Shin Trump ya juya baya ga tsarin tattalin arziƙi da Amurka ta ginu a kai?

Asalin hoton, Pool/BBC
Shugaba Donald Trump ya sake gina wata katanga, kuma yana tunanin kowa zai taimaka wajen tabbatar da ita.
Amma matakin da ya ɗauka na sanya harajin aƙalla kashi 10% a kan kusan duk wani nau'in kaya da ya shiga Amurka, mataki ne da aka tsara don ci gaba da samar da ayyukan yi a cikin Amurka, maimakon korar baƙin haure.
Wannan mataki ya zama irinsa na farko a tarihi tsawon ƙarni guda. Hakan zai taimaka wa Amurka zarce ƙasashen G7 da G 20 ta fannin tara haraji.
Abin da ya faru a makon nan ba wai kawai ta fara yaƙin cinikayya duniya ba ne, ko kuma rikita kasuwannin hannayen jari ba. Ita ce babbar ƙasa a duniya da ta juya baya ga tsarin dunƙulewar duniya da ta ɗauka , kuma daga nan ne ta sami riba mai yawa a cikin 'yan shekarun nan.
Kuma ta yin amfani da lissafin da ya dogara da babban kuɗin fito, Fadar White House ta kuma juya baya ga wasu muhimman abubuwan tattalin arziki na al'ada da diflomasiyya.

Asalin hoton, Getty Images
Babbar muhawarar kasuwanci maras shinge
Trump ya maganganu da dama kan 1913 a lokacin sanar da matakin ƙarin harajin.
Wannan wani sauyi ne lokacin da Amurka ta ƙirƙiri harajin kuɗin shiga na tarayya da kuma rage yawan kuɗin fito.
Kafin wannan lokaci, tun lokacin kafuwarta gwamnatin Amurka, galibi ta fi dogara ne kan kudin haraji.
Babban darasin da Fadar za ta iya koya daga wannan shi ne ƙarin harajin a matakin farko zai sa Amurka ''haɓaka'', sannan hakan na nufin za a rage buƙatar harajin tarayya.
'China ta kaɗu' kuma ta fara ji a jikinta
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Yayin da mataimakin shugaban Amurka, JD Vance ya faɗa cikin wani jawabi da ya gabatar a watan da ya gabata, ya ce gwamnatinsa na ganin an kasa cimma muradin dunƙulewar ƙasashen duniya, saboda manufar ita ce ''ƙasashe masu arziki sun fi samun ƙaruwar arziki, yayin da matalauta ke tafiyar hawainiya''.
Hakan bai taka kara ya karya ba, musamman game da ƙasar China, don haka Amurka ta yi nisa sosai daga wannan duniyar.
A 2001harin 11 ga watan Satumba ya kawar da hankalin duniya, lamarin da ya sa China ta shiga Ƙungiyar Cinikayya ta Duniya, WTO abin da ya sa ta samu damar shiga kasuwannin Amurka, tare da sauya safalin kasuwancin duniya.
Rayuwa da ci gaba da kasuwannin hannayen jari suka bunƙasa a Amurka, yayain da ayyukan china suka sauya daga yankunan karkara zuwa manyan kamfanonin biranen ƙasar domin sarrafa abubuwan da za fitar zuwa ƙasashen ƙetare musamman Amurka.
China ta samu tiriliyoyin daloli inda ta sake zuba jarin da dama daga cikinsu a Amurka , domin taimaka wa rage kuɗin ruwan da kamfanonin ƙasar ke biya.

Asalin hoton, .
Kowa ya amfana, kodayake ba daidai wa daida ba. Ainihin masu sayen kaya a Amurka sun wadata da kayayyaki masu rahusa, amma an samu raguwar masana'atu a Gabashin yankin Asiya.
Ƙididdigar da Autor ya yi a 2011, ta ''girgizar kasar China'' wadda ta nuna ta yi asarar ayyukan masana'antun Amurka miliyan daya, da kuma ayyuka miliyan 2.4 jimilla. Wannan ya ƙunshi yankin Rust Belt da Kudancin Asiya.
An ci gaba da fuskantar asarar ayyukan yi da albashi a ƙasar ta China.
A farkon wanna mkon ƙungiyoyin masu sayar da ƙananan motoci da ma'aikatan man fetur da iskar gas suka riƙa nuna murna kan ƙarin haraji a Fadar White House.
Alƙawarin a nan shi ne waɗannan ayyuka za a maido da su, ba wai ga Rust Belt (yankin da kamfanonin suka daina aiki ) ba har ma da faɗin Amurka.
Saƙon da da Trump ya aike wa kamfanonin ƙasashen waje shi ne idan suna son kauce wa tarin haraji to su koma Amurka.
Kamfanonin Amurka sun yi amfani da damar wajen samar da kayayyaki masu inganci da ke yaɗuwa zuwa China da Gabashin Asiya don samun riba mai gwaɓi, ta hanyar sayar da kayayyakin Amurka a ko'ina a duniya.
Wannan ya sa tattalin arzikin Amurka ya bunƙasa sosai. Matsalar, a sauƙaƙe, ita ce, ba a rarraba ta a tsakanin sassa. Kuma abin da Amurka ta rasa shi ne matakan sake rarrabawa da daidaitawa don yaɗa dukiyar a faɗin kasar. Wannan yana nuna zaɓin siyasar Amurka.
Yaƙin kasuwancin shafukan sada zumunta na farko

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu, yayin da Amurka ta zaɓi sake farfaɗo da masana'antu tare da kare ayyuka, wasu ƙasashe kuma suna da zaɓi game da ko za su goyi bayan kwararar jari da kasuwancin da suka sa Amurka ta kasance mai arziki.
Masu amfani da kayyaki a duniya na da zaɓi.
Ba abin mamaki ba ne manyan kamfanonin Amurka - waɗanda suka ginu a kan samar da kayayyaki masu inganci da rahusa zuwa gabashin Asiya suna sayarwa ga duniya baki ɗaya bisa kyawawan nau'ika - su samu babbar matsala.
Matsalar ta fi shafar hannayen jarinsu musamman saboda shugaban ya lalata dabarun samar da kayayyaki, sannan kuma akwai hatsarin zai cutar da kimar su a tsakanin masu siyar da kayayyaki na duniya.

Asalin hoton, Shutterstock
A taƙaice, wannan shi ne yaƙin kasuwanci na dandalin sada zumunta na farko. Batun karyewar kamfanin Tesla da koma bayan Kanada kan kayayyakin Amurka na iya zama mai illa. Wannan zai iya shafar sauran kamfanonin ƙasashen duniya.
Waɗannan ƙasashen da suka fara yin tarukan bita na masu amfani da kayyaki a Amurka suna da zaɓi a kan ciniki da kamfanonin da suke da muradi. Sabbin ƙawance za su ƙulla kuma za su ƙara ƙarfi domin neman yanke hulɗa da Amurka.
Manufar shugaban ta bayyana ne a lokacin da ya yi barazanar ƙara haraji idan EU da Canada suka haɗa kai wajen ɗaukar fansa. Wannan zai zama mataki mai ban tsoro.
A cikin ƙa'idar yaƙin kasuwanci, inganci na da mahimmanci. Amurka tana da ƙarfin soja da fasaha mai ƙarfin gaske, wanda ke taimaka mata. Amma don canza tsarin kasuwancin duniya ta hanyar amfani da tsarin da ya saɓa nata, za ta iya abin da zai sa sauran ƙasashen su nuna turjiya ko mayar da martani.
Wannan shi ne abin da ya faru musamman a lokacin da sauran ƙasashen duniya ke tunanin akwai abinda shugaban ƙasar ya taka ya sa yake ɓullo da waɗanna abubuwa na haraji da ƙasashen duniya.
Kasuwar hannayen jari ta fadi mafi yawa a Amurka. Hauhawar farashin kayayyaki zai ƙaru sosai a Amurka. Abin da ya sa mujallar Wall Street yanzu ke lissafin yiwuwar samun koma bayan tattalin arziki fiye da ko yaushe a Amurka.
Wataƙila akwai wani abu a cikin ƙa'idar cewa ainihin manufar anan ita ce raunana dala da rage farashin rancen Amurka.
A yanzu, Amurka tana duba tsarin kasuwancin duniya da ta ƙirƙira. Yana iya ci gaba ba tare da ita ba. Amma sauyi zai kasance da wahala sosai.










