Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da suaran sassan duniya 15/02/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da suaran sassan duniya 15/02/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Labarai da dumi-dumi, Isra'ila ta tabbatar da karɓar mutane uku da Hamas ta saki

    Rundunar sojin Isra'ila ta tabbatar da isar mutanen uku hannunta.

    Motocin Red Cross ne suka ɗauki mutanen uku daga Khan Younis, tare da rakiyar mayaƙan Hamas da na PIJ a lokacin da suka tafi da mutanen.

    A yanzu dakarun na Isra'ila za su ɗauki mutanen uku da jiragen soji zuw asibiti a Isra'ila domin a duba lafiyarsu.

  2. Kalli yadda aka miƙa wa Red Cross Isra'ilawa uku da Hamas ke garkuwa da su

  3. An ɓarke da murna a Isra'ila bayan sakin mutanen

    Iyalai da ƴan'uwan mutanen nan uku da Hamas ta saki sun ɓarke da muna da sowa bayan sakin Isra'ilawan

    Al'umma sun taru a dandalin tunawa da mutane a birnin Tel Aviv, inda suka kalli sakin Isra'ilawan kai tsaye ta akwatunan talbijin.

    Mutanen sun ɓarke da murna da sowa bayan da Hamas ta miƙa wa Red Cross mutanen.

  4. Labarai da dumi-dumi, Hamas ta miƙa wa Red Cross Isra'ilawa uku

    Hamas ta kamma miƙa wa Red Cross Isra'ilawan nan uku da ta saki a yau.

    An gudanar da bikin miƙa Isra'ilawan a birnin Khan Younis da ke kudancin Gaza.

    Tuni motcin Red Cross suka ɗauki mutanen zuwa wani wuri da sojojin ISra'ila suke a wani wuri a Gazar domin ɗaukarsu zuwa gida.

    Ana sa ran nan gaba kaɗan Isra'ila za ta saki Falasɗinawa 369 da take tsare da su a gidanjen yarinta.

  5. Labarai da dumi-dumi, An fito da Isra'ilawan uku daga motar mayaƙan Hamas

    Hamas ta fito da Isra'ilawan nan uku da za ta saki yau daga motar da ta kawo su wajen.

    Mutanen uku - Alexander Troufanov, da Yair Horn da kuma Sagui Dekel-Chen - sun hau kan dandamali domin miƙa su ga Red Cross

  6. Ma'aikaciyar Red Cross na sanya hannu kan takardun miƙa Isra'ilawan

    Ma'aikaciyar Red Cross na sanya hannu a kan teburin da ƙungiyar Hamas ta tsara gudanar da miƙa Isra'ilawan uku.

    A baya ma ƙungiyar ta tsara irin wannan teburi, inda a nan ne ake gudanar da bikin miƙa mutanen.

    A yau ma an miƙa Isra'ialwan a birnin Khan Younis da ke kudancin Gaza

  7. Labarai da dumi-dumi, Motocin Red Cross sun isa wurin da za su karɓi Isra'ilawan

    Motoci uku dauke da tutocin ƙungiyar agaji ta Red Cross sun isa Khan Younis domin karɓar Isra'ilawa uku daga hannun mayaƙan Hamas da suka yi garkuwa da su.

    Red Cross za ta kai mutanen ga sojojin Isra'ila da ke Gaza, da zarar Hamas ta mika su.

    Kamar yadda aka miƙa na baya, a yau ma al'umma sun taru domin shaida miƙa Isra'ilawan.

  8. An shirya karɓa Isra'ilawa uku da Hamas ke garkuwa da su a Gaza

    An shirya tsaf domin miƙa Isra'ilawa uku da Hamas ke tsare da su, yayin da Isra'ila za ta yi musayarsu da Falasɗinawa fiye da 350 da ke tsare a gidajen yarinta.

    Wannan ce musaya ta shida tsakanin ɓangarorin biyu tun bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninsu a watan da ya gabata.

    Isra'ilawa sun matsa lamba har sai sun ga an sako mazajen uku bayan shafe sama da kwanaki 500 ana tsare da su a arewacin Gaza.

    A farkon makon nan Hamas ta yi barazanar jan ƙafa a musayar fursunonin, kan zargin Isra'ila da karya sharuɗɗan tsagaita wutar, da hana shigar da agaji ga Falasɗinawa.

  9. M23 ta ce za ta ci gaba da dannawa bayan ƙwace iko da gabashin Congo

    'Yan tawayen M23 da gwamnatin Rwandan ke mara wa baya, - da suka karbe daukacin gabashin jamuriyar Dimukradiyyar Congo - sun ce za su ci gaba da dannawa har sai sun cimma nasara, bayan karbe iko da kudancin Kivu a jiya Juma'a.

    Mayaƙan na M23 sun kuma kwace iko da babban filin jirgin saman Bukavu.

    Ƴantawayen na M23 sun karɓe iko da birnin Bukavu, mai al'umma kusan miliyan guda.

    Hakan ne kuma ya bai wa M23 damar karɓe iko da tafkin Kivu da kewaye. \

    A watan da ya gabata ne suka karɓe birnin Goma mai muhimmanci, lamarin da ya MDD ta ce sama da mutum 3000 ne suka mutu, wasu dubban farar hula sun rasa muhallansu.

    Shugaban Congo ya zargi gwamnatin Rwanda da taimaka wa 'yan tawayen M23, zargin da Kigali ta sha musantawa.

    Ana sa ran batun tashin hankalin na Congo da Sudan, su za su mamaye taron ƙasashen Afurka da ke gudana a birnin Addis Ababa na ƙasar Habasha.

  10. Assalamu alaikum

    Masu bin wanan shafi namu barkamu da safiya, fatan kun wayi gari lafiya.

    Abdullahi Bello Diginza ne ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin kawo mukuririn wainar da ake toyawa a fadin duniya.

    Ku kasance da mu a wannan shafi da ma shafukanmu na sada zumunta