutu?

    Tsohon Shugaban Ƙasar Jimmy Carter ya fara rayuwa a matsayin manomin gyaɗa har ya kai ga jagorantar ƙasar.

    Wa'adi ɗaya Carter ya yi a fadar White House kafin ya sha kaye a hannun Ronald Regan a lokacin da ya tsaya takarar neman wa'adi na biyu.

    Ya shafe shekaru da dama bayan ya sauka daga mulki yana fafutukar kare haƙƙin dan'adam, da tabbatar da adalci, da kyakkyawar zamantakewa, inda ya lashe lambar yabon zaman lafiya ta Nobel Peace a 2002.

  5. Biden da Trump na alhinin rasuwar tsohon Shugaban Amurka Jimmy Carter

    Shugaba Biden da shugaban ƙasa mai jiran gado Donald Trump na jagorantar ta'aziyya da alhinin rasuwar tsohon Shugaban Ƙasa Jimmy Carter.

    Biden ya bayyana shi a matsayin "jajirtaccen shugaba" kuma "cikakken dattijo".

    "A yau, Amurka da duniya, a ganina, sun yi rashin fitaccen shugaba, cikakken dattijo, mai tausaya wa al'umma," in ji Shugaba Biden. "Ni da Jill mun yi rashin abokin arziki."

    A nasa ɓangaren, Donald Trump ya ce ya kamata Amurkawa "su gode wa Mista Carter kan kalubalen da ya fuskanta a lokacin shugabancinsa a wani muhimmin lokaci a tarihin Amurka".

    Carter ya rasu yana da shekara 100 a duniya.

  6. Barka

    Maraba da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa.

    Ku biyo mu domin sanin halin da duniya ke ciki a yau Litinin.

    Ni ne Umar Mikail zan jagoranci shafin bisa kulawar Haruna Ibrahim Kakangi.