An kama saurayin
wata mata, wadda ta kashe kanta, da laifin cin zarafi da wulaƙanta ta,
amma an wanke shi daga zargin aikata kisa.
An gurfanar da
Ryan Wellings, na yankin Lancashire a Birtaniya ne gaban kotu bisa zargin shi
da kashe abokiyar zamansa, Kiena Dawes, wadda ta kashe kanta sanadiyyar cin
zarafi.
Wellings bai
yi ko gezau ba a lokacin da kotu ta wanke shi daga zargin na kisa.
Sai dai ƴar’uwar
marigayiya Dawes ta fashe da kuka a lokacin da aka sanar da hukuncin.
Shi kuwa
Wellings ya yi murmushi sannan ya sumbaci budurwarsa a lokacin da za a fitar da
shi daga kotun, domin nuna farin ciki.
An tuhumi
Wellings da aikata kisan kai ne bayan abokiyar zamansa ta kashe kanta inda ta
bar rubutaccen saƙo cewa: “An kashe ni ne” ta ƙara da cewa Wellings ne “ya
kashe ni”.
An haƙƙaƙe
cewa ta rubuta saƙon ne gabanin ta kashe kanta a ranar 22 ga watan Yulin 2022.
Marigayiya Dawes ta haɗu da Wellings ne a watan Janairun 2020, inda suka fara soyayya nan take.
Cikin mako ɗaya bayan haɗuwarsu, Dawes - wanda a baya aka taɓa kamawa da laifin cin zarafin abokiyar zamansa - ya sa an zana masa suna da fuskar sabuwar masoyiyarsa Dawes a jikinsa.
Haka nan ya yi mata alƙawarin aure a cikin wata uku.
Sai dai bayan sun fara zama tare, Dawes ta ce “mafarkinta mai daɗi” ya koma “mafarkin tashin hankali”, kasancewar Wellings mutum ne mai saurin zuciya kuma yana yawan shaƙar hodar iblis da kuma kwankwaɗar barasa.
Cikin abubuwan da ya riƙa yi mata har da mari a kai-a kai, da jan gashin kanta, da kuma barazanar karya mata haƙora, kamar yadda aka shaida wa alƙali.
Wellings ya yi mata tabo a fuska a lokacin da ta samu ciki, inda ya riƙa sukar ƙibar da ta yi, sannan ya riƙa bin karuwai a shafukan sada zumunta.
Ana sa ran yanke wa Wellings hukunci a ranar 16 ga watan Janairu.