Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zafin cin Barca, ya sa Madrid fara tunanin maye gurbin Ancelloti, AC Milan na son Rashford
Manchester United za ta iya karbar tayin Alejandro Garnacho, Bayern Munich na son Kobbie Mainoo, Manchester City na son barin Kyle Walker ya bar kungiyar a kyauta...
An ce Manchester United za ta sa farashin dan wasan gefenta Alejandro Garnacho, mai shekara 20, a kan fan miliyan 42, yayin da Napoli ke zawarcinsa. (Sport Italia)
Bayern Munich ta bi sahun Chelsea wajen neman dan wasan Manchester United da Ingila Kobbie Mainoo mai shekaru 19. (Sun)
Manchester City na son barin dan wasan bayanta Kyle Walker, mai shekara 34, ya tafi kyauta a wannan watan, sakamakon zawarcinsa AC Milan da Inter Milan ke yi. (Gazzetta dello Sport)
AC Milan za ta nemi dan wasan gaban Manchester United Marcus Rashford, mai shekara 27, wanda ke shirin barin Old Trafford a wannan watan. (Sky Sports)
Borussia Dortmund kuma rahotanni sun ce sun gana da wakilan Rashford da fatan kulla yarjejeniya a watan Janairu. (Sky Sport )
Aston Villa ta amince da yarjejeniyar £19m don siyan dan wasan gaban Holland Donyell Malen, mai shekara 25, daga Borussia Dortmund. (The Athletic )
Villa ta kuma fara tattaunawa da Sevilla yayin da take neman dauko dan wasan bayan Faransa Loic Bade mai shekaru 24. (L'Equipe )
Leicester na shirin dauko dan wasan bayan Faransa Woyo Coulibaly, mai shekara 25, daga Parma kan kudi fan miliyan uku. (Fabrizio Romano)
Chelsea za ta bar dan wasan tsakiyarta Carney Chukwuemeka, mai shekara 21, ya tafi aro a wannan watan, yayin da Borussia Dortmund da Strasbourg ke son daukarsa. (Fabrizio Romano)
Dan wasan bayan Portugal Renato Veiga, mai shekara 21, da alama zai bar Chelsea a watan Janairu, inda kungiyoyi a Ingila, Jamus, Faransa da Italiya suka nuna sha'awarsu. (Athletic)
Dan wasan baya na Netherlands Tyrell Malacia, mai shekara 25, zai iya barin Manchester United a matsayin aro a wannan watan. (Fabrizio Romano)
Real Madrid ta fara tunanin wanda zai maye gurbin kocinta Carlo Ancelotti bayan ta sha kashi a hannun Barcelona da ci 5-2 a wasan karshe na cin kofin Spanish Super Cup. (Relevo)