Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me dokokin Najeriya suka ce game da kama mabarata?
A ranar Alhamis ne wata babbar kotun tarayya ta sanya ranar fara sauraron wata ƙara da wani lauya mai rajin kare haƙƙin ɗan'adam ya shigar inda yake ƙalubalantar matakin kama mabarata a Abuja, babban birnin ƙasar.
Barista Abba Hikima wani lauya mai zaman kansa a birnin Kani ya shigar da ministan Abuja, Nyesom Wike ƙara a gaban kotun ranar Laraba bisa zargin muzguna wa mabarata da masu ƙananan sana'o'i a babban birnin ƙasar.
A makonnin baya ne, ministan na Abuja Nyesom Wike ya ƙaddamar da matakin kama mabarata waɗanda ya ce sun cika titunan Abuja, har ma sun zama barazana ga tsaron birnin, kuma suna zubar da mutuncin Najeriya a idon baƙi da ke ziyartar ƙasar.
'Dalilin da ya sa na kai Wike kotu'
Barista Abba Hikima ya ce ya je birnin Abuja domin gudanar da wani abu daban sai kawai ya shaida yadda jami'an kwamitin hadin gwiwa na tsaftace Abuja daga bara ke far wa jama'a.
Yayin ƙaddamar wani aikin titi a Unguwar Katamfe cikin watan Oktoban, Mista Wike ya ce sannu a hankali mabaratan na mayar da birnin Abuja cibiyar mabarata.
“Bari na bayyana muku ƙarara cewa mun ƙaddamar da kamen mabarata, suna neman mayar da birnin Abuja, cibiyar mabarata. Idan ka san kana da 'yan'uwan da e bara a Abuja, ku hana su, domin za mu kama su, Abin kunya ne idan muka yi baki, abin da za su fara gani shi ne mabarata a kan titi'', in Nyesom Wike.
To amma Abba Hikima ya ce duk da cewa bara ba abun so ba ne, amma bai ji daɗin yadda kame ya rutsa da mutanen da ba mabarata ba.
Lauyan ya kuma zargi masu kama mabaratan, da kama mutane masu ƙananan sana'o'i da masu ƙaramin ƙarfi.
''A gaban idona ankama masu sayar da abinci, an kama masu sayar da kayan tireda da masu sayar da ayaba da lemo, kuma abin takaici ma jami'an tsaron sun riƙa cin ayaba da lemon mutumin da suka kaman'', kamar yadda ya shaida wa BBC.
Abba Hikima ya ce wannan mataki da ministan ya ɗauka ya saɓa wa dokokin Najeriya, saboda yadda ya ce ana azabtar da su a lokacin kamun da kuma inda ake ajiye su bayan kama su.
Wannan batu dai ya janyo saɓanin ra'ayi tsakanin lauyoyi da masana shari'a a faɗin ƙasar, inda wasu ke ganin matakin ministan na kan ƙa'ida, yayin da wasu kuma ke ganin matakin nasa ya saɓa wa doka.
Mene ne ra'ayin lauyoyi?
Kan lauyoyi ya rabu dangane da halascin ko haramcin umarnin ministan na kama mabaratan.
Barista Sanusi Musa SAN ya ce dokokin Najeriya sun haramta yin barace-barace, kan haka ne ma ya ce bai ga baiken ministan na Abuja ba, kan wannan mataki.
Babban lauyan ya ce akwai dokokin da dama da suka haramta barace-barace a Najeriya.
''Alal misali kundin Penal Code wanda ya shafi duka jihohin arewacin Najeriya, wanda Abuja tana ciki ya tanadi hakan, idan ka duba sashe na 186 na wannan kundi ya haramta bara tare da mayar da shi laifi'', in ji shi.
''Haka ma akwai dokar kare haƙƙin yara, ita ma ƙarara ta haramta yin bara da ƙananan yara, ko amfani da su wajen yin bara, sannan akwai dokar kare haƙƙin masu nakasa, ita ma ta haramta amfani da naƙasassu ko wata nakasa wajen yin bara'', in ji lauyan.
Ya ƙara da cewa indai magana ake yi ta dokar da Wike ya saka to tana kan tsarin doka.
Babban lauyan ya kuma koka yadda ake amfani da ƙananan yara wajen barace-barace musamman a birnin Abuja .
''Abin akwai tashin hankali da tausayi, ƙarfe 11 na dare idan ka taho da mota sai ka ga yara ƙanana ana bara da su a kan tituna, akwai inda na taba zuwa na ga matan Hausawa na kwana a ƙofar Club tare da 'ya'yansu 'yan mata, saboda su yi wa masu zuwa Club ɗin bara'', in ji shi.
Masu adawa da matakin
Barista Abba Hikima Fagge - wanda shi ne ya gabatar da ƙarar ya ce abin da dokokin Najeriya suka haramta shi ne bara a kan tituna, amma a wannan umrnin ministan ana bin mutanen har lungu da sakuna ana kamasu.
Lauyan ya ce sashe na 41 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa kowane ɗan ƙasar damar su je duk inda suke so a faɗin ƙasar domi su zauna ba tae da izinin kowa ba.
''Haka kuma sashe na 35 ya ce kowane ɗan Najeriya na da damar yin tafiyarsa, in mutum ya ga dama ya yi tafiya a kan titi ko ya kwana a kan titi, duk wannan ba laifi ba ne'', in ji lauyan.
Barista El-Zubair Abubakar wani lauya ne mai zaman kansa a ƙasar, shi ma ya ce babu wata doka a Najeriya da ta haramta barace-barace a faɗin ƙasar.
Amma ya ce akwai kiraye-kirayen da jami'an gwamnati da wasu hukumomin ƙasar ke yi na cewa a daina barace-barace, saboda ba abu ne mai kyau ba.
Lauyan ya kuma ce a baya an samu wasu jihohin da suka haramta bara, kamar Kaduna da Kano da Plateau, amma a cewarsa a yanzu dokokin ba sa aiki.
Barista El-Zubair ya ce a matakin ƙasa, majalisar Najeriya ba ta yi wata doka da ta haramta bara ba.
''Sai dai a yi ta jan hanakalin mutane da cewa su daina yin bara, inda har aka kafa Task Force, da ke hana bara, waɗanda kuma ba dokoki ba ne, sai ai mu ce musu 'Rules, saboda ba majalisa ce ta yi ba, dokoki ne da mahukunta ke yi don tsaftace birnin Abuja, amma babu wata doka tsayayyiya da ta haramta bara a Najeriya", in ji Barista El-Zubair.
Don haka ne ma yake ganin kama mabaratan da ake yi a Abuja ya saɓa wa doka, saboda babu wani laifi da suka yi da ya saɓa wa dokar gwamnatin tarayya.
Lauyan ya ce idan ana so a kama mabaratan sai a kai ƙudurin dokar zuwa majalaisar dokokin ƙasar domin ta zama doka.
''A kai ƙudirin dokar zuwa majalisa, sannan 'yan majalsa su yi muharawa a kai har zuwa matakan da ake bi wajen tabbatar da ƙuduri ya zama doka, sannan shugaban ƙasa ya sanya hannu, daga nan ya zama doka, sai a kama mabarata sabda sun saɓa wa doka'', in ji shi.