Usman Minjibir, Ibrahim Muhammad da Isiyaku Muhammed
Muna da ƙwarin gwiwar cewa Isra'ila za ta iya kare kanta - Blinken
Asalin hoton, Reuters
Sakataren harkokin wajen Amurka mai barin gado, Antony Blinken ya ce Hamas na son ta tsunduma gabas ta tsakiya cikin yaƙi sanadiyyar hare-haren da take kai wa Isra'ila
Sai dai ya ce sojojin Isra'ila sun nuna wa ƙungiyar iyakarta ta hanyar wargaza shirin nata.
A jawabinsa na karshe kan gabas ta tsakiya, Mista Blinken ya ce martanin da Isra'ila ta mayar ya tabbatar da cewa tana iya kare kanta, yanayin da ya tilasta wa Hamas daukan sabbin sojoji yayin da ake cigaba da kashe su.
Yayin da mutane suka yi ta ƙoƙarin katse shi a lokacin jawabin nasa a Washington, Mista Blinken ya ce ya so fadin cewa gwamnatin Biden ta yi daidai a matakan da ta ɗauka.
Kotu ta wanke mutumin da matarsa ta ce 'shi ne ya kashe ta'
Asalin hoton, Lancashire Police
Bayanan hoto, Wellings ya shaida wa alƙali cewa bai taɓa bugun Dawes da gangan ba, sai dai domin ya kare ta daga wani abu da zai cutar da ita
An kama saurayin
wata mata, wadda ta kashe kanta, da laifin cin zarafi da wulaƙanta ta,
amma an wanke shi daga zargin aikata kisa.
An gurfanar da
Ryan Wellings, na yankin Lancashire a Birtaniya ne gaban kotu bisa zargin shi
da kashe abokiyar zamansa, Kiena Dawes, wadda ta kashe kanta sanadiyyar cin
zarafi.
Wellings bai
yi ko gezau ba a lokacin da kotu ta wanke shi daga zargin na kisa.
Sai dai ƴar’uwar
marigayiya Dawes ta fashe da kuka a lokacin da aka sanar da hukuncin.
Shi kuwa
Wellings ya yi murmushi sannan ya sumbaci budurwarsa a lokacin da za a fitar da
shi daga kotun, domin nuna farin ciki.
An tuhumi
Wellings da aikata kisan kai ne bayan abokiyar zamansa ta kashe kanta inda ta
bar rubutaccen saƙo cewa: “An kashe ni ne” ta ƙara da cewa Wellings ne “ya
kashe ni”.
An haƙƙaƙe
cewa ta rubuta saƙon ne gabanin ta kashe kanta a ranar 22 ga watan Yulin 2022.
Asalin hoton, Family handout
Bayanan hoto, Alƙalai sun saurari ƙorafin da ya nuna cewa Kiena Dawes ta shafe shekara biyu tana fuskantar cin zarafi a hannun Wellings
Marigayiya Dawes ta haɗu da Wellings ne a watan Janairun 2020, inda suka fara soyayya nan take.
Cikin mako ɗaya bayan haɗuwarsu, Dawes - wanda a baya aka taɓa kamawa da laifin cin zarafin abokiyar zamansa - ya sa an zana masa suna da fuskar sabuwar masoyiyarsa Dawes a jikinsa.
Haka nan ya yi mata alƙawarin aure a cikin wata uku.
Sai dai bayan sun fara zama tare, Dawes ta ce “mafarkinta mai daɗi” ya koma “mafarkin tashin hankali”, kasancewar Wellings mutum ne mai saurin zuciya kuma yana yawan shaƙar hodar iblis da kuma kwankwaɗar barasa.
Cikin abubuwan da ya riƙa yi mata har da mari a kai-a kai, da jan gashin kanta, da kuma barazanar karya mata haƙora, kamar yadda aka shaida wa alƙali.
Wellings ya yi mata tabo a fuska a lokacin da ta samu ciki, inda ya riƙa sukar ƙibar da ta yi, sannan ya riƙa bin karuwai a shafukan sada zumunta.
Ana sa ran yanke wa Wellings hukunci a ranar 16 ga watan Janairu.
Kuɗin hayar gidaje ya yi tashin gwauron zabi a Los Angeles
Asalin hoton, Getty Images
Nan ba da jimawa ba dubban mazauna LA da gobarar daji ta raba da muhallansu za su fuskanci ƙalubale na neman wurin zama a kasuwar gidaje ta LA - wadda tun asali ta kasance ɗaya daga cikin kasuwannin gidaje mafi tsada a ƙasar.
Mazauna yankin da ke neman wurin zama sun zanta da BBC game da fargabar ganin ƙarin kuɗin haya yayin da suke ƙoƙarin farfaɗowa daga asarar da gobarar ta janyo musu.
Michael Storc, wanda ya rasa gidan da mallaka a gobarar ya ce "Gidajen da ke akwai ba su da kyau ko kaɗan, kuma kuɗin hayar na da matuƙar tsada."
Jessica Heredia, wata mai harkar gidaje ne a unguwar masu hannu da shuni ta Brentwood, ta nuna wa BBC wata ma’adanar bayanai da ƴan kasuwa ke amfani da su wajen bin diddigin hauhawar farashin haya, ta kuma gano cewa kuɗɗen hayar wasu manyan gidaje sun ƙaru da dubban daloli a cikin wannan makon kaɗai.
'Ukraine ta ƙaddamar da hari mafi girma kan Rasha'
Ukraine ta ce ta kai hari kan wurare da dama a cikin Rasha a yau Talata, wani abu da ta bayyana a matsayin "hari mafi girma" da ta kai a Rasha tun bayan fara yaƙi.
Babban hafsan tsaron Ukraine ya ce harin ya faɗa kan rumbunan ajiye makamai da cibiyoyin adana sanadarai masu guba a yankunan da dama, wadanda suka kai nisan ɗaruruwan kilomitoci daga kan iyakar ƙasashen biyu.
Rasha ta sanar da cewa ta kakkaɓo makamai masu linzami samfurin Atacms waɗanda Amurka ta bai wa Ukraine gudumawa da kuma makami mai linzami na Storm Shadow na Birtaniya, kuma ta lashi takobin ɗaukar fansa.
Aƙalla filayen jiragen sama 9 ne a tsakiya da yammacin Rasha suka tsayar da zirga-zirga sanadiyyar hare-haren, yayin da makarantu a kudu maso yammacin yankin Saratov suka rufe.
Hare-haren da aka kai a yankin Bryansk na kusa da kan iyaka ya haifar da fashewar abubuwa a wata matatar man fetur, da rumbunan ajiye makamai da kuma cibiyoyin sanadarai masu guba, kamar yadda wata majiya daga ɓangaren tsaro na Ukraine ta tabbatar wa BBC.
Kuma babban hafsan tsaron na Ukraine ya bayyana cewa sun kai hare-hare har zuwa wurare masu nisan kimanin kilomita 1,100 daga kan iyaka.
Asalin hoton, White Sands Missile Range Public Affairs
Nasarar da Trump ya yi a zaɓe ta hana a ɗaure shi - Rahoto
Asalin hoton, Reuters
Da zaɓaɓɓen shugaban Amurka Donald Trump bai samu nasarar sake zaɓensa a shekara ta 2024 ba, da za sai an kama shi da laifin yunƙurin kifar da sakamakon zaɓen shugaban kasa na 2020 da ya sha kaye, a cewar mutumin da ya jagoranci binciken gwamnatin Amurka a kansa.
Shaidun da aka samu a kan Trump "sun isa a same shi laifi a kuma tabbatar da hukunci a kansa a gaban kotu," lauya na musamman Jack Smith ya rubuta a cikin wani rahoton da aka fitar.
Trump ya mayar da martani, yana mai cewa Smith yana fama da “taɓin hankali” kuma bincikensa “ƙarya ne”
An zargi Trump da tursasawa jami'ai su sauya sakamakon zaɗen na 2020, da yada ƙarya game da maguɗin zaɓe da kuma neman yin amfani da tarzomar da aka yi a majalisar dokokin Amurka a ranar 6 ga Janairu 2021. Ya dai musanta aikata ba daidai ba.
Trump, wanda ya kasance shugaban ƙasa a lokacin da ake zarginsa da aikata laifukan, ya shafe shekara huɗu ba ya fadar White House- amma an yi nasarar sake zaɓensa a watan Nuwamba.
A mako mai zuwa ne zai koma kan karagar mulkin ƙasar.
An sake ciro wasu gawarwaki daga wata mahaƙar ma'adanai a Afirka ta Kudu
Asalin hoton, Giwusa
An ciro wasu gawarwaki shida daga wata mahaƙar ma'adinai a Afirka ta Kudu yayin da ake kwana na biyu ana ƙokarin taimakawa wasu masu hakar ma'adanai ba bisa ka'ida da suka maƙale a cikin ramin haƙar ma'adinan da ke da zurfin kusan kilomita biyu.
Mutane takwas ne suka fito da ransu a ranar Talatar da ta gabata yayinda aka ceto mutane 26 aka kuma zaƙulo gawawwaki tara a ranar litinin.
Mutanen dai sun kasance a ƙarƙashin ƙasa tun lokacin da ƴansanda suka fara kai hare-hare kan masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a bara a faɗin ƙasar.
A makon da ya gabata ne wata kotu ta umurci gwamnati da ta gudanar da aikin ceto wanda aka daɗe ana jinkiri a kai.
Fiye da mutane 100 daga cikin masu hakar ma'adinan ba bisa ka'ida ba ne suk mutu a ƙarƙashin ƙasa tun lokacin da jami'ai suka kai farmaki a mahakar ma'adinan mai tazarar kilomita 145 daga birnin Johannesburg.
Rundunar ƴansandan Najeriya ta buƙaci ƙungiyar Amnesty ta janye kalamunta
Asalin hoton, Nigeria Police
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta buƙaci Kungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International a Najeriya, da ta gaggauta janye kalaman da ta wallafa na zargin jami’an tsaro da aikata laifukan cin zarafin masu zanga-zanga,
Ta kuma buƙaci ƙungiyar ta nemi afuwar al’umma.
A cewar kakakin rundunar Muyiwa Adejobi, ya ce an riga an aike wa ƙungiyar wasikar tun a ranar shida ga wannan watan na Janairu, kuma muddin ba ta aiwatar da wannan buƙata ba, rundunar ƴan sandan za ta ɗauki matakin shari'a
Bayanin da rundunar ta fitar ya nuna cewa akwai abubuwa da dama da suka haɗa zarge-zargen da rundunar ƴan sandan ta ce na ƙarya ne, masu nasaba da take hakkin ɗan Adam ta hanyar azabtar da masu zanga-zanga.
Bayanin ya ce akwai hujjoji ƙarara da suka nuna babu wani abu makamancin haka da ya wanzu, ciki kuwa har da hotunan bidiyo da gidajen talabijin suka watsa kai tsaye a lokacin da ake gudanar da zanga-zangar ta watan Agustan shekarar 2024, kuma rundunar ƴan sandan ta yi nazarin ƙwaƙwaf tare da gudanar da bincike inda ta gano dukan abubuwan da kungiyar ta yi iƙirari ba su da ƙamshin gaskiya.
A cewar rundunar ƴansandar Najeriyar, jami’anta sun yi amfani da ƙwarewa tare da bin cikakkun ka’idojin aikin da aka san jami’an tsaro da su, har ma a wuraren da suka fuskanci farmaki daga masu zanga-zanga bai sa sun yi amfani da ƙarfin da ya wuce kima ba.
Ƴanbindiga sun kashe sama da mutane 100 a Sudan
Rahotanni daga Sudan na cewa an kashe sama da mutane 100 a ranar Litinin sakamkon harbe-harbe na kan mai uwa da wabi da wasu mutane masu ɗauke da makamai suka yi a yankin Omdurman, da ke kusa da birnin Khartoum.
Wata ƙungiyar agaji ta Ombada, ta ce ba su iya gano waɗanda suka kai harin ba.
Kwana nan sojojin Sudan suka samu nasarar karɓe wasu yankunan da ke hannun dakarun RSF.
Wakilin BBC ya ce, ana dai zargin ɓangarorin da ke rikici da juna da kashe fararan-hula, ciki har da jami'an lafiya da kuma kai hare-hare mara kan gado kan unguwanni.
Kotu ta fara zama kan batun tsige shugaban Koriya ta Kudu
Asalin hoton, Getty Images
Kotun tsarin mulkin ƙasar Koriya ta Kudu ta gudanar da zamanta na farko don yanke hukunci kan ko za a tsige shugaban ƙasar Yoon Suk Yeol da aka dakatar daga mukaminsa bayan yunƙurin da ya yi na sanya dokar mulkin soja a ƙasar a watan da ya gabata.
An kammala sauraren ƙarar ne a cikin mintuna hudu saboda rashin halartar Yoon - tun da farko lauyoyinsa sun ce ba zai halarci zaman kotun ba domin kare lafiyarsa, saboda akwai sammacin kama shi bisa zargin tayar da ƙayar baya.
A watan Disamba, an dakatar da Yoon bayan da ƴan jam'iyyarsa suka kaɗa ƙuri'ar tsige shi.
Sai dai za a tsige shi a hukumance ne kawai idan aƙalla shida daga cikin mambobi takwas na kotun tsarin mulkin ƙasar suka kaɗa ƙuri'ar tabbatar da tsige shi.
A bisa dokar ƙasar Koriya ta Kudu, dole ne kotun ta sanya sabon ranar da za a ci gaba da sauraren ƙarar ba tare da halartar sa ba.
A ranar Alhamis mai zuwa ne dai aka shirya ci gaba sauraren ƙarar.
Yoon bai ce uffan a bainar jama'a tun bayan da majalisar dokokin ƙasar ta kaɗa ƙuri'ar tsige shi a ranar 14 ga watan Disamba kuma yana magana ne ta bakin lauyoyinsa.
Babban layin lantarkin Najeriya zai ci gaba da lalacewa - ministan lantarki
Asalin hoton, Getty images
Babban layin wutar lantarki na ƙasa zai ci gaba da fuskantar matsaloli sakamakon gazawar gwamnati wajen gyara wani muhimmin layin lantarki a arewacin Najeriya saboda rashin tsaro da ake fama da shi.
Ministan wutar Lantarki, Adebayo Adelabu ne ya bayyana haka, yayin da ya ke magana a zaman kare kasafin kuɗin 2025 a gaban kwamitin haɗin gwiwa na Majalisar Dattawa kan wutar lantarki.
Adelabu ya bayyana tasirin layin Shiroro-Kaduna-Mando da ya lalace, wanda ba ya aiki tun bayan lalata shi da aka yi a watan Oktoban 2024. Wannan gazawar ta sanya matsin lamba sosai a kan babban layin, wanda ke haifar da faɗuwarsa akai-akai.
Ministan ya jaddada cewa yayin da ake ganin layin lantarkin zai ci gaba da faɗuwa, gwamnati ta mai da hankali kan rage yawan afkuwar hakan.
Ministan ya kuma bayyana shirin amfani da kuɗin da suka kai Naira biliyan 36 wajen rabon taransfoma a ɓangarori daban-daban na ƙasar.
Amincewa da tsagaita wuta tamkar "miƙa wuya" ga Hamas ne - Ministocin Netanyahu
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Ben Gvir yana alfaharari da kawo tsaiko ga yunƙurin tsagaita wuta a Gaza
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu yana fuskantar barazana daga wasu jami'an gwamnatinsa masu tsatstsauran ra'ayi, inda suke cewa za su yi murabus saboda a cewarsu amincewa da tsagaita wuta tamkar "miƙa wuya" ne da Hamas.
A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa, ministan tsaron cikin gida na ƙasar, Ben Gvir, ya ce amincewa da yarjejeniyar "zai goge nasarorin da aka samu a yaƙin."
Ben Gvir ya yi kira ga Netanyahu ya hana kayayyakin agaji da ruwa da fetur daga shiga Gaza, sannan ya cigaba da yaƙi har sai an tarwatsa Hamas baki ɗaya.
Ministan ya yi alfaharin hana cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a cikin shekarar da ta gabata ta hanyar matsin lamba na siyasa.
Wani ɗan majalisar ministocin ƙasar, ministan kuɗi Bezalel Smotrich, ya kira yarjejeniyar da za a yi a matsayin wani bala'i ga tsaron ƙasar Isra'ila, ya kuma yi kira da a ci gaba da mamaye Gaza har sai an fatattaki Hamas tare da mayar da mutanen da aka yi garkuwa da su.
Idan jam'iyyun waɗannan ministocin biyu suka janye daga kawancen, hakan zai sanya gwamnatin Netanyahu ta kasance ta marasa rinjaye za kuma ta fuskancirugujewa ta hanyar jefa kuri'ar rashin amincewa.
Amurka ta ce an tsara sabon daftarin yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza
Asalin hoton, Reuters
Amurka ta ce ana daf da amincewa da wasu ɓangarorin yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da ake ta kai-komo a kai.
Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Jake Sullivan, ya shaidawa manema labarai cewa tattaunawar da ake yi tsakanin Isra'ila da Hamas ta shiga wani muhimmin mataki, kuma ɓangarorin biyu, inda ya ce ana daf da ƙulla yarjejeniya.
An bayar da rahoton cewa, masu shiga tsakani na Isra'ila da Hamas sun karɓi wani sabon daftarin yarjejeniya a jiya Litinin, kuma za su sake haɗuwa yau a Doha, gemu da gemu don ƙarƙarewa.
Wakilin BBC ya ce yarjejeniyar ta yi bayanin cewa ƙarin taimakon jin ƙai zai fara shiga nan take, kana dakarun Isra'ila za su fice daga yankunan da ke da yawan jama'a, kuma za su saki fursunonin Falasɗinawa dubu guda.
Afirka ta Tsakiya ta naɗa Song a matsayin kocin ƙasarta
Asalin hoton, Getty Images
Tsohon kyaftin ɗin tawagar ƙasar Kamaru, Rigobert Song, ya zama sabon kocin tawagar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, kamar yadda ma'aikatar wasannin ƙasar ta bayyana.
Tsohon ɗanwasan mai shekara 48, wanda ya yi tashe a matsayin ɗanwasan baya, ya wakilci ƙasar Kamaru a gasan cin kofin duniya guda huɗu, sannan shi ne ya horar da tawagar ƙasar Kamaru a gasar cin kofin duniya da aka yi a Qatar a shekarar 2022.
Yanzu abin da ke gabansa shi ne wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya tsakanin Madagascar da Mali a watan Maris.
Ƙasar ce ta shida a teburin I da maki huɗu.
Song ya taka leda a ƙungiyoyin Liverpool da West Ham United da Racing Lens da Galatasaray.
A gasar cin kofin duniya da aka buga a Qatar, ya samu saɓani mai zafi da golan Manchester United Onana, wanda ya sa mai tsaron gidan ya bar gasar ana tsaka da fafatawa.
Nahiyar Afirka za ta iya riƙe kanta da kanta — Tinubu
Asalin hoton, Bola Ahmed Tinubu/X
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu na Najeriya ya ce nahiyar Afirka na da duk abin da ake buƙata domin riƙe kanta da kanta.
Tinubu ya bayyana haka ne a birnin Abu Dhabi na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a ranar Litinin lokacin da yake ganawa da Shugaban Ƙasar Rwanda, Paul Kagame.
Tinubu ya wallafa a shafinsa na X cewa, "a yammacin yau a makon taron ci gaba na Abu Dhabi, na samu ganawa da Shugaban Ƙasar Rwanda, Paul Kagame.
"Nahiyar Afirka na da duk abin da ake buƙata domin ciyar da kanta gaba. Muna da ɗimbin arziki da mutane da ƙwarewa. Dole mu yi nazari a tsakaninmu domin inganta hanyoyin kasuwancin ƙasashen Afirka domin amfanin nahiyarmu da mutane. Yanzu ne lokacin da Afrka za ta dara."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Ƴan fansho a Nijar sun koka kan rashin biyansu haƙƙoƙinsu
Asalin hoton, ORTN
A jamhuriyar Nijar ƙungiyar ƙwadago ta ma’aikatan da suka yi ritaya ce ta koka kan yadda ƴan fansho ke fuskantar matsaloli a wajen biyansu kuɗin fansho.
Ƙungiyar ta ce tun lokacin da aka ƙirƙiro bincike kan waɗanda suka yi ritaya da dama daga cikin su daina samun fansho.
Sakataren ƙungiyar ƴan fansho na ƙasar, Mahamadou Moussa, ya ce akwai waɗanda suka yi sama da wata 10 ba tare da sun samu kuɗin fansho ba.
Rasha na tursasa ƴan uwan fursunonin yaƙin da ta kama suna mata leƙen asiri - Ukraine
Asalin hoton, EPA
Jami'an Ukraine sun ce Rasha na amfani da fursunonin yaƙin da take tsare da su wajen tursasawa ƴan uwansu da ke gida cin amanar ƙasarsu ta hanyar kai hare-haren zagon ƙasa.
Kyiv ta ce an tuntuɓi kusan rabin iyalan dakarun Ukraine waɗanda yanzu haka ake tsare da su.
Ana zargin cewa ana amfan da ƙarfi da kuma barazana kan fursunonin yaƙin da kuma ƴan uwansu don tursasa masu yin wani abu idan suna son a saki ƴan uwansu.
An faɗa musu cewa za a azabtar da ƴan uwansu ko ma a kashe su, idan suka ƙi yin ƙone-ƙone ko leƙen asiri ga Rasha, amma za a iya sakinsu su da wuri idan suka amince suka yi hakan.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Rasha ta musanta wannan zargi.
An lalata mutum-mutumin tsohon Shugaban Ƙasar Ghana Akufo-Addo
Asalin hoton, Citi Newsroom
Mutum-mutumin tsohon Shugaban Ƙasar Ghana, wanda ya ƙaddamar a ƙarshen shekarar da ta gabata ya gamu da fushin al'ummar ƙasar.
Ƙaddamar da mutum-mutumin a ƙarshen zangon mulkinsa ya haifar da ce-ce-ku-ce da suka inda wasu ƴan ƙasar ta Ghana ke cewa hakan na nufin yabon kai.
Sai dai wasu na ganin mutum-mutumin alama ce ta nuna irin gudummawar da Akufo-Addo ya bayar ga ci gaban Ghana.Tun a wancan lokacin ne aka fara harin lalata mutum-mutumin, inda ƴansanda suka ce suna ƙoƙarin kama waɗanda ke da hannu tare da yi masu hukunci dai-dai da abin da suka aikata.
Sai dai a jiya Litinin, wasu kafofin sadarwa sun nuna hutunan yadda aka lalata mutum-mutumin, da kansa a ƙasa.
A makon jiya ne Akufo-Addo ya sauka daga mulkin ƙasar, bayan ya yi zango biyu.
Mutum biyu na ikirarin zama sakataren PDP na ƙasa
Asalin hoton, PDP
A Najeriya, bisa dukkan alamu rikicin babbar jam’iyyar hamayya ta PDP ya ɗauki sabon salo bayan da a wannan karon ake tirka-tirka tsakanin mutum biyu inda kowannensu ke ikirarin cewa shi ne halastaccen sakataren jam’iyyar.
Rahotanni na cewa a baya-bayan nan wata kotun ɗaukaka ƙara ta ce Sunday Ude-Okoye shi ne sahihin sakataren jam’iyyar na ƙasa, amma wanda yake kai ya ce ba zai sauka ba.
Lamarin ne ya janyo ruɗani a shalkwatar jam’iyyar a ranar Litinin.
Wannan wata sabuwar rigima ce da ta fito, cikin rigingimun da suka dabaibaye jam'iyyar.
'Fursunonin da ke jiran shari'a a Najeriya sun kai 48,932'
Asalin hoton, OTHER
Hukumar kula da gidajen yari ta Najeriya ta yi kiran a samar da tsari mai kyau da zai rage yawan cunkoso a gidajen yarin ƙasar, inda yanzu haka yawan fursunonin da ke jiran shari’a ya kai 48,932.
Da yake jawabi a wani taron tattaunawa da jami’an hukumar a ranar Litinin, muƙaddashin shugaban hukumar kula da gidajen yarin ta Najeriya, Sylvester Nwakuche, ya ce cunkoson da ake fama da shi a gidajen yarin ƙasar ya zama babbar barazana ga aikin su.
CSC Musbahu Lawan Ƙofar Nasarawa, shi ne kakakin hukumar gidan yarin reshen jihar Kano, ya ce lallai gidan yarin suna cikin wani hali, inda ya ƙara da cewa akwai buƙatar a samar da tsari mai kyau domin rage cunkosun.
An kama waɗanda ake zargi da sace-sace a gidajen da gobara ta illata a Los Angeles
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Masu kashe gobara
Ƴansanda a jihar Los Angeles na cigaba da kama waɗanda suke fasa gidajen da gobara ta illata a Los Angeles suna wawushe kayayyaki.
Tun bayan da gobarar ta yi ƙamari ne aka samu rahoton wasu ɓatagari na amfani damar wajen satar kayayyakin mutanen da suka tsere.
Zuwa jiya Litinin, an ƴansanda sun kama aƙalla mutum tara bisa zargin sata da kuma wani wanda ake zargi da rura wutar.
Ƴansandan Los Angeles sun wallafa wani bidiyo, inda a ciki aka nuna sun kama wani wani mutum a cikin wani gida, sannan an kama wanda ake zargi da ƙara rura wutar.
Nathan Hochman, shi ne babban lauyan gundumar ta L.A. ya ce "idan burinka shi ne fakewa da wannan bala'i don cimma wata manufa ta son rai, to za mu kama ka, mu gurfanar da kai don yanke maka hukunci daidai da rashin imaninka."