Rufewa
A nan muka kawo ƙarshen wannan shafin na yau.
Sai kuma gobe idan Allah ya nuna mana.
Mu kwana lafiya
Wannnan Shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Haruna Ibrahim Kakangi da Ibrahim Yusuf Mohammed da Abdullahi Bello Diginza
A nan muka kawo ƙarshen wannan shafin na yau.
Sai kuma gobe idan Allah ya nuna mana.
Mu kwana lafiya

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce tattaunawar da aka yi a Paris domin kawo ƙarshen yaƙin Ukraine na da matuƙar muhimmanci kuma abu ne da kowa ya yarda da ita.
Shugaban ya yi jawabin ne bayan ganawar da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio da kuma jakadan Amurka na musamman Steve Witkoff, inda suka zauna tare da wasu wakilan Ukraine da na ƙasashen tarayyar Turai da ke goyon bayan Ukraine.
To sai dai kuma Mr Macron bai bayar da cikakken bayani a game da yadda za a cimma yarjejeniyar zaman lafiyar ba.
Steve Witkoff, ya je Paris ne bayan tattaunawa da shugaban Rasha Vladimir Putin. Da yake magana da BBC, wani ɗan majalisar Ukraine Vadym Halaichuk, ya ce yana fatan ƙasashn Turai za su yi duk mai yiwuwa wajen ganin an kawo ƙarshen yaƙin da ƙasashen suke yi.
Ya ce "abin takaici ba mu ga Rasha na ɗaukar wannan batu da muhimmanci ba, sannan ita kanta Amurka ba ta wani ƙoƙari take yi ba wajen ganin ta matsa wa Rasha lamba kan tsagaita wuta da kuma cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Ukraine."
Amurka da Somaliya sun kai wani hari ta sama kan masu kishin Islama a yaƙin da suke yi a ƙoƙarin ƙwace wani gari mai muhimmanci a tsakiyar ƙasar, in ji gwamnatin ƙasar.
Harin da aka kai kan Adan-Yabaal da ke arewacin Mogadishu babban birnin ƙasar, ya zo ne sa'o'i bayan da al-Shabab ta kai farmaki kan garin da ke matsayin babbar matattarar ƙaddamar da hare-haren soji.
A wata sanarwa da ma'aikatar watsa labaran Somaliya ta fitar ta shafin X, ta ce daga cikin ƴan ta'adda 12 da aka kashe a harin ta sama, akwai wasu manyan mayaƙa daga ƙungiyar al-Qaeda.

Asalin hoton, TCN
Ministan Makamashi na Najeriya, Adedayo Adelabu ya ce aƙalla ƴan Najeriya miliyan 150 ne suke samun wutar lantarki, inda a cewarsa, sauran mutanen kusan miliyan 80 suke cigaba da fama da rashin wutar.
Ministan ya bayyana haka ne a ranar Alhamis lokacin da yake jawabi a taron ƙara wa juna sani kan ayyukan ministoci a Abuja, inda ya yi jawabi a tare da ministan yaɗa labarai, Mohammed Malagi da sauran masu ruwa da tsaki.
Adelabu ya ce Najeriya ta samu wannan nasarar ce bayan ta samu shiga tsarin “Mission 300” wanda bankin duniya da bankin raya yankin Afirka suka tsara domin ganin aƙalla ƴan Afirka miliyan 300 suna samun wutar lantarki zuwa ƙarshen shekarar 2030.
Ya ce, "ina farin cikin bayyana muku cewa daga cikin ƴan Afirka miliyan 300 da bankin duniya da bankin raya yankin Afirka suka tsara samar wa wutar lantarki, Najeriya ce za ta ci moriyar kashi 25, wanda ke nufin kusan mutum miliyan 75," in ji shi kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.
Adelabu ya ce Najeriya mai kusan mutum miliyan 240, a yanzu haka aƙalla mutum miliyan 150 suna samun wutar lantarki.
"Babbar matsalar ita ce samun lantarki wadatacciya kuma mai rahusa. Da waɗannan ababen ne muke auna samun wutar. Dole ne mu tabbatar waɗanda suke samun lantarkin, suna samunta a-kai-a-kai, kuma suna samunta da rahusa," in ji shi.

Asalin hoton, BOKO HARAM
A jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, bayanai na nuna cewa akwai wasu yankunan na wasu ƙananan hukumomin jihar da ƙungiyar Boko Haram ko Iswap ke nuna ƙarfin iko.
A ƙarshen makon da ya gabata ne Sanata Ali Ndume, ɗan majalisar dattijai daga jihar Borno ya bayyana wa manema labarai a Abuja cewa ƙananan hukumomin jihar uku na cikin irin wannan hali a yanzu haka.
Ƙananan hukumomin sun haɗa da Gudumbari da Marte da kuma Abadam

Asalin hoton, Bayo Onanuga/Facebook
Shugaban Najeriya Bola Tinubu na gudanar da harkokin gwamnati duk kuwa da cewa yana ƙasashen turai.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar, inda a ciki ya ce tafiyar shugaban ta wani ɗan lokaci ne kawai.
"Tafiyar ta wani ɗan lokaci ne kuma tana kan tsarin wa'adin mako biyu. Shugaban ƙasar ya bar Paris ya tafi Landan a ƙarshen mako, amma duk da haka yana cigaba da tattaunawa da jami'an gwamnati, kuma bibiya tare lura da duk abubuwan da ke tafiya, ciki har da ba shugabannin tsaron ƙasar umarni su magance matsalar tsaron da ta kunno kai a wasu ɓangarorin ƙasar."
Sanarwar ta ƙara da cewa Tinubu zai koma Najeriya bayan hutun Easter, sannan ta ce zai cigaba da sauke nauyin da ya ɗauka, "gwamnati na cigaba da gudana ba tare da wata matsala ba a ƙarƙashin kulawarsa."

Asalin hoton, Getty Images
Aƙalla shanu 36 ne aka kashe, sannan wasu suke kwance suna shan magani bayan sun ci wani yalo da ake zargin an zuba a ranar Laraba a yankin garin Tafi Gana da ke ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Filato.
Jami'in hulɗa da jama'a na Ƙungiyar Miyetti Allah na ƙasa, Muhammad Nuru Abdullahi ne ya tabbatar da hakan a zantawarsa da BBC, inda ya ce dama ba yau aka saba kashe musu shanu da guba ba.
A cewarsa, "muna zargin wasu manoma ne suka sayo yalo suka zuba guba a ciki, sai suka ajiye shanu suka ci. Shanu 36 ne suka mutu, sannan muna ba sauran magani ba mu sani ba ko za su rayu."
Sai dai ya ce sun gamsu da matakan da jami'an tsaro suka ɗauka, "domin jami'an tsaro da suka haɗa da sojoji da ƴansanda sun same mu, sun kwantar mana da hankali kuma sun ce za su ɗauki mataki. Mun faɗa musu matsalolin da muke fuskanta, kuma sun faɗa mana irin matakan da za su ɗauka.
Ya ce ba sabon abu ne a Filato domin "ko a baya a Mangu kusan shanu 29 suka mutu a sanadiyar guba. Suna so ne su karya mana tattalin arzikimu."
A game da zargin shanun ne suke ɓarna a gonaki, sai Muhammad Nur ya ce ba haka ba ne, domin a cewarsa, "yanzu fa rani ake yi. Babu wata gonar da muka yi ɓarna, kawai da tattalin arzikinmu suka yaƙi."
Ya ƙara da cewa al'adarsu ba ta aminta da zalunci ba, "don haka idan dabbobi suka yi ɓarna mun amince mu biya saboda idan ba mu biya ba, dukiyar za ta lalace."

Asalin hoton, EPA
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yaƙin kasuwanci da ke tsakanin ƙasarsa da ƙasar China zai iya zuwa ƙarshe a nan gaba domin a cewarsa za su shiga maslaha mai kyau a nan gaba.
Da aka tambaye shi ko Amurka ta shiga damuwa ganin yadda ƙawayenta na kusa suke komawa ɓangaren China, sai Trump ya amsa da cewa, "ko kaɗan ba ya cikin damuwa."
Sai dai ya ƙara da cewa "Babu ƙasar da za ta iya jayayya da mu," in ji shi.
"Amma ina tunanin za mu shiga maslaha da yarjejeniya masu kyau da ƙasar China."

Asalin hoton, BOKO HARAM
A jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, bayanai na nuna cewa akwai wasu yankunan na wasu ƙananan hukumomin jihar da ƙungiyar Boko Haram ko Iswap ke nuna ƙarfin iko.
A ƙarshen makon da ya gabata ne Sanata Ali Ndume, ɗan majalisar dattijai daga jihar Borno ya bayyana wa manema labarai a Abuja cewa ƙananan hukumomin jihar uku na cikin irin wannan hali a yanzu haka.
Ƙananan hukumomin sun haɗa da Gudumbari da Marte da kuma Abadam.

Asalin hoton, Getty Images
Ƙasar Colombia ta ayyana dokar ta-baci a duk faɗin ƙasar bayan da aƙalla mutane 34 suka mutu sakamakon kamuwa da cutar zazzabin shawara, a cewar hukumomin lafiyar ƙasar.
Cutar dai na bazuwa ne ta hanyar ƙwayoyin cuta da sauro ke yaɗawa ga mutane.
Ana iya kaucewa kamuwa da ita ta hanyar allurar rigakafi wanda a mafi yawan lokuta ke ba da kariya na tsawon rayuwar mutum.
Gwamnati ta buƙaci mutane da su yi allurar rigakafin ƙafin karshen makon bukukuwan Easter, lokacin da yawancin ƴan Colombia ke tafiya zuwa wurare masu zafi inda sauro ke iya yaɗa cutar.
Ministan lafiya Guillermo Alfonso Jaramillo ya ce za a buƙaci waɗanda za su je wuraren da ke da haɗari su nuna shaidar rigakafin.
Ministan lafiyan ya ce an samu mutane 74 da aka tabbatar sun kamu da cutar a Colombia a cikin ƴan kwanakin nan, ya kuma buƙaci mutane da su yi allurar rigakafin, wanda kyauta ake yi a Colombia.

Asalin hoton, Reuters
Hukumar tsaron fararen hula ta Gaza, ta ce hare hare ta saman da Isra'ila ta kai a sassan yankin sun yi sanadin mutuwar akalla mutane 37.
Yawancin waɗanda aka kashe suna zaune ne sansanonin ƴan gudun hijira.
Wasu hare haren makamai masu linzami da Isra'ila ta kai a gaɓar ruwan Al Mawasi da ke kusa da kudancin birnin Khan Younis sun faɗa kan wasu tantunan da mutane ke zama a ciki.
Kazalika an kashe wasu iyalai mutum bakwai a arewacin birnin Jabalia.
Amande Bazuroll, jami'a a ƙungiyar likitoci ta Medicns Sans Frontiers ta bayyana cewa harin da aka kai ya faɗa ne a kusa da ofishin su da ke kudancin Gaza, inda tantuna da dama suka kama da wuta yayin da jami'an ƙungiyar suka yi ta kai-komo domin tallafawa waɗanda lamarin ya rutsa da su.
Isra'ila dai ta yi iƙirarin cewa ta koma kai hare harenta a kan Hamas ne domin tursasa musu sakin sauran mutanen da ta yi garkuwa da su a Gaza.

Asalin hoton, Rolling Narratives
Kotun ƙolin Rasha ta dakatar da haramcin da ta yi wa Taliban wanda ya buɗe kofar cire ta daga cikin jerin ƙungiyoyin ƴan ta'adda a duniya.
Amma yunƙurin ba ya na nufin a hukumance ta amince da ƙungiyar ba ne, amma abu ne da ke nuni da yadda ta ke son ta ƙarfafa alaƙa da ƙungiyar.
Rahotanni sun ce Rasha na shirin amfani da Afghanistan a matsayin hanyar da zata rika fitar da iskar gas dinta, sannan kuma shugaba Putin ya bayyana Taliban a matsayin ƙawaye a yaƙin da ake yi da ta'addanci.
A shekarun baya Rasha ta sha karɓar baƙuncin ƙungiyar Taliban a ƙasarta a yayin wasu taruka da suka gudanar tsakaninsu.

Asalin hoton, Getty Images
Amurka da Somalia sun kai wani hari ta sama kan masu iƙirarin jihadi a yaƙin da suke yi na ƙwace wani gari mai mahimmanci a tsakiyar ƙasar, in ji hukumomin gwamnati.
Harin da aka kai kan garin Adan Yabaal da ke arewacin Mogadishu babban birnin ƙasar, ya zo ne sa'o'i bayan mayaƙan Al-Shabab sun kai farmaki kan garin da ake amfani da shi a matsayin babban fagen ƙaddamar da hare-haren soji.
Wata sanarwa da ma'aikatar yaɗa labaran Somalia ta wallafa a shafinta na X, ta ce daga cikin ƴan ta'adda 12 da aka kashe a harin ta sama akwai wasu manyan mayaƙa daga ƙungiyar ta Al-Shabab da ke da alaƙa da ƙungiyar al-Qaeda.
Faɗan baya-bayan nan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake fargabar sake farfaɗowar ƙungiyoyin mayaƙa masu iƙirarin jihadi a Somalia bayan an samu ƙaruwar hare-haren ƴan bindiga, ciki har da wanda aka kai kan ayarin motocin shugaba Hassan Sheikh Mohamud a watan jiya.
Ƙungiyar Al-Shabab da ke riƙe da yankuna da dama da ke kudanci da kuma tsakiyar Somalia ta kwashe kusan shekaru 20 tana yaƙar gwamnati inda ta ke neman hamɓarar da gwamnatin tarayya ta kuma kafa daular musulunci.

Asalin hoton, Reuters
Wani mutum da jami'ai suka amince an tasa ƙeyarsa zuwa gidan yari a El Salvador 'bisa kuskure' ba zai sake rayuwa a Amurka ba, in ji fadar White House.
An tasa ƙeyar Kilmar Ábrego García ɗan ƙasar El-Salvador zuwa ƙasar ta sa ne da ke yankin Amurka ta tsakiya daga Maryland bayan an zarge shi da kasancewa memba na haramtacciyar ƙungiyar MS-13, zargin da lauyansa ya musanta.
Wani alƙali ya umarci gwamnatin shugaba Donald Trump da ta tabbatar da dawowar sa Amurka - amma shugaban El Salvador Nayib Bukele ya bayyana a farkon wannan makon cewa ba shi da "ikon" yin hakan.
A ranar Laraba, sakatariyar yaɗa labaran fadar White House, Karoline Leavitt, ta ƙara nanata zargin da ake yi wa Mista Ábrego García, na cewa shi ɗan haramtaciyar ƙungiyar ne, ta kuma zarge shi da kitsa tashin hankali.
Leavitt ta shaidawa taron manema labarai cewa: "Idan Mr Ábrego García ya sake dawowa Amurka, nan take za a sake tasa ƙeyarsa. "Ba zai sake zama a Amurka ba."

Asalin hoton, Reuters
Manyan ƴan siyasar Isra’ila sun yi kira da a kai hari kan cibiyoyin nukiliyar Iran, bayan wani rahoto da ba a tabbatar da shi ba daga Amurka ya ce Washington ta yi watsi da wannan shirin.
Tsohon ministan tsaro, Benny Gantz, ya bayyana shugabannin Tehran a matsayin "ƙwararru a dabarun jan ƙafa" kuma ya ce "dole ne Isra'ila ta kai hari kan Iran".
Da take ambato majiyoyin hukuma da ba a bayyana sunayensu ba, jaridar New York Times ta ce Isra'ila na son Amurka ta taimaka wajen aiwatar da wannan shirin kai harin a watan Mayu.
Amma a makon da ya gabata, shugaba Trump ya bayyana cewa Amurka na tunanin tattaunawa ne da Iran.
Za dai a ci gaba da tattaunawa kan lamarin a birnin Rome a ranar asabar mai zuwa.

Asalin hoton, Getty Images
Ƙugiyoyin Arsenal da Inter Milan da Barcelona da kuma Paris St-Germain sun samu gurbi a wasan kusa da na ƙarshe a Gasar Zakarun Turai.
Yanzu kuma tunani ya fara komawa kan ƙungiyar da za ta kafa tarihin lashe gasar, wadda ake sauya wa fasali.
A watan Mayu ne za a buga wasan ƙarshe a birnin Munich na ƙasar Jamus.
Tuni dai masana harkokin wasanni suka fara tsokaci kan ƙungiyar da suke ganin za ta iya lashe gasar ta bana.
Ga bayanai game da ƙungiyoyin huɗu da kuma hasashen masana wasanni kan lashe gasar.

Asalin hoton, AFP
Ministan tsaron Isra'ila ya ce sojojin ƙasar za su ci gaba da zama a wuraren da ake kira yankunan tsaro da suka kafa ta hanyar ƙwace manyan yankuna na Gaza ko da bayan kawo ƙarshen yaƙin.
Isreal Katz ya ce yankunan za su kasance wani mataki na kare al'ummomin Isra'ila "a kowane hali na wucin gadi ko na dindindin", kuma Isra'ila ta ƙara faɗaɗa yankin da ta ke iko da shi a Gaza tun lokacin da ta dawo da kai hare-hare makonni uku da suka gabata.
Ya ce Isra'ila za ta ci gaba da daƙile tallafin jin kai na tsawon makonni shida, domin matsa wa Hamas ta sako mutanen da ta yi garkuwa da su, duk da gargadin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi na "mummunan sakamako".
A ranar Laraba ƙungiyar Likitoci ta Médecins Sans Frontières (MSF) ta zama ƙungiyar ƙasa da ƙasa ta baya-bayan nan da ta yi kakkausar suka kan mummunar tasirin da yaƙin Isra'ila ke yi, tana mai cewa Gaza "ta zame wani wani babban kabari na Falasɗinawa da waɗanda ke zuwa taimaka mu su".
Ma'aikatar lafiya ta Gaza ta ce sama da mutane 1,650 aka kashe tun bayan sake ɓarkewar yaƙin a ranar 18 ga Maris.
Jami’an asibiti sun ce aƙalla Falasdinawa 24 ne aka kashe a hare-haren da Isra’ila ta kai a Gaza ranar Laraba.

Asalin hoton, Atiku Abubakar
Jagoran ƴan adawa a Najeriya, Atiku Abubakar ya bayyana ziyarar aiki da shugaban ƙasar Bola Tinubu ke yi a ƙasar Faransa a matsayin 'mummunan watsi da aikinsa' na shugaban ƙasa yayin da ƙasar ke fama da manyan ƙalubale.
Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya fitar ta hannun mai magana da yawunsa, Paul Ibe, wanda aka wallafa a shafinsa na X.
Hakan na zuwa ne yayin da ƴan adawa a Najeriyar ke ci gaba da sukar matakin da Bola Tinubu ya ɗauka na kasancewa a ƙasar Faransa duk kuwa da abubuwa na rashin tsaro da ke haifar da kashe-kashe a Najeriya.
A farkon watan Afrilu ne shugaban na Najeriya ya bar ƙasar zuwa Faransa domin gudanar da wata ziyarar aiki, kamar yadda fadar shugaban ƙasar ta sanar.
Sai dai tun bayan tafiyarsa an kai munanan hare-hare a jihar Filato, waɗanda suka yi sanadiyyar kashe fiye da mutum 100.
A cikin sanarwar da ya fitar, Atiku ya ce "wane dalili (Tinubu) ke da shi na ci gaba da karaɗe ƙasashen Turai bayan ana zubar da jini a Najeriya?
"Yayin da Tinubu ke cin gara a ƙasaitattun wurare, ƙasar da yake jagoranta ta faɗa tsundum cikin yamutsi," in ji Atiku.
Ya ƙara da cewa "idan har Tinubu na da tausayi, to ya kamata ya katse tafiyarsa ya koma gida ba tare da ɓata lokaci ba."
Hakan na zuwa ne jim kaɗan bayan sukar da ɗan takarar shugaban Najeriya a jam'iyyar LP, Peter Obi ya yi wa Tinubu kan tafiyar tasa zuwa Faransa yayin da ake samun hare-haren da ke haifar da asarar rayuka a ƙasar.
A sanarwar da fadar shugaban ƙasar ya fitar ta hannun mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga a ranar biyu ga watan Afrilu ya ce a lokkacin ziyarar ta Tinubu zuwa Faransa, "zai yi nazari kan ayyukan gwamnatinsa da kuma nasarorin da ya cimma.
Haka nan kuma zai yi amfani da lokacin wajen nazari kan sauye-sauyen da ya kawo sannan ya fara shirye-shirye kan bikin cikarsa shekaru biyu kan mulki."

Asalin hoton, Getty Images
Wakilin Donald Trump na musamman Steve Witkoff da babban jami'in diflomasiyya Marco Rubio za su tattauna da takwarorinsu na Turai a birnin Paris domin tattaunawa kan ƙoƙarin kawo ƙarshen yaƙin Ukraine.
Ministan harkokin wajen Ukraine da ministan tsaro sun isa babban birnin Faransa domin halartar tattaunawar.
Tattaunawar, wadda sakataren harkokin wajen Burtaniya David Lammy zai halarta, shi ne mafi girman matakin shiga tsakani kan yaƙin tun watan Fabrairu.
Jami'an diflomasiyyar Turai sun ce za su buƙaci Amurka da ta ƙara matsa wa Rasha lamba kan ta amince da tsagaita wuta ba tare da wani sharaɗi ba.
Wannan yunƙuri na tabbatar da tsagaita wuta na zuwa ne ƴan kwanaki kaɗan bayan harin makami mai linzami da Rasha ta kai ya kashe mutane aƙalla 35 tare da jikkata 117 a birnin Sumy na ƙasar Ukraine.
A farkon wannan watan, aƙalla mutane 18 ne suka mutu a wani harin da aka kai wata unguwa a Kryvyi Rih.
Da dadren ranar Laraba, hukumomin Ukraine sun ce harin da jiragen saman Rasha suka kai kan birnin Dnipro ya kashe mutane uku ciki har da wata ƙaramar yarinya.
Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce za a mai da hankali ne kan yadda za a kawo ƙarshen faɗan da ake yi a Ukraine, kuma Witkoff zai bayar da rahoto kan ganawarsa da shugaban Rasha Vladimir Putin a makon jiya.

Asalin hoton, NPF
Rundunar ƴansandan Najeriya ta ce za ta hukunta jami’anta da aka nuna suna ƙarbar kuɗaɗe daga hannun wasu ƴan ƙasar China a wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta.
A cikin bidiyon, an ga wasu ƴan ƙasar China suna rabawa wasu jerin jami'an ƴansanda kuɗi, lamarin dai ya janyo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta, inda ƴan Najeriya da dama ke nuna rashin jin daɗinsu tare da yin kira da a kawo sauyi kan yadda rundunar ke gundanar da ayyukanta.
A wata sanarwa da aka wallafa a shafin rundunar ƴansandan na dandalin X, kakakin rundunar Muyiwa Adejobi, ya yi Allah-wadai da halin jami’an, inda ya bayyana abin da suka yi a matsayin rashin da’a.
Ya ce, “Halayyar waɗannan jami’an ta saɓawa ƙa’idojin da’a, da muhimman dabi’u na rundunar ƴansandan Najeriya.''
Ya ƙara da cewa rundunar ta zuƙulo jami'an da lamarin ya shafa kuma ana shirin ɗaukar matakan ladabtarwa a kansu.
Ko da yake bai bayyana yanayin matakan da za a ɗauka kan ƴansanda ba, Adejobi ya tabbatar wa jama’a cewa za a yi adalci.
Rundunar ta kuma gargadi mutane da ƙungiyoyi masu amfani da ƴansanda, a matsayin masu rakiya da masu gadi da su kaucewa duk wani aiki da zai iya zubar da mutuncin jami’anta ko kuma janyo wa rundunar bacin suna.