Nico Williams ya fifita Barca kan Arsenal, City da Bayern na harin Wirtz

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Atletico Madrid na duba yiwuwar dauko mai kai hari na Chelsea, Nicolas Jackson, Inda kungiyoyin Aston Villa da Newcastle ke son dan wasan Senegal din mai shekara 23. (Sun)

Paris St-Germain na son mai tsaron baya na Faransa da ke taka leda a Liverpool Ibrahima Konate, mai shekara 23, wanda zai iya komawa League 1 a kowanne lokaci. (ESPN)

Newcastle ta bi takwarorin ta na Brentford da Brighton a zawarcin dan wasan gaba na Jamus mai taka leda a Celtic, Nicolas Kuhn mai shekara 24. (Teamtalk)

Manchester City da Bayern Munich na son daukar mai tsaron baya na Jamus, Florian Wirtz , daga kungiyar Bayer Leverkusen. (Football Insider)

Chelsea na tuntubar wakilan dan wasan tsakiya na Sifaniya mai taka leda a Barcelona Marc Casado, mai shekara 21.(Cadena)

Dan wasan Sifaniya da Athletic Bilbao, mai shekara 22 Nico Williams , ya fi son komawa Barcelona, duk da kungiyoyin Arsenal da Liverpool na son dan wasan. (TBR Football)