Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis 30/05/2025.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Ahmad Bawage, Aisha Babangida da Badamasi Abdulkadir Mukhtar

  1. Hamas ta yi watsi da yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra'ila ta gabatar

    Wani babban mai magana da yawun Hamas ya shaidawa BBC kungiyar ta yi watsi da daftarin yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra'ila ta gabatar, sakamakon cewa babu batun amincewa da shigar da daruruwar motocin jin kai a kulluyaumin a yarjejeniyar.

    Hamas ta kuma ce daftarin bai yi wata magana a kan ba da tabbacin kawo karshen yakin din din din ba.

    Babban jam'in na Hamas ya shaida wa BBC cewa abun da yarjejeniyar ta kunsa, ya saɓa wa tattaunawar farko da suka yi da jami'an Amurka.

    Ita dai Hamas ta nemi Amurka ta ba da lamunin cewa Isra'ila ba za ta ci gaba da yaƙin ba idan tattaunawar tsagaita wuta ba ta yi nasara ba bayan fara aiwatar da ta farko.

  2. Assalamu Alaikum

    Masu bibiyar mu barkan mu da safiyar Juma'a - Hajj babbar rana.

    Wannan shafi zai kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da kuma sassan duniya.

    Ku kasance da mu!