Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da suaran sassan duniya 15/02/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da suaran sassan duniya 15/02/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Jama'a masu bibiyarmu a wannan shafin na BBC Hausa, da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye, a nan za mu rufe shafin na wannan rana ta Asabar, 15 ga watan Fabarairun 2025.

    A madadin kowa da kowa muke fatan za ku kasance da mu gobe Lahadi, idan Allah Ya kai mu.

    Amma kuma za ku iya ci gaba da leƙawa shafukanmu da sada zumunta domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo da muke sanyawa, har ma ku tafka muhawara.

    Bari mu rufe da wannan karin maganar da ke cewa - Kowa ya ɗau babban kashi ba ruwansa da gyara

  2. Ba lalle ba ne a sa Turai tattaunawar sulhun Ukraine - Amurka

    Wakilin Amurka na musamman ya yi nuni da cewa akwai yiwuwar ƙasashen Turai ba za su taka wata rawa ba a tattaunawar sulhu ta kawo ƙarshen yaƙin Ukraine.

    Keith Kellogg ya bayyana hakan ne a taron tsaro da aka yi a birnin Munich inda ya ce yunƙurin da aka yi a baya ya ci tura ne, saboda akwai ɓangarori da dama da ke da hannu a cikin lamarin.

    Tun da farko, Shugaban Volodymyr Zelensky na Ukraine, ya shaida wa taron cewa ya kamata nahiyar Turai ta ƙirƙiro wata rundunar sojoji.

    Ya ce sojojin ƙasarsa ne kawai a Turai ke da gogewa a fagen daga na zamani, yana mai gargaɗi da cewa sojojin Ukraine kaɗai ba za su isa ba.

    Tuni dai babbar jami'ar harkokin waje ta kungiyar ta EU, Kaja Kallas, ta yi watsi da shawarar ta Mista Zelensky.

  3. Ministan Wajen Djibouti ya ci zaɓen hukumar zartarwar AU

    An zaɓi ministan harkokin wajen Djibouti Mahmoud Ali Youssouf a matsayin sabon shugaban hukumar zartarwa ta ƙungiyar Tarayyar Afrika,AU.

    Ya kayar da jagoran ƴanhamayya na Kenya Raila Odinga a fafatawar da aka yi ta neman wanda zai gaji Moussa Faki Mahamat, a wa'adin shekara huɗu.

    An yi waje da Mista Odinga daga gasar a zagaye na shida na zaɓen, kuma shugabannin ƙasashe na ƙungiyar ta AU sun yanke shawarar mara baya ga ɗantakarar na Djiboutian.

    An gudanar da zaɓen ne a taron kungiyar ta AU da aka yi a Addis Ababa, babban birnin ƙasar Habasha.

    Taron ƙungiyar ya kasance cike da fargabar yaƙin Kongo zai iya rikiɗewa zuwa rikicin yanki.

  4. Ana harbe-harbe da wawashe kaya a birnin Bukavu na JD Kongo

    An samu rahotannin kwasar kaya da sunan ganima da harbe-harbe a birnin Bukavu na gabashin Kongo, wanda ƴantawaye da ke samun goyon bayan Rwanda suka shiga a jiya Juma'a.

    rahotanni na cewa mayaƙan na ƙungiyar M23 na ci gaba da kai hare-hare a gabashin ƙasar ta Jamhuriyar Dumukuraɗiyyar Kongo, lamarin da ke ƙara sanya fargabar cewa rikicin zai iya bazuwa zuwa wasu ƙasashen yankin.

    'Yantawaye sun kutsa cikin Bukavu ne makonni bayan sun ƙwace iko da Goma, birni mafi girma a gabashin ƙasar.

    Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres, ya yi kira da a gudanar da tattaunawa, inda ya yi gargaɗin cewa rikicin na Kongo na iya dagula zaman lafiyar yankin baki ɗaya.

  5. Amurka ta sake korar baƙin-haure 'yan India sama da 100 gida

    Wani jirgin sama da ke ɗauke da 'yan ƙasar India sama da ɗari ɗaya da ake zargin sun shiga Amurka ba bisa ƙa'ida ba na shirin sauka a birnin Amritsar, na jihar Punjab.

    Rukunin mutanen shi ne na biyu 'yan India da aka mayar ƙasar daga Amurka tun bayan da Shugaba Trump ya sake hawa kujerar mulki a watan da ya wuce.

    Yawancin mutanen da ke cikin wannan rukuni 'yan jihar ta Punjab ne.

    Wasu jagororin siyasa da 'yan uwan waɗanda aka koron sun je filin jirgin sama domin tarbarsu.

    A farkon watan nan wani jirgin saman soji na Amurka ya mayar da 'yan ƙasar ta India ɗari da huɗu, sanya da ankwa da sasari a ƙafarsu, lamarin da ya janyo kakkausar suka daga ƙasar ta India, kan wannan abu da Amurkar ta yi.

    Shugaba Trump ya lashi takobin aiwatar da korar baƙin hauren, wadda ba a taɓa ganin irinta ba a tarihin na Amurka, idan ya hau mulki.

    An yi ƙiyasin cewa akwai 'yan ƙasar India dubbai da suka shiga Amurka ba bisa ƙa'ida ba.

  6. Dubbai na zanga-zanga kan rugujewar rufin tashar jirgin ƙasa a Serbia

    Dubban ɗalibai da sauran jama'ar gari na gangami a birnin Kragujevac na Serbia domin wata babbar zanga-zangar da ke da alaka da rugujewar rufin wata tashar jirgin ƙasa.

    Lamarin da ya afku a tashar jirgin ƙasa da ke Novi Sad ya ƙara fusata al'ummar ƙasar da ke nuna wa gwamnati ya tsa bisa zargin aikata cin-hanci da rashawa.

    Wani da ya je domin shiga gangamin ya ce, “na je ne domin nuna goyon bayan wannan yunƙurin na ɗalibai, wanda ya rikiɗe ya zama fafutukar tabbatar da doka da adalci a cikin al’umma.''

    Zanga-zangar ta sauya salo cikin kwanakin nan inda take ƙalubalantar gwamnatin Shugaba Aleksander Vucic.

  7. Gwamnatin Afghanistan ta Taliban ta hana gidajen talabijin shiri kan siyasa da tattalin arziƙi

    Ƙungiyar kare haƙƙin 'yanjarida ta Afghanistan ta yi kakkausar suka kan wani umarni da hukumomin Taliban suka bayar na hana tashoshin talabijin watsa duk wasu shirye-shirye masu zaman kansu na siyasa ko tattalin arziƙi.

    A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ta ce shugabannin gwamnatin Taliban sun bayar da umarnin ne da baki ga gidajen talabijin cewa idan har suna ganin yin shirin ya zama dole to su gana da masu magana da yawun gwamnati a kan shirye-shiryen.

    Ƙungiyar ta ce wannan ba wani abu ba ne illa yunƙurin rufe bakin 'yan sauran masu suka da suka rage a ƙasar ta Afghanistan.

    Babu dai wata magana ta hukuma da ta fito daga ma'aikatar yaɗa labarai da al'adu ta ƙasar a kan batun.

    A watan Satumba na shekarar da ta wuce hukumomin na Taliban suka sanya doka kan watsa shirye-shiryen siyasa kai tsaye, da cewa dole ne kafafen yaɗa labarai su samu amincewar ma'aikatar kafin su yi irin waɗannan shirye-shirye na kai tsaye.

  8. Ɗaya daga cikin waɗanda Hamas ta saki yau ya tarar da 'yarsa da bai taɓa gani ba

    Lokacin da Hamas ta yi garkuwa da Ba'amurke ɗan Isra'ila, Sagui Dekel-Chen a ranar 7 ga watan Oktoba na 2023, daga garin Kibbutz Nir Oz, matsar na ɗauke da cikin wata takwas na haihuwarsu ta uku.

    Bayan da Hamas ta sake shi a musayar da ake yi ta yarjejeniyar dakatar da buɗe wuta a yaƙin Gaza yau, Asabar, ya yi murna sosai bayan da jami'an Isra'ila suka sheda masa cewa yana da 'ya mai shekara ɗaya.

    Da aka tambaye shi a game da lafiyarsa, Dekel-Chen, ya ce, ''ina cikin ƙoshin lafiya, ina cikin ƙoshin lafiya, ina da 'ya."

    Iyalansa sun yi matuƙar farin ciki da sakinsa, ''mahaifinmu ya dawo,'' kamar yadda suka bayyana a wata sanarwa.

    Haka kuma sun bayyana godiyarsu ga al'ummar Isra'ila waɗanda suka taimaka a fafutukar sakinsa, tare da kiran ci gaba da gwagwarmayar ganin an saki kowa ya koma gida.

  9. 'Yansanda sun kama wani 'malami' da zargin kisan ɗaliba a jihar Kwara

    Rundunar 'yansandan Najeriya a jihar Kwara ta kama wani mutum, AbdulRahman Bello, da ke iƙirarin malami ne, bisa zargin kisan wata ɗaliba domin aikata tsafi.

    An ce wadda aka kashe Hafsoh Yetunde Lawal, ɗalibar Kwalejin Ilimi ce ta jihar Kwara, da ke babban birnin jihar, Ilori.

    An bayar da rahoton ɓatanta a ranar Litinin da ta gabata 10 ga watan nan na Fabarairun 2025, bayan da ta halarci wani bikin suna.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, an kira ɗalibar ne ta waya a lokacin da take wajen bikin, inda daga baya aka bayar da rahoton cewa ba a san inda take ba.

    Ana zargin wanda ya kashe ta ya haɗu da ita ne ta shafin Facebook, inda ya yaudare ta ya karɓi lambar wayarta, har ta kai ya gayyace ita wajensa.

    Bayan ɓatan nata ne iyayenta suka shiga fargaba da damuwa, inda suka kai rahoton rashin ganin nata caji ofis na Oja Oba da ke Ilori

    Wata majiya ta sheda wa jaridar cewa, 'yansanda sun yi amfani da bayanan lambar wayar tata ne inda suka bi diddigin kiranta na ƙarshe, lamarin da ya kai su ga mutumin da ake zargi a Garejin Offa, kodayake an ce gidan su mutumin yana Isalekoto ne.

    Bayanai sun nuna cewa, bayan da aka kama mutumin, da farko ya ce bai san inda take ba, amma da aka matsa shi da bincike ya amsa cewa ɗalibar ta je wajensa amma ta mutu a sanadiyyar cutar numfashi ta asma.

    Majiyar ta ƙara da cewa an gano wasu abubuwa a gidan mutumin da ake zargi, wanda hakan ya nuna wannan ba shi ne karon farko da yake daddatsa jikin mutane ba.

    An ce mutumin ɗan wani fitaccen malami ne wanda ya rasu kwanan nan.

    Kakakin 'yansanda na jihar, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, wanda ya tabbatar da kisan a yau Asabar, ya bayyana shi da tsabar rashin tausayi da imani.

  10. NNPCL ya musanta zargin rashin aukin man fetur ɗin da yake sayarwa

    Babban kamfanin mai na Najeriya NNPCL ya yi watsi da iƙirarin da wani mutum ya yi cewa man da kamfanin ke sayarwa bai kai na Dangote auki ba.

    Cikin wani bidiyo da ya karaɗa shafukan sada zumunta an ga wani mutum da ya ce ya sayi man fetru daga kamfanin NNPCL a kan farashin naira 945, sannan ya sayi wani man a wani gidan mai da ke sauke man Dangote, a kan naira 925.

    A cikin bidiyon mutumin ya yi iƙirarin cewa man Dangote ya zarta na kamfanin NNPLC daɗewa ana amfani da shi, inda har ya yi iƙirarin gwada mayukan biyu a injuna biyu, daga ƙarshe ya ce na NNPCL ya riga na Dangote ƙarewa da minituna fiye da 10.

    To sai dai cikin wata sanarwar martani da NNPCL ɗin ya fitar ya ce gwajin da mutumin ya yi bai yi shi da ƙwarewa ba, sannan babu wata hujja ta kamawa a cikinsa.

    Sanarwar ta kuma ƙara da cewa mafi yawan man da wannan gidan mai na NNPCL - da mutumin ya yi iƙirarin sayo man - daga kamfanin Dangote yake sayensa.

    “NNPCL na jaddada ƙudirinsa na cewa man da yake sayarwa ana haɗa shi da ɗaya daga cikin manyan sidanarai masu inganci da ke taimakawa wajen tabbatar aukinsa da kuma rashin illa ga muhalli'', in ji sanarwar.

    Daga ƙarshe ya gargaɗi masu irin wannan ɗabi'a cewa ba zai jure irin waɗannan ƙarairayi da ake shiryawa domin ɓata masa suna da kuma cutar da ƴan Najeriya ba.

  11. Manyan motocin da ke ɗauke da fursunonin Isra'ila sun isa Gaza

    Bayanai daga Gaza na cewa motocin da ke ɗauke da fursunonin Falasɗinawa sun isa Gaza.

    Dama dai an tsara cewa 333 daga cikin fursunonin da Isra'ila za ta saka Gaza za a kaisu.

    Tuni ƴan'uwa da abokan arziki suka yi dafifi a wurin domin yin arba da ƴan'uwansu.

  12. An gudanar da bikin al'adar Rigata a jihar Kebbi

    Al'ummar Masarautar Yauri a Kebbi da ke arewacin Najeriya sun gudanar da bikin al'ada na Rigata.

    Rigata, Biki ne wanda ake yi shekara-shekara na al'ada a ƙasar Yauri da ke Kebbi.

    Bikin ya samu halartar gwamnan jihar Kebbi Comr. Nasir Idris da sarkin Yauri, Muhammad Zayyanu Abdullahi.

  13. Gwamnatin Najeriya ta musanta zarge-zargen rashawa da jami'in Binance ya yi wa ƙasar

    Gwamnatin tarayya ta yi watsi da iƙirarin da jami'in kamfanin Binance, Tigran Gambaryan, wanda ya shafe wata takwas yana tsare a ƙasar, kan zarge-zargen rashawa.

    A kwanakin baya ne aka gurfanar da Gambaryan- ɗan Amurka - a kotun Najeriya bisa zargin laifukan kuɗi.

    To sai dai hukumomin Najeriya sun sake shi ne bayan shiga tsakani da gwamnatin Amurka ta yi.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Gambaryan ya yi ikirarin cewa kama shi da gwamnatin Najeriya ta yi ba bisa ƙa'ida ba ya sa tsohon shugaban ƙasar Amurka, Joe Biden ya kauce wa ganawar da ya shirya yi da Shugaban Najeriya, Bola Tinubu a yayin taron Majalisar Dinkin Duniya na 2024 (UNGA).

    Ya kuma zargi mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu kan lamarin, sannan ya ce gwamnatin Amurka ta rage yawan wakilan Najeriya da suka halarci taron na MDD.

    Jami'in na Binance ya kuma zargi wasu ƴan majalisar ƙasar uku da neman cin hancin dala miliyan 150 daga wajensa.

    To sai dai a martanin da gwamnatin ƙasar ta mayar masa, ta ce zarge-zargen nasa ba su da tushe balle makama.

    Cikin wata sanarwa da ministan yaɗa labaran ƙasar, Mohammed Idris ya fitar, ya bayyana iƙirarin Gambaryan a matsayin tsantsar ƙarya da gangan.

    "Gwamnatin Najeriya ta damu matuƙa da zarge-zargen marasa tushe, da kuma kalaman ɓatanci da Tigran Gambaryan, da aka yi wa shari'a a Najeriya kwannan kan laifukan kuɗi,'' a cewar sanarwar.

    Ta kuma ƙara da cewa ''gwamnati ta ki amincewa da tayin da Binance ta yi na biyan dala miliyan biyar don sakin Mista Gambaryan, don yin sulhu da gwamnatin Amurka."

    A farkon shekarar da ta gabata ne dai gwamnatin Najeriya ta tsare Mista Gambaryan tare da abokin aikinsa, Nadeem Anjarwalla ɗan Kenya asalin Birtaniya mai shekara 37 bisa zargin laifukan ɓarnatar da kuɗi da hukumar EFCC ke bincike.

    To amma a watan Maris ɗin shekarar Anjarwalla ya gudu daga wurin da ake tsare da su, ya kuma fice daga Najeriya.

  14. Zelensky na kira ga ƙasashen Turai su kafa rundunar sojin kare kai daga barazanar Rasha

    Shugaban ƙasar Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya yi kira ga ƙasashen Turai su kafa rundunar sojin haɗin gwiwarsu, domin kare ƙasashensu daga barazanar ƙasar Rasha.

    Yayin da yake jawabi a wurin tsaron tsaro na ƙasashenv da ke gudana a birnin Munich na ƙasar Jamus, Mista Zelensky ya ce tsohon ƙawance na gomman shekaru da ke tsakanin Amurka da Turai na zuwa ƙarshe, don haka Turai na buƙatar ɗaukar mataki.

    Mista Zelensky ya jaddada buƙatar ƙasashen Turai -- da Ukraine -- su shiga duk wata tattaunawar sulhu da Rasha.

    A farkon wannan makon, Shugaba Trump na Amurka ya yi magana kai tsaye da Vladimir Putin, wanda da alama ya mayar da ƙawayen Amurka gefe.

    Da yake magana a gaban Mista Zelensky, Shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz, ya ce ƙasarsa ba za ta taɓa goyon bayan zaman lafiyar da aka tilasta ba.

  15. Labarai da dumi-dumi, Rukunin farko na fursunonin Falasɗinawa sun isa Ramallah

    Isra'ila ta fara sakin fursunonin Falasɗinawa da ke tsare a gidajen yarinta, bayan da Hamas ta saki Isra'ilawa uku da take garkuwa da su.

    Motar farko ɗauke fa Falasdinawan ta isa birnin Ramallah a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.

    Dandazon mutanen da ke dakon isowar Falasɗinawan sun ɓarke da murna da sowa a lokacin da motar d aisa wurin da suke jira.

    Ana sa ran Isra'ilar za ta saki Falasɗinawa 369 a yau, waɗanda ke tsare a gidajen yarinta.

  16. Netanyahu ya gode wa Trump bayan sakin Isra'ilawa uku

    Ofishin firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya fitar da wata sanarwar maraba da dawowar Isra'ilawa uku da aka saki yau.

    Sanarwar ta ce gwamnati na ci gaba aiki da Amurka domin ganin an sako sauran Isra'ilawan da suka rage a hannun Hamas a Gaza.

    Haka kuma sanarwar ta nanata ikirarin cewa Hamas ta "yi yunƙurin karya yarjejeniyar" a wannan makon, tana mai cewa ƙungiyar ta haifar da "ruɗani ta hanyar ikirarin ƙarya".

    A ƙarshe sanarwar ta gode wa sojojin Isra'ila da ke yankin Gaza da kewaye - da shugaban Amurka Donald Trump bisa "ƙoƙarinsa" - na ci gaba da sakin mutanen da aka yi garkuwa da su.

    Tana mai cewa Isra'ila na aiki da Amurka domin kuɓutar da duka mutanen da aka yi garkuwa da su daga Gaza cikin gaggawa

  17. Hotunan yadda Hamas ta saki Isra'ilawa Uku a Gaza

    Yayain da muke kawo muku bayanan sakin Isra'ilawan nan Uku da Hamas ta yi garkuwa da du, Alexander Troufanov da Yair Horn, da kuma Sagui Dekel-Chen , ga hotunan yadda sakin nasu ya kasance.

  18. Ana shirye-shiryen sakin fursunonin Falasɗinawa 369

    Jami'an tsaro na shirye-shiryen sakin fursunonin Falasɗinawa.

    Ana sa ran sakin fursunoni 369 daga gidajen yarin Isra'ila a yau.

    Ciki har da mutum 29 daga Gaɓar Yamma da kuma bakwai daga Birnin Kudus.

    Za a fitar da mutum 24 daga cikinsu zuwa ƙasashen waje, kamar yadda ƙungiyar fursunonin Falasɗinawa ta bayyana.

    Haka kuma za a saki mutum 333 da aka tsare a Gaza tun bayan harin ranar 7 ga watan Oktoban 2023, a cewar ƙungiyar.

    Daga cikin Falasɗinawa da za a saki har da waɗanda ake tsare da su bayan samunsu da laifin munanan hare-hare kan Isra'ilawa.

    To amma da dama daga cikinsu an kama su ne bayan a lokacin yakin inda ake tsare da su ba tare da wata tuhuma ba.

  19. Ana dakon Isra'ila ta saki Falasɗinawa 369 daga gidajen yarinta

    Bayan kammala miƙa Isra'ilawa uku da Hamas ke garkuwa da du a Gaza, yanzu kallo ya koma Isra'ila domin sakin Falasɗinawan da take tsare da su a gidajen yarinta.

    Ana saran Isra'ilar za ta saki Falasɗinawa 369 daga gidajen yarinta.

    Za a kai da dama cikinsu birnin Kahn Younis da ke kudancin Gaza inda za a duba lafiyar da dama daga cikinsu, yayin da ake sa ran fitar da wasu daga yankin zuwa ƙasashen waje.

  20. Hamas ta ce ta hanyar sulhu 'ne kaɗai' za ta saki Isra'ilawan da take garkuwa da su

    A wata Sanarwa da Hamas ta fitar a yau, ta ce sakin Isra'ilawan da ta yi a yau, ya nuna cewa babu hanyar da za su kuɓuta ''in ba ta hanyar sulhu tare da aiki da sharuɗan yarjejeniyar tsagaita wuta ba''.

    Ƙungiyar ta kara da cewa: ''Muna faɗa wa duniya cewa babu wata ƙaura, in ba ta Birnin Ƙudus ba,'' a wani martani ga shawarar shugaban Amurka Donald Trump na kwashe duka al'ummar Gaza daga yankin domin mayar da su ƙasashe makwabta.

    A kwanakin baya-bayan nan dai an shiga ruɗani dangane da ci gaba da aiki da yarjejeniyar tsagaita wutar, bayan da Hamas ta yi barazanar dakatar da sakin Isra'ilawan, saboda zargin Isra'ila da saɓa wa yarjejeniyar, zargin da Isra'ilar ta musanta.