Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 14/01/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Ibrahim Muhammad da Isiyaku Muhammed

  1. Gwamnatin Borno ta buƙaci mutane su daina ƙetare wuraren da sojoji ke sintiri

    Gwamnatin jihar Borno ta buƙaci al’umma su kaucewa tsallake iyakokin da sojoji suka shata don kaucewa faɗawa tarkon ƙungiyar Boko Haram.

    Gwamantin dai ta yin ƙarin bayani ne bayan wani hari da ƴan boko haram suka kai A ranar Lahadi, kan masunta da manoma a wani ƙauye da ke Baga a ƙaramar hukumar Kukawa.

    Kwamishinan yaɗa labaran jihar ta Borno Usman Tar ya shaidawa BBC cewar manoman sun faɗa tarkon maharan ne lokacin da suka tsallake yankunan da ke da tsaro, zuwa yankunan da babu tsaro.

    Ya ce tsallake iyakar ne ya ba maharan damar kai musu farmaki.

  2. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Talata daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu kawo labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sadarwa irin su X da Facebook da Instagram domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo.

    Ku kasance tare da mu