Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 22/11/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya. 22/11/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Abdullahi Bello da Isiyaku Muhammed

  1. Kashi biyu cikin uku na gidajen Najeriya ba su samun lafiyayyen abinci - NBS

    Hukumar ƙididdiga ta Najeriya NBS ta ce wani bincike da ta gudanar ya gano cewa rashin wadata ya sa kashi biyu cikin uku na gidaje a Najeriya ba su iya samun lafiyayyen abinci mai ɗauke da ingantattun sinadarai.

    Binciken da hukumar ta gudanar ya mayar da hankali ne kan ƙaruwar talauci a tsakanin gidajen ƙasar da irin tasirin da hakan ke yi wajen raguwar sayen abubuwa da 'yan ƙasar suka yi sakamakon tashin farashinsu.

    “Kusan kashi biyu cikin uku na gidajen Najeriya ba su iya cin lafiyayyen abinci mai ɗauke da sinadarai ko su dafa abinci saboda rashin wadata da suke fama da shi'', kamar yadda rahoton binciken ya nuna.

    Haka kuma binciken ya gano cewa kashi 63.8 cikin 100 na gidajen ƙasar na cin abincin ɗan kaɗan saboda rashin kuɗi, yayin da kashi 62.4 na gidajen ke cikin fargabar rashin samun wadataccen abinci, sannan kuma kashi 60.5 cikin 100 na gidajen ba sa iya cin abincin da ya kamata a ce suna ci.

    Rahoton binciken na zuwa ne ƙasa da wata guda bayan da wani rahoto da gwamnatin Najeriya ta fitar tare da tallafin Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa 'yan ƙasar fiye da miliyan 33 za su fuskanci matsalar ƙarancin abinci a 2025.

  2. PDP ta ɗage babban taron shugabanninta na ƙasa

    Babbar jam'yyar hamayya ta PDP a Najeriya, ta sanar da ɗage babban taron shugabaninta a ƙasa karo na 99 da ta shirya gudanarwa ranar 28 ga watan Nuwamban da muke ciki.

    Cikin wata sanarwa da babban sakataren jam'iyyar na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu ya fitar ranar Alhamis, ya ce an ɗage taron shugabannin jam'iyyar karo na 99 saboda jana'izar mai ɗakin gwamnan jihar Akwa Ibom, Patience Umo Eno da za a yi.

    Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da jam'iyya, ke samun saɓani da rikice-rikice tsakanin 'ya'yanta.

    Tun bayan da wata kotu ta sanar da cire shugaban jam'iyyar na ƙasa, Sanata Iyorchia Ayu a 2023, jam'iyyar ta sanar da naɗa Ilya Damagum a matsayin shugabanta na riƙo.

    To sai dai shi ma Damagun ya riƙa fuskantar suka daga wasu 'ya'yan jam'iyyar - waɗanda suka riƙa kiraye-kirayen ya sauya daga muƙamin.

    A taronsu karo na 98 da suka gudanar cikin watan Afrilu, shugabannin jam'iyyar sun amince da kafa kwamitocin sasanto da na ladabtarwa da shirya tarukan jam'iyyar tun daga matakin mazaɓu zuwa jihohi.

  3. Kotun ɗaukaka ƙara ta soke hukuncin kotun tarayya kan zaɓen ƙananan hukumomin Rivers

    Kotun ɗaukaka ƙara a Abuja ta soke hukuncin babbar kotun tarayya da ke Abujar, wadda ta hana hukumar zaɓen ƙasar, INEC bai wa hukumar zaɓen jihar Rivers rajistar masu zaɓe, a zaɓen ƙananan hukumomin jihar da aka gudanar.

    Yayin yanke hukuncin tawagar alƙalan kotun ɗaukaka ƙarar, ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Onyekachi Otisi, ta ce babbar kotun tarayyar ba ta da hurumin sauraron ƙarar, saboda da a cewar alƙalan sashe na 28 na dokar zaɓen ƙasar bai shafi zaɓukan da jihohi za su shirya ba.

    Alƙalan sun ce sashen na magana ne kawai kan zaɓukan tarayya da na gwamnoni da kuma na ƙananan hukumomin Abuja.

    Kotun ɗaukaka ƙarar ta ce babbar kotun tarayyar ta yi kuskuren hana jami'a tsaro shiga zaɓen domin samar da tsaro a lokacin zaɓukan.

    Gabanin zaɓen ƙananan hukumomin jihar Rivers da aka gabatar ranar 5 ga watan Oktoba, babbar kotun tarayyar da ke Abuja ta yanke hukuncin hana hukumar zaɓe ta ƙasa INEC bai wa hukumar zaɓen jihar rajistar da ke ɗauke da sunayen masu zaɓe.

    Yayin yanke hukuncin alalin kotun, Mai shari'a Peter Lifu ya ce hukumar zaɓen Rivers ta saɓa dokar zaɓukan ƙananan hukumomi, saboda gaza wallafa sanarwar saka ranar zaɓen wata uku kafin ranar zaɓen.

    Alƙalin ya kuma haramta wa jami'an tsaro shiga a dama da su domin su wanzar da tsaro a lokacin zaɓukan.

    Wani abu da wasu ke alaƙantawa da haifar da hargitsin da aka samu a jihar bayan bayyana sakamakon zaɓukan.

  4. Sammacin kotun ICC na kama Netanyahu abin takaici ne - Biden

    Shugaba Joe Biden na Amurka ya kira sammacin kama firaministan Isra'ila da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta ba da da abin takaici.

    ICC ta ce ta bayar da sammacin Benyamin Netanyahu kan zargin aikata laifukan yaƙi a Gaza.

    Tuni 'yan siyasa a Isra'ila suka fara martani kan hukuncin, ciki har da tsohon firaministan ƙasar, Naftali Benneth, wanda ya ce an ''gina ilahirin sammacin a kan ƙarya'',

    ''Wannan abin dariya ne ma, za mu maida martani, ba za mu zuba ido haka nan a cuce mu ba'', in ji Mista Benneth.

    Da wannan sammacin na kotun ICC ƙasashe mambobin kotun na da damar kamawa tare da tsare Mista Netanyahu idan ya shiga ƙasashensu.

  5. 'Rasha ta sayar wa Koriya ta Arewa ɗanyen mai ganga miliyan guda'

    Hotunan tauraron ɗan'dam da BBC ta samu sun nuna Rasha ta sayar wa Koriya ta Arewa ɗanyen mai da ya kai ganga miliyan daya, tun cikin watan Maris da ya wuce.

    Hakan na zuwa na zuwa ne a daidai lokacin da Koriya ta Arewar ke aika wa Rasha makamai da sojoji a yaƙin da take yi da Ukraine.

    Masu bincike sun shafe wata takwas suna bibiyar yadda tankokin mai na Koriya ta Arewa ke zuruftu a yankin da rijiyoyin man Rasha suke a yammacin ƙasar.

    Masu binciken na cibiyar Open Source mai mazauni a Birtaniya sun ce tankokin sun yi zirga-zirga sama da sau 40.

  6. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar Juma'a Haji babbar rana, kamar yadda Hausawa ke yi mata kirari.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a wannan lokaci domin kawo muku iri wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Kuna kuma iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa da kuma kallon bidiyo da hotuna