Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis 30/05/2025.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Ahmad Bawage, Aisha Babangida da Badamasi Abdulkadir Mukhtar

  1. Isra'ila ta kori mutane daga asibiti ɗaya tilo da ya rage a arewacin Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, al-Awda staff

    An rufe asibiti ɗaya tilo da ya rage a arewacin Gaza, bayan dakarun Isra'ila sun bayar da umarnin a fice daga cikin sa da gaggawa.

    Shugaban asibitin Dr Mohammed Salha ya ce an kwashe jama'a daga asibitin Al-Awda da ke Jabalia a ranar Alhamis da yammaci.

    Ya shaidawa BBC cewa "Muna cikin takaici matuƙa saboda tilasta rufe asibitin, bayan kutse na makonni biyu da aka yi. A yanzu dai wannan na nufin babu sauran asibiti a arewaci.''

    Isra'ila ba ta ce komai ba a kai, kuma BBC ta tuntuɓi rundunar sojin Isra'ilan.

    Dr Salha ya tabbatarwa BBC cewa an yi ruwan bama-bamai da harsasai a kan asibitin a ranar Alhamis, kuma dakarun Isra'ilan ne suka yi.

    Ya ce yana cikin asibitin ne kuma dakarun Isra'ilan suka kira shi tare da bayar da umarnin kowa ya fice daga asibitin cikin gaggawa.

    Hukumomin lafiya na duniya sun yi Allah wadai da matakin.

  2. China ta mayar da martani kan zargin karya yarjejeniyar haraji da Trump ya yi mata

    Trump/Xi

    Asalin hoton, PA Media / Getty Images

    China ta mayar da martani ga zargin da shugaba Trump ya yi mata a farkon watan nan cewa tana saɓawa sharuɗɗan yarjejeniyar da suka ƙulla.

    Martanin da Beijing ta mayar ranar Juma'a ya ce kamata ya yi Amurka ta mayar da hankali wajen sassauta ''tsauraran matakan ƙin jini da ta ke nuna wa China.''

    Shugaba Trump ya zargi China da ƙin janye matakin ƙarin haraji da ta sanya wa Amurka, duk da yarjejeniyar yin hakan da suka ƙulla.

    Washington da Beijing sun amince su rage yawan harajin da suka sanya wa juna, bayan wata tattaunawa tsakanin ɓangarorin a Geneva.

    Zargin da ke fitowa daga dukkan ɓangarorin sun fara janyo fargaba a tsakanin ƴan kasuwa saboda tunanin cewa dambarwar za ta janyo tashin farashi da koma bayan kasuwanci.

    China ta buƙaci Amurka ta gyara kura kuren da matakan da ta ɗauka suka haifar, da kuma tabbatar da biyayya ga ƙa'idojin yarjejeniyar da suka ƙulla a Geneva.

  3. 'Rikicin Indiya da Pakistan zai ƙara haɗarin kazancewar al'amura'

    Wani babban janar ɗin soji a Pakistan ya ce ƙasarsa da Indiya sun kusa rage yawan dakarun da aka jibge a iyakokinsu kafin arangamar da aka samu tsakanin sojojinsu a farkon watan nan.

    Janar Sahir Mirza, ya yi gargaɗi cewa rikicin baya-bayan nan zai ƙara haɗarin ƙazancewar lamarin a gaba tsakanin ƙasashen biyu masu adawa da juna da suka mallaki makamin nukiliya.

    Duka ɓangarorin biyu sun yi amfani da jiragen yaƙi da makamai masu linzami da kuma jirage marasa matuƙa da artilari a rikicin na kwanaki huɗu.

    Rikicin baya-bayan nan a watan Afrilu ya samo asali ne sakamakon harin da aka kai wa ƴan yawon buɗe ido a yankin Kashmir da ke ƙarƙashin Indiya wanda ya yi sanadin kashe mutum ashirin da shida.

    Delhi ta ɗora alhakin lamarin kan abin da ta kira ƴan'ta'adda da ke samun goyon bayan Pakistan, zargin da Pakistan ɗin ta musanta.

  4. INEC ta tsayar da ranar zaɓen gwamnan Ekiti da Osun

    ZAƁE

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar zaɓe ta Najeriya, INEC ta tsayar da ranar 20 ga watan Yunin 2026 a matsayin ranar gudanar da zaɓen gwamnan jihar Ekiti,da kuma ranar 8 ga watan Ogustan 2026 a matsayin ranar zaɓen gwamnan jihar Osun.

    Shugaban hukumar, farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana haka a wajen rantsar da sabbin kwamishinonin hukumar shida da majalisar dokoki ta amince da su kwanan nan.

    Ya ce “A zaɓen jihar Ekiti, za a gudanar da zaɓukan fitar da gwani daga ranar 20 ga watan Oktoban 2025, a kuma kammala a ranar 10 ga watan Nuwamban 2025 domin a kammala duk wasu ayyukan buga sunan ƴan takara da misalin ƙarfe 6 na yammacin ranar 22 ga watan Disamban 2025.''

    ''Za a fara yaƙin neman zaɓe a ranar 21 ga watan Janairun 2026 a kuma kammala ana saura sa'oi 24 a kaɗa ƙuri'a.''

    Ya ƙara da cewa ''A jihar Osun kuma za a yi zaɓukan fitar da gwamni daga ranar 24 ga watan Nuwamnban 2025 a kuma kammala a ranar 15 ga watan Disamban 2025. INEC za ta wallafa sunan ƴan takara da misalin ƙarfe 6 na yammacin ranar 9 ga watan Faburairun 2026.''

    ''Za a yi yaƙin neman zaɓe daga daga ranar 11 ga watan Maris zuwa ana saura sa'oi 24 a kaɗa ƙuri'a.''

    Farfesa Yakubu ya ce INEC tana shiri domin gudanar da zaɓukan cike gurbi na kujerun majalisar dokoki a matakin tarayya da kuma wasu jihohin Najeriya.

  5. An fara shari'ar Simon Ekpan a Finland

    Simon Ekpa

    Asalin hoton, Simon Ekpa/Facebook

    An fara shari'ar ɗaya daga cikin jagororin ƙungiyar IPOB mai rajin kafa ƙasar Biafra, Simon Ekpa, inda hukumomin Finland ke zargin shi da shiga ayyukan ƙungiyar ta'addanci.

    Epka, wanda tsohon kansila ne a yankin Lahti na ƙasar ta Finland ya gurfana ne a gaban kotun lardin Päijät-Häme a yau Juma'a, inda aka fara sauraron ƙarar da aka yi masa kan zargin ta'addanci.

    Ana zargin Ekpa da tunzura jama'a domin tayar da hankali, da kuma sauran ayyukan ta'addanci

    Masu gabatar da ƙara sun yi zargin cewa ya na da hannu dumu-dumu a ayyukan neman kafa ƙasar Biafra a yankin kudu maso gabashin Najeriya.

    Masu gabatar da ƙarar sun ce ayyukan sa sun saɓa wa dokar ta'addanci ta ƙasar Finland, kuma suna neman a yanke masa hukuncin ɗaurin shekara shida.

    A yayin zaman kotun, lauyan Ekpa, Kaarle Gummerus, ya musanta zargin, kuma ya bayyana shakku a kan sahihancin bayanan da ake samu daga Najeriya a game da shi.

  6. Mutumin da ya ƙirƙiro maganin zubar da ciki ya mutu

    Farfesa Etienne-Emile Baulieu, wanda ya ƙirƙiri maganin zubar da ciki na RU 486, a ranar 5 ga watan Disamban 1984, birnin Paris

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙwararren mai binciken kimiyya wanda ya ƙirƙiri maganin zubar da ciki, Étienne-Émile Baulieu ya mutu yana da shekara 98 a duniya.

    Dr Baulieu ya ƙirƙiro maganin zubar da cikin ne a shekarar 1984.

    Bayan ƙirƙiro shi, maganin mifepristone ya kawo sauyi a tsarin haihuwa a duniya.

    Maganin nasa ya bai wa mata damar kauce wa yin tiyata domin zubar da ciki, da kuma yanke hukunci a kan rayuwarsu.

    Maganin nasa ya shiga cikin magunguna masu muhimmanci ga hukumar lafiya ta duniya.

    Matar Dr Baulieu ta ce binciken da ya yi sun zamo abubuwan kawo cigaban rayuwa a duniya.

  7. Sojojin Najeriya sun kashe ƙasurgumin ɗan Boko Haram, Abu Fatima

    Sojoji

    Asalin hoton, X/Defence HQ

    Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe wani ƙasurgumin ɗan Boko Haram wanda ake kira Amir Abu Fatima.

    Wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar a shafinta na X, ta ce an samu nasarar kashe Abu Fatima ne a wani samame da dakarun Haɗin-Kai suka kai yankin Kukawa na jihar Borno.

    Sojojin sun ce Abu Fatima na cikin mutanen da rundunar ke nema ruwa a jallo, inda ta ƙuduri aniyar bai wa duk wanda ya bayar da rahoton inda za a kama shi ladan naira miliyan 100.

    "Abu Fatima ya samu munanan raunuka lokacin da ake ba ta-kashi kafin mutuwarsa. An kuma kashe mataimakinsa da wasu ƙwararru kan ababen fashewa da dama har ma da sauran ƴan ta'adda da suke tare da shi," in ji sanarwar.

    Dakarun sun kuma ƙwato bindigogin AK-47 da harsasai da kuma abubuwan fashewa.

    Ta ce babu jami'inta ko ɗaya da ya mutu ko ya samu rauni yayin samamen.

    Wannan dai babban koma-baya ne ga jagorancin mayaƙan na Boko Haram a yankin, da kuma ƙarin ƙarfin gwiwar sojojin Najeriya wajen dawo da zaman lafiya a yankin arewa maso gabas a daidai lokacin da ake ganin dawowar ayyukan mayaƙar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  8. An zargi dakarun RSF da kai farmaki ba ƙaƙƙautawa a birnin El Fasher na Sudan

    Sudan

    Asalin hoton, Abdulhafeez al Ghali

    Shirin samar da abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya ya zargi dakarun RSF da kai farmaki ba ƙaƙƙautawa kan ɗakunan ajiyar kayayyaki da ke birnin El Fasher, babban birnin arewacin Darfur da ke Sudan.

    A cewar wakilin BBC, shirin samar da abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi allawadai da yadda ake yawaita kai mata hari a El-Fasher.

    Rikici tsakanin sojoji da RSF ya ƙazanta a birnin a makonnin baya-bayan nan wanda shi ne birni na ƙarshe a yankin da ke ƙarƙashin ikon sojoji.

    Sama da farar hula ɗari biyar aka kashe sannan wasu dubbai sun ɗaiɗaita sakamakon rikicin.

    Ƙungiyoyin agaji na tara kayan abinci da sauran abubuwan buƙata gabanin saukar damina yayin da farashin kayan abinci ke ƙaruwa sannan al'amura na ƙara taɓarɓarewa.

  9. Al'ummar Gaza na cikin barazanar faɗa wa yunwa - MDD

    Gaza

    Asalin hoton, EPA / Shutterstock

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa baki-ɗaya al'ummar Gaza na cikin barazanar faɗa wa yunwa.

    Jens Laerke na hukumar kula da al'amuran jin-ƙai ta MDD ya ce yankin Gaza ya zama wajen da aka fi fama da yunwa a duniya.

    A wani taron manema labarai a birnin Geneva, jami'in ya zargi Isra'ila da rufe hanyoyin shigar da kayan jin-ƙai zuwa yankin Falasɗinawa tun bayan ɗage matakin na wani ɗan lokaci a farkon watan nan.

    A baya-bayan nan an yi ta fuskantar ruɗani yayin shirin rarraba agaji da ke samun goyon bayan Isra'ila da Amurka, inda Falasɗinawa da dama da ke fama da yunwa suka yi dandazo a cibiyoyin rarraba kayayyakin.

  10. Labarai da dumi-dumi, Mutanen da ambaliyar ruwa ta kashe a Neja sun kai 110

    Ambaliya

    Asalin hoton, Adamu Ngulde

    Alkaluman waɗanda ambaliyar ruwa ta kashe a jihar Neja ya kai mutum 110, a cewar hukumar ba da agajin gaggawa na jihar.

    Masu aikin ceto sun ce sun gano gawawwaki da dama.

    Jami'ai a yankin Mokwa wurin da lamarin ya faru, sun yi gargaɗin cewa ƙarin mutane na cikin barazana a birnin.

    An shafe tsawon sa'o'i ana tafka mamakon ruwan sama a yankin ranar Laraba, inda ruwa ya tafi da gidaje aƙalla 50.

    Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin yiwuwar samun ambaliya a kusan rabin jihohin ƙasar 36.

    Sama da mutum 1,200 ne suka mutu sakamakon ambaliya a bara sannan sama da miliyan ɗaya suka ɗaiɗaita, a ambaliyar da ba a taɓa gani ba cikin gomman shekaru.

  11. Jirgin sama ɗauke da shugaban Laberiya ya yi saukar ba-zata

    Laberiya

    Asalin hoton, FrontPage Africa

    An samu jinkirin tashi da saukar jiragen sama a babban filin jirgin saman Laberiya a jiya da daddare bayan da jirgin sama ɗauke da shugaba Jospeh Boakai ya yi saukar ba-zata.

    Hukumar kula da sufurin jiragen sama a ƙasar ta ce tayar jirgin ce ta samu matsala lokacin da ya zo sauka filin jiragen sama na Roberts kusa da Monrovia.

    Hukumar ta musanta cewa rashin kyawun yanayin hanyar da jirage ke bi wajen tashi ne ya janyo matsalar.

    An samu fitar da shugaba Boakai da tawagarsa daga cikin jirgin ba tare da wata matsala ba.

    Ofishin shugaban ƙasar Laberiya dai ba ta ce uffan ba kan lamarin.

    Yanzu dai komai ya fara daidaita sannan jirage na tashi da kuma sauka.

  12. Sojoji sun ce sun hallaka ƴan ta'adda 60 a jihar Borno

    Sojoji

    Asalin hoton, Nigerian Army

    Dakarun sojin Najeriya na Operation Haɗin-Kai sun ce sun kashe ƴan ta da ƙayar-baya sama da 60 a wani artabu da suka yi a jihar Borno.

    Wata sanarwa da rundunar sojin Najeriya ta fitar ranar Juma'a, ta ce dakarun sun samu nasarar kashe ƴan ta'ddan ne bayan bata-kashi da suka yi daddare a yankin Bita na jihar.

    Sanarwar ta ce ƴan ta da ƙayar-bayan sun far wa sojojin birget 26 ne da misalin karfe 1:09 na asubahin yau Juma'a, inda dakarun Haɗin-Kai suka mayar da martani da hare-hare ta sama da kuma ƙasa kan ɓata-garin.

    "Sojoji sun kaddamar da hare-haren sama da kuma ta ƙasa kan sansanonin ƴan ta da ƙayar baya a yankin Bita na jihar Borno da asubahin yau Juma'a, lamarin ya kai ga hallaka aƙalla 60 daga cikinsu," a cewar sanarwar sojojin.

  13. Gwamnatin Tinubu ta jefa ƴan Najeriya fiye da miliyan 150 cikin tsananin talauci - NLC

    Joe Ajero

    Asalin hoton, NLC

    A daidai lokacin da gwamnatin shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ke cika shekara biyu da soma wa’adin mulkinta na farko, hadaddiyar kungiyar kwadagon kasar ta NLC ta bayyana gwamnatin a matsayin wadda ta kasa cika alkawarrun da ta dauka a bangarori da dama.

    Kungiyar ta NLC ta ce ikirarin shugaban kasar na cewa lokacin wahalar rayuwa ya zo karshe, na tamkar yaudara ce kasancewar manufofi da tsare-tsaren gwamnatin sun jefa fiye da ‘yan Najeriya miliyan 150 a cikin tsananin talauci da tsadar rayuwa.

    A cikin wani bayani da ta fitar, Kungiyar kwadagon ta Najeriya ta bakin shugabanta Kwamared Joe Ajaero ya ce babu komi a cikin tafiyar wannan gwamnati face maimaita gazawar da gwamnatin da ta gada ta yi ne musamman a bangaren sabunta fata da manufofi.

    To sai dai jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, ta mayar da martini ga kungiyar ta kwadago ta NLC, inda ta ce babu adalci a maganar ‘yan kwadagon sannan ba su yi bincike mai zurfi ba, kafin furta wadannan kalamai.

  14. Pakistan ta amince da dokar haramta auren wuri a Islamabad

    Pakistan

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Pakistan Asif Ali Zardari ya amince da dokar kawo karshen auren wuri a Islamabad, babban birnin ƙasar.

    Sabuwar dokar ta yi tanadin cewa daga yanzu sai namiji ko mace ta kai shekara 18 kafin ta yi ko kuma ya yi aure a Islamabad.

    Za a ɗauki batun auren wuri a matsayin babban laifi a yanzu.

    Iyalai da malamai waɗanda ke tilasta yara yin auren wuri, za su fuskanci ɗaurin shekara bakwai a gidan yari.

    Sai dai ƙungiyoyin addini sun yi adawa da dokar, inda suka ce ya saɓa wa addini da kuma al'adun al'ummar Pakistan.

    Unicef ta ce Pakistan gida ce ga sama da mutum miliyan 19 da aka yi wa auren wuri - wanda ya sa ƙasar ke mataki na shida a duniya.

  15. 'Isra'ila ta tilastawa al'ummar Gaza shiga yunwa da gan-gan'

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Babban jami'in Majalisar Ɗinkin Duniya da ke kula da ba da agajin jin-kai, Tom Fletcher ya ce Isra'ila ta tilastawa al'ummar Gaza shiga cikin yunwa da gan-gan.

    Ya shaida wa BBC cewa duniya na da alhakin ɗaukar manyan matakai na kai agaji.

    Ya ce ministocin Isra'ila na ta nanata cewa suna son ganin an kori mutanen Gaza daga yankin, ba tare da ra'ayinsu ba - ta hanyar hana shigar da abinci, a wani mataki na jefa jama'a cikin yunwa.

    Mista Fletcher ya sake yin kira ga ƙasashen duniya da su hana kisan kare dangi a Gaza.

    Ya kuma musanta zargin da Isra'ila ta yi na cewa yawancin agajin da aka aika zuwa yankin na karewa ne a hannun Hamas.

  16. Yadda tsadar raguna ke tilasta masu layya sauya tunani

    Raguna

    Yayin da rage mako guda a yi bikin babbar Sallah a Nijeriya, wasu masu niyyar yin layya sun ce sun fara canza tunani saboda tsadar rago.

    Ana matuƙar kokawa da tsadar rayuwa a ƙasar, yayin da masu sayar da dabbobi ke cewa kuɗin sufuri ya ƙara ta'azzara farashin raguna a bana.

    Wakilin BBC Ahmed Wakili wanda ya ziyarci kasuwar ƴan awaki da ke yankin Maraba a jihar Nasarawa, ya ruwaito ganin ɗaruruwan raguna da rakuma da shanu da kuma sauran dabbobi waɗanda aka kai don sayarwa.

    Shugaban kasuwar, Yakubu Sani ya bayyana cewa raguna sun fi tsada a bana idan aka kwatanta da bara.

    "Abin da ke janyo ƙarin tsadar shi ne kudin mota, a bara 3,500 masu mota ke ɗaukar rago ɗaya - a bana kuwa abin ya kai kusan 8,000," in ji Sani.

    Wani mai suna Ubale Bala wanda ya je sayar da raguna daga jihar Bauchi, ya ce farashin bana da na bara ya bambanta.

    "Ragunan sun yi tsada ba kaɗan ba. Na zo sayan ragon 150,000 - zuwa 180,000 amma gaskiya sun yi ƙanƙanta ba su ma kai a yanka su ba," in ji wani da ya je saye.

    • Dalilan da suka sa farashin dabbobi ya yi tashin gwauron zabbi
    • Yadda farashin raguna ya yi tashin gwauron zabi a kasuwannin Abuja
  17. Fernandes na duba yiwuwar barin Man Utd zuwa Al-Hilal

    Fernandes

    Asalin hoton, Getty Images

    Bruno Fernandes na duba yiwuwar ficewa daga Manchester United a mako mai zuwa, inda yake tunanin komawa Al-Hilal ta Saudiyya waɗanda suka yi masa tayin albashi mai tsoka.

    An bayyana cewa wakilan Fernandes sun gana da jami'an Al-Hilal cikin kwanaki da suka gabata domin samun mafita da za ta kai ga ɗan wasan mai shekara 30 ya koma ƙungiyar.

    Batun dai na janyo muhawara a kafofin sada zumunta a daidai lokacin da Man Utd ɗin tayi balaguro zuwa nahiyar Asiya don buga wasannin sada zumunta. Latsa nan domin karanta cikakken labarin

  18. Rasha ta samu dala biliyan 25 wajen fitar da mai zuwa Turai

    Man fetur

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani bincike da BBC ta gudanar ya nuna cewa Rasha ta samu sama da dala biliyan ashirin da biyar a bara wajen fitar da albarkatun mai zuwa Tarayyar Turai.

    Bayanai sun nuna cewa ya zarce dala biliyan huɗu da Tarayyar Turai ta bai wa Kyiv tallafi.

    A cewar binciken, tun bayan mamayar Moscow shekaru uku da suka wuce, ƙawayen Ukraine sun biya Rasha biliyoyin daloli na man fetur da iskar gas fiye da abun da suka bai wa Kyiv don taimaka mata a yakin.

    Ƙasashen Turai sun rage yawan man da suke saya daga Rasha, sannan ƙungiyar EU na shirin dakatar da shigo da iskar gas daga ƙasar zuwa karshen shekarar 2027.

  19. 'Na rasa ƴan uwana 12 a ambaliyar jihar Neja'

    Ambaliya

    Asalin hoton, Getty Images

    Mutum 12 ƴan gida ɗaya na cikin waɗanda suka rasu sakamakon ambaliya da ta afka wa karamar hukumar Mokwa na jihar Neja.

    Lamarin wanda ya faru a anguwar Tiffin Maza da kuma anguwan Hausawa a ranar Laraba da daddare, ya kuma janyo ɓatan sama da almajirai 50 da lalata gidaje da dama.

    Yawancin waɗanda lamarin ya shafa dai sun kasance mata da yara.

    Duk da cewa hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane 21, amma mazauna yankin sun ce alkaluman za su haura mutum sama da 60.

    Wata mazauniyar yankin, mai suna Hassana Mokwa, ta shaida wa jaridar Daily Trust cewa ƴan uwanta 12 ne lamarin ya rutsa da su, inda mutum ɗaya kaɗai ya samu tsira.

    "Mutum 12 ne suka mutu a gidan ɗan uwana, su 13 ne amma mutum ɗaya ne ya tsira kuma yana ci gaba da samun kulawa a asibiti," in ji Hassana.

    Ta ƙara da cewa: "Almajirai da dama ne kuma suka mutu. Babu wanda ya tsira a gidan da suke zaune kuma ruwa ya tafi da gidan baki-ɗaya. Idan ka je wurin ba za ka taɓa sanin cewa akwai gida a wurin ba kafin ambaliyar.

    Ta kuma ce an yi jana'izar gawawwaki da aka gano a yammacin ranar Alhamis.

  20. Trump ya ce hukuncin kotu na dakatar da lafta haraji na da alaƙa da siyasa

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Trump ya bayyana hukuncin wata kotu na dakatar da harajin da ya laftawa ƙasashen duniya a matsayin abin tsoro, kuskure kuma mai alaka da siyasa.

    A ranar Laraba ne wasu manyan alkalai suka yanke hukuncin cewa Mista Trump ya saɓa wa kundin tsarin mulki wajen sanya harajin.

    Daga bisani ranar Alhamis kotun ɗaukaka kara ta dawo da matakin na sa, yayin da take ci gaba da sauraron karar.

    Da yake jawabi a karon farko a shafukan sada zumunta, shugaban na Amurka ya ce biliyoyin daloli sun fara kwarara Amurka saboda harajin da ya sanya.

    Ya ce hukuncin da alkalan suka yanke zai kassara ikon shugaban ƙasa, don haka ba abu ne da za a lamunta ba.