Hamas ta yi watsi da yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra'ila ta gabatar

Asalin hoton, Reuters
Wani babban mai magana da yawun Hamas ya shaidawa BBC kungiyar ta yi watsi da daftarin yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra'ila ta gabatar, sakamakon cewa babu batun amincewa da shigar da daruruwar motocin jin kai a kulluyaumin a yarjejeniyar.
Hamas ta kuma ce daftarin bai yi wata magana a kan ba da tabbacin kawo karshen yakin din din din ba.
Babban jam'in na Hamas ya shaida wa BBC cewa abun da yarjejeniyar ta kunsa, ya saɓa wa tattaunawar farko da suka yi da jami'an Amurka.
Ita dai Hamas ta nemi Amurka ta ba da lamunin cewa Isra'ila ba za ta ci gaba da yaƙin ba idan tattaunawar tsagaita wuta ba ta yi nasara ba bayan fara aiwatar da ta farko.
