Rundunar 'yansandan Najeriya a jihar Kwara ta kama wani mutum, AbdulRahman Bello, da ke iƙirarin malami ne, bisa zargin kisan wata ɗaliba domin aikata tsafi.
An ce wadda aka kashe Hafsoh Yetunde Lawal, ɗalibar Kwalejin Ilimi ce ta jihar Kwara, da ke babban birnin jihar, Ilori.
An bayar da rahoton ɓatanta a ranar Litinin da ta gabata 10 ga watan nan na Fabarairun 2025, bayan da ta halarci wani bikin suna.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, an kira ɗalibar ne ta waya a lokacin da take wajen bikin, inda daga baya aka bayar da rahoton cewa ba a san inda take ba.
Ana zargin wanda ya kashe ta ya haɗu da ita ne ta shafin Facebook, inda ya yaudare ta ya karɓi lambar wayarta, har ta kai ya gayyace ita wajensa.
Bayan ɓatan nata ne iyayenta suka shiga fargaba da damuwa, inda suka kai rahoton rashin ganin nata caji ofis na Oja Oba da ke Ilori
Wata majiya ta sheda wa jaridar cewa, 'yansanda sun yi amfani da bayanan lambar wayar tata ne inda suka bi diddigin kiranta na ƙarshe, lamarin da ya kai su ga mutumin da ake zargi a Garejin Offa, kodayake an ce gidan su mutumin yana Isalekoto ne.
Bayanai sun nuna cewa, bayan da aka kama mutumin, da farko ya ce bai san inda take ba, amma da aka matsa shi da bincike ya amsa cewa ɗalibar ta je wajensa amma ta mutu a sanadiyyar cutar numfashi ta asma.
Majiyar ta ƙara da cewa an gano wasu abubuwa a gidan mutumin da ake zargi, wanda hakan ya nuna wannan ba shi ne karon farko da yake daddatsa jikin mutane ba.
An ce mutumin ɗan wani fitaccen malami ne wanda ya rasu kwanan nan.
Kakakin 'yansanda na jihar, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, wanda ya tabbatar da kisan a yau Asabar, ya bayyana shi da tsabar rashin tausayi da imani.