Msu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo karshen labarai da rahotonnin.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.
A madadin sauran abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.
Tinubu ya karrama Bill Gates da lambar yabo ta CFR
Asalin hoton, STATE HOUSE NG
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya karrama ɗaya daga cikin hamshaƙan attajiran duniya, Bill Gates da lambar yabo ta CFR.
An yi bikin karrama attajirin ne ranar Talata a birnin Legas da ke kudu maso yammacin ƙasar.
Attajirin shi ne mai fitaccen kamfanin fasahar nan na Microsoft da kuma gidauniyar Bill Gates.
A watan da ya gabata ne dai attajirin ya alƙawarta rabar da kashi 99 cikin 100 na dukiyarsa da aka ƙimanta za ta kai dala biliyan 200 ga marasa galihu nan da 2045.
Asalin hoton, STATE HOUSE NG
Asalin hoton, STATE HOUSE NG
Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil-adama na duniya sun yi kiran sakin Moussa Tchangari a Nijar
Asalin hoton, FIDH
A jamhuriyar Nijar, haɗin gwiwar ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa sun fitar da wata sanarwa suna masu cewa dole ne mahukuntan Nijar su gaggauta sakin mai fafutukar kare haƙƙin bil'adama, Moussa Tchangari.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam ɗin da suka haɗa da Amnesty International da Humar Right Watch da FIDH da kuma OMCT sun yi wannan kira ne cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da suka fitar yau Talata inda suka bayyana kamun Moussa Tchangari da ci gaba da tsare shi a matsayin saɓa wa ƙa'ida da dokokin duniya.
Dangwagwarmayar ya shafe wata shida a tsare a hannun hukumomin mulkin sojin na Nijar.
Ƙungiyoyin sun kuma yi kira ga hukumomin mulkin sojin su daina abin da suka kira amfani da tuhume-tuhumen ta'addanci wajen toshe muryoyin da a su yar da da su ba.
ƙungiyoyin sun ce sun yi nazarin tuhume-tuhumen da ake yi wa ɗan gwagwarmayar kuma sun fahimci babu ɗaya daga cikin laifukan da duniya ta amince da su a matsayin laifi, saboda duka suna da alaƙa da yancin faɗin albarkacin baki.
Mallam Isa Sanusi, shugaban ƙungiyar Amnesty a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa abin da hukumomin Nijar ɗin ke yi shi ne ƙoƙarin rufe wa Moussa Tchangari baki da tsorata mutane da hana su amfani da yancin da doka ta ba su na faɗin albarkacin baki.
''Ya kamata a fahimci cewa su masu fafutika ba suna yi ne domin amfanin kansu ba, suna yi domin amfanin jama'a, domin a tabbatar da cewa al'umma ta gyaru'', in ji shi.
A ranar 3 ga watan Disamban 2024 ne dai wasu mutane da ke bayyana kansu a matsayin jami'an yansanda suka kama Moussa Tchangari a gidansa da ke Yamai.
Kuma a ranar 3 ga watan Janairun wannan shekara ne babbar kotun birnin Yamai ta tuhumi ɗan gwagwarmayar da laifuka da dama ciki har da alaƙa da ƙungiyoyin masu aikata ta'addanci da ruguza tsaron ƙasa da makirci ga hukumomin gwamnati.
Almajirai 11 sun mutu bayan ruftawar ƙasa a mahaƙar bulo a Kaduna
Asalin hoton, Kaduna State Pocice Command
Bayanan hoto, Mahaƙar bulon da ke ƙauyen Ƴar-Doka
A Najeriya an yi jana'izar wasu almajirai 11, yayin da wasu bakwai kuma ke kwance a asibiti suna jinya, bayan da ƙasa ta rufta masu a wani kududdufi da ke ƙauyen 'Yar-Doka a ƙaramar hukumar Kubau da ke jihar Kaduna.
Yaran dai 'yan ƙasa da shekara 10 ne, har ma da mai shekara huɗu da haihuwa, kuma rundunar 'yan sandan ƙasar na gudanar da bincike kan lamarin.
Kakakin rundunar ƴansandan jihar ta Kaduna, DSP Mansir Hassan ya shiada wa BBC cewa almajiran sun gamu da ajalin nasu a daidai lokacin da suke haƙar ƙasar bulo a kududdufin.
Ya ce bayan samun bayanin jama'ar gari da jami'an tsaro suka garzaya domin kai ɗaukin gaggawa wajen ceto wadanda ba su mutu ba, tare da tono gawarwakin wadanda suka mutu.
jami'ain ƴansandan ya ce yaran sun ce kududdufin ne domin gina bulo don gyaran gidaje ko katangu ko ma cike wasu wurare.
DSP Mansir Hassan ya yi kira ga iyaye su riƙa sanya idanu kan wurare da ƴaƴansu ke zuwa.
Amurka za ta rage yawan dakarunta a Syria
Jakadan Amurka a Syria Thomas Barrack, ya ce Washinton za ta rage yawan sojojinta a ƙasar.
Mista Barrack ya bayyana haka bayan wata sanarwa a watan Afirilu ta ce ma'aikatar tsaro ta Pentagon za ta rage dakarun ta 2,000, sakamakon raguwar barazana daga ragowar mayaƙan Jihadi.
A watan da ya gabata, shugaba Trump ya sanar da janye dukkan takunkumin da Amurka ta ƙaƙaba wa Syria, watanni 6 bayan ƴan tawaye sun hamɓarar da tsohon shugaba Bashar al-Assad.
Ƴansandan sun hana hawan sallah a Kano
Rundunar ƴansandan jihar Kano tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro a jihar sun ɗauki matakin haramta bukukuwan hawan salla a Kano.
Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴansandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ya ce hukumomin tsaron sun ɗauki matakin ne sakamakon dalilai na tsaro.
Matakin na zuwa ne bayan da wata takarda da aka yi amanna daga fadar Sarki Muhammadu Sanusi II ta fito, ta yi kira da hakimai da su shiga birnin Kano domin gudanar da bukukuwan hawan Sallah.
Ko a lokacin bukukuwan ƙaramar sallah ma hukumomin tsaron jihar sun haramta hawan sallah, saboda bayanan sirrin da suka ce sun samu na wasu ''ɓata-gari'' da ke son amfani da bukukuwan hawan sallar wajen tayar da zauen tsaye a jihar.
''Kan haka ne hukumomin tsaron suka sake ɗaukar matakan haramta hawan babbar sallah , saboda wancan barazanar tsaron har yanzu yana nan'', a cewar sanarwar.
Rundunar ƴansandan ta ce an ɗauki matakin ne bayan tuntuɓar masu ruwa da tsaki kan bayanan sirri da suka samu da ke nuna cewa akwai wasu ɓata-gari da ke shirin amfani da lokacin bikin hawan sallar domin tayar da fitina a jihar.
Isra'ila za ta yi bincike kan kisan Falasɗinawa a wurin rabon tallafi
Asalin hoton, Reuters
Rundunar sojin Isra'ila ta ce za ta binciki rahoton kisan Falasdinawa 27 da aka yi a kusa da cibiyar rabon agaji a tsakiyar Gaza.
Tun da farko Kakakin gwamnatin ƙasar, David Mencer ta musanta cewa dakarun Isra'ila sun hari fararen hula. Inda ya dage cewa wadanda suka mutu a ''waɗanda aka zargi'' ne da suka bijire wa gagaɗi, bayan da suka tunkari sojojin Isra'ila a wani yanayi na ''baranaza''.
Haka kuma Isra'ila ta musanta harbin Falasɗinawa a cibiyar a ranar Lahadi.
To amma Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya sabunta kiran gaggauta gudanar da bincike game da lamarin, tare da wani da ka kai ranar Litinin, wadanda duka suka yi sanadin kisan mutum 60.
Sauyin yanayi da rashin bin ƙa'idar gini ne suka haddasa ambaliyar Mokwa - Gwamnatin Najeriya
Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Najeriya ta ce sauyin yanayi da rashin bin ƙa'idar gine-gine da rashin gyara magunan ruwa ne suka haddasa mummunar ambaliyar da ta auku a garin Mokwa na jihar Neja.
Ministan albarkatun ruwa da tsaftar muhalli na ƙasar, Farfesa Joseph Utsev ne ya bayyana haka a Abuja babban birnin ƙasar, yayin da yake bayani kan ambaliyar da auka wa garin Mokwa na jihar Neja.
Ministan ya ce ba ɓallewar madatwar ruwa ba ce ta haifar da ambaliyar, yana mai alaƙanta matsalar da ƙaruwar tasirin sauyin yanayi, da kuma ruwan sama da ya wuce kima.
Ya ƙara da ce tawagar ƙwararru daga ma'aikatarsa da kuma sauran hukumomi na garin domin auna irin ɓarnar da lamarin ya haifar.
Mista Utsev ya buƙaci gwamnatocin jihohi da masu ruwa da tsaki su riƙa la'akari da gargaɗin da hukumomi ke fitarwa tare da aiwatar da matakan kariya.
Garin Mokwa - mai nisan kilomita 350 daga Abuja, babban birnin ƙasar - ya kasance mahaɗar da ta haɗa ƴankasuwa daga arewaci zuwa kudancin ƙasar.
Fiye da mutum 230 ne suka mutu yayin da ake ci gaba da neman wasu fiye da 400 bayan mummunar ambaliyar da ta auka wa garin.
'Mutum biyar sun mutu bayan hari kan ayarin motocin MDD a Sudan'
Asalin hoton, Reuters
Majalisar Dinkin Duniya ta ce harin da aka kai kan ayarin motocin agaji a arewacin Darfur na ƙasar Sudan ya kashe aƙalla mutum biyar tare da jikkata wasu da dama.
Manyan motoci 15 na kokarin kai kayan abinci zuwa babban birnin El Fasher da aka yi wa kawanya, inda ake fama da yunwa.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce harin ya saɓa wa dokokin duniya.
Gwamnatin Sudan da dakarun sa-kai na RSF sun zargi juna da kai hari kan ayarin motocin na Majalisar Dinkin Duniya.
Bangarororin biyu sun shafe fiye da shekaru biyu suna yaƙi da juna.
El Fasher shi ne birni na ƙarshe a arewacin Darfur wanda har yanzu sojojin Sudan ke iko da shi.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutum miliyan huɗu ne suka tsere daga Sudan tun bayan fara yaƙin.
Ya kamata Najeriya ta gina katanga a kan iyakokinta - CG Musa
Asalin hoton, X/@DHQNigeria
Bayanan hoto, Babban hafsan sojin Najeriya, Janar Christopher Musa
Babban hafsan sojin Najeriya, Janar Christopher Musa ya nuna buƙatar gina katanga a ilahirin iyakokin ƙasar da maƙwaftanta domin kare kwararar masu ɗauke da makami zuwa cikinta.
Yanzu haka dakarun sojin Najeriya na fafutikar ganin sun yaƙi matsalar tsaro da ke addabar ƙasar, musamman rikicin Boko Haram da ƙasar ta kwashe shekara 16 tana fama da shi a arewa maso gabas.
Mayaƙan ƙungiyar - wadda ta samo asali daga kungiyar IS reshen yammacin Afirka - sun kashe jami'an tsaro da dubban fararen hula, yayin da rikicin ya tagayyara miliyoyi.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato Janar Christopher Musa a wani taron tsaro da ke gudana a Abuja yau Talata a Abuja na cewa "kula da kan iyakoki abu ne mai muhimmanci," inda ya bayar da misali da iyakar ƙasar Pakistan mai katangar da ke da tsawon kilomita 1,350 tsakaninta da Afghanistan, da kuma Saudiyya wadda ke da katanga mai tsawon kilomita 1,400 tsakaninta da Iraqi, a matsayin kyawawan misalai.
Wannan ne karon farko da wani babban jami'in gwamnatin Najeriya ke bayar da irin wannan shawara a bainar jama'a.
"Wasu ƙasashen sun yi katanga a kan iyakokinsu sanadiyyar matsalar tsaro," in ji Janar Musa.
Najeriya ta yi iyaka da ƙasashen Nijar da Kamaru da Benin da kuma Chadi, waɗanda dukkaninsu ke fama da rikicin ƴanbindiga.
Hukumomin Najeriya sun sha ɗora laifin matsalar tsaron da ƙasar ke fama da ita a akan kutsen mayaƙa daga ƙasashen ƙetare.
Iyaka mafi tsawo da Najeriya ke da ita da wata ƙasa ita ce tsakaninta da Kamaru ta ɓangaren gabas - mai nisan kilomita 1,975 - yankin da rikicin Boko Haram ya yi katutu.
Sai kuma iyaka mai tsawon kilomita 1,500 da Jamhuriyar Nijar, da kuma iyaka mai tsawon kilomita 80 da ƙasar Chadi, waɗanda dukkaninsu ke fama da matsalar kwararar masu ɗauke da makamai.
Janar Musa ya yi gargaɗin cewa kallon tarin arziki da ake yi wa Najeriya ya sanya kowa ke aniyar kaiwa cikinta. "Kowa Najeriya kawai yake hari. Wannan ne dalilin da ya sa muke buƙatar kare iyakokinmu," in ji shi.
"Wannan na da matuƙar muhimmanci ga wanzuwarmu da kuma ƴancinmu."
Ukraine ta ce ta lalata wata muhimmiyar gada a Rasha
Hukumar tsaro ta Ukraine ta ce kai wa wata gada mai muhimmanci hari da ta haɗa Rasha da yankin Crimea da bamabamai.
Ta ce an jera bamabaman ne masu nauyin kilogiram 1,100 a cikin ruwa na tsawon watanni kuma aka tashe su daga nesa da farar safiyar yau Talata.
Ta yi iƙirarin cewa gimshiƙan gadar aka lalata.
An dakatar da ababen hawa bin hanyar da farko kafin su ci gaba da bi. Amma hukumomi sun sake rufe ta.
Gadar da ake kiran ta Kerch, Rasha ce ta gina ta bayan ta mamaye yankin na Crimea a 2014 daga hannun Ukraine.
Karo na biyu kenan ana kai wa gadar hari tun bayan ɓarkewar yaƙi tsakaninsu a 2022.
Girgizar ƙasa ta kashe mutum ɗaya a Turkiyya
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Girgizar ƙasa da aka yi a watan Fabrairun 2023 ta kashe sama da mutum 53,000 a Turkiyya
Girgizar ƙasa mai ma'aunin 5.8 ta yi sanadiyyar mutuwar mutum ɗaya a yammacin Turkiyya a yau Talata.
Masu yawon buɗe ido a garin Marmaris da ke maƙwabtaka da Tsibirin Rhodes sun ce sun ji motsin ƙasar, wadda ta raunata ƙarin wasu 69.
An ji girgizar a wasu yankuna masu makwabtaka, ciki har da Tsibirin Rhodes da ke ƙasar Girka, wadda ta tashi mutane da daga barcinsu.
Wani mahaifi mai suna Matthew McCormick ya shaida wa kamfanin labarai na PA cewa girgizar ce ta farkar da shi daga barci yayin da suke yawon buɗe ido a tsibirin na Rhodes.
Fursunoni 200 sun tsere daga gidan yarin Pakistan bayan girgizar ƙasa
Asalin hoton, EPA
Sama da fursunoni 200 ne suka tsere daa gidajen yari a Pakistan bayan girgizar ƙasar da auku bayan ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a yau Talata, a cewar 'yansanda.
Dubban fursunoni sun ɓalla ƙofofi da makulla ɗakunansu, sannan suka farfasa tagogi bayan sun ji motsin ƙasar a gidan yarin Malir da ke birnin Karachi.
Daga cikin waɗanda suka gudu, 'yansanda sun ce an sake kama 80, sannan ana ci gaba da neman sama da 130. An kashe fursuna ɗaya a samamen tare da raunata jami'an gidan yari biyu.
Wani gandiroba ya faɗa wa BBC cewa fursunoni sun fara ihu ne daga ɗakunansu tun daga tsakar dare saboda fargabar kada ginin ya rushe.
Najeriya na neman dala biliyan 25 don gina bututun gas zuwa Turai - Shettima
Asalin hoton, @officialSKSM
Najeriya na neman dala biliyan 25 a matsayin kuɗin aikin shimfiɗa bututun gas zuwa nahiyar Turai.
Mataimakin Sugaban Najeriya kashim Shettima ne ya bayyana hakan yayin ganawarsa da shugaban kamfanin Vitol Group a fadar shugaban ƙasa ranar Litinin.
Aikin bututun wanda zai bi ta ƙasar Morocco, za a yi amfani da shi wajen sayar wa ƙasashen Turai iskar gas, yayin da suke yunƙurin rage dogaro da Rasha a fannin makamashi.
Mataimakin shugaban ya nemi masu zuba jari na ƙasashen duniya da su antaya kuɗaɗensu a Najeriya, yana mai cewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu "na aikin saita Najeriya".
Jami'an tsaro sun kama 'yan Saudiyya da zargin safarar mutum 108 zuwa Makkah
Asalin hoton, Saudi Authorities
Dakarun tsaro na aikin Hajj a saudiyya sun kama 'yan ƙasar uku da zargin yin safarar wasu baƙi 'yan ƙasar waje 108 zuwa birnin Makkah domin yin ibadar Hajjin ba tare da izini ba.
Rahoton jaridar Saudi Gazette ya ce mutane sun yi yunƙurin safarar ne ta hanyar wucewa da su a cikin manyan motoci, kuma mutanen na ɗauke ne da bizar ziyara.
A gefe guda kuma, ma'aikatar harkokin cikin gida ta hukunta mutum 17 saboda karya dokokin aikin Hajjin.
Jami'an tsaro sun kama 'yan Saudiyyar 11 da mazauna ƙasar shida yayin da suka yunƙurin shigar da mutum 54 garin Makkah ba tare da takardun izini ba.
Hukuncin da hukumomi suka tanada sun haɗa da ɗauri, da cin tarar riyal 100,000, da kuma bayyana sunayen masu laifin a bainar jama'a.
Waɗanda ba 'yan ƙasa ba kuma, za a iya tasa ƙeyarsu da hana su shiga ƙasar tsawon shekara 10.
Al'ummar Koriya ta Kudu na gudanar da zaɓe domin maye gurbin tsohon shugaban ƙasar, Yoon Suk Yeol, wanda aka tsige.
An tilasta wa Mista Yoon barin mulki bayan ya yi yunƙurin kafa dokar sojin da ba ta samu karɓuwa ba, da haifar da rarrabuwar kawuna.
Kuri'ar jin ra'ayi ta nuna shugaban jam'iyyar Democratic, Lee Jae-Myung, ya sha gaban abokin hamayyarsa na Conservative, Kim Moon-soo, wanda kimar jam'iyyarsa ta zube saboda matakan Mista Yoon.
Wakiliyar BBC ta nuna cewa 'yan Koriya ta Kudu da dama sun gaji, saboda haka wannan kamar wani 'yanci ne da zai kawo karshen yanayin da aka shafe tsawon watanni na rikicin siyasa a ƙasar.
Asalin hoton, Reuters
Falasɗinawa 27 aka kashe a wurin karɓar abinci, in ji ma'aikatar lafiya
Ma'aikatar lafiya ta Zirn Gaza ta ce aƙalla Falasɗinawa 27 aka kashe yayin da suke kan layin karɓar agajin abinci a yau Talata.
Sanarwar da ta fitar ta kuma an raunata wasu 90.
Ta ƙara da cewa cikin waɗanda aka raunata ɗin akwai waɗanda suke cikin mummunan hali.
An kashe sojojin Isra'ila uku a Gaza
Asalin hoton, EPA
Rundunar sojin Isra'ila ta fitar da sunayen dakarunta uku da ta ce an kashe a arewacin Zirin Gaza ranar Litinin.
Mutanen uku da ke da shekaru 20 da ɗoriya sun fito daga bataliya ɗaya - an ce biyu daga ciki likitoci ne, na ukun kuma kwamanda, a cewar wata sanarwa da rundunar sojin ta IDF ta fitar.
Jaridar Times of Israel ta bayar da rahoton cewa an kashe su ne sakamakon wani bam da ya tashi da su lokacin da suke tsaka da fafatawa da mayaƙan ƙungiyar Hamas a yankin Jabalia.
Mutum biyu sun mutu bayan fashewar bam a Uganda
Mutum biyu sun mutu bayan wata fashewa a birnin Kampala na Uganda yayin da ake bikin tunawa da mutanen da suka rasa rayukansu a ƙasar.
Lamarin ya faru ne a kusa da ƙabarin ɗaya daga cikin dakarun, inda dubban mabiya addinin Kirista suka taru.
A cewar rahotonnin kafofin yaɗa labarai a ƙasar, mutanen mace da namiji sun rasu ne lokacin da suke tafiya a kan babur.
Sai dai kuma kakakin rundunar sojin ƙasar, Chris Magezi, ya yi iƙirarin cewa mutanen da suka mutun 'yanta'adda ne da aka kama ɗauke da bamabamai.
An tsaurara tsaro a yankin yayin da miliyoyin mutane ke tururuwar zuwa Namugongo domin bikin ranar da ake kira Martyrs Day.
'Yan sa-kai biyu ne suka mutu a harin da muka kai Zamfara - Sojin Najeriya
Asalin hoton, Nigeria Airforce
Rundunar sojin sama ta Najeirya ta tabbatar da kai hare-hare ta sama a jihar Zamfara da ke arewacin ƙasar, tana mai cewa dakarun sa-kai biyu sun rasu yayin da take harar 'yanfashin daji.
A jiya Litinin ne mazauna ƙaramar hukumar Maru suka shaida wa BBC Hausa cewa jirgin yaƙin sojin ya kashe 'yan sa-kai, yayin da ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International ta ce mayaƙa 20 aka kashe a lokacin da suke bin sawun 'yanbindigar da suka kai musu hari da sace wasu mutane.
Kakakin rundunar Ehimen Ejodame ya ce hare-haren da suka kai bayan samun bayanan sirri sun yi sanadiyyar kashe 'yanbindigar 20.
"A martanin da muka mayar cikin gaggawa ranar 31 ga watan Mayu, dakarunmu sun kashe sama da 'yanta'adda 20 tare da lalata babura fiye da 21," a cewarsa yayin wani taron manema labarai kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
"Abin takaici, yayin wannan aiki ne kuma 'yan sa-kai biyu suka rasa rayukansu kuma wasu biyu suka ji raunuka. Rundunarmu ba ta ji daɗin abin da ya faru ba kan waɗannan jajirtattun mutane kuma muna aiki da hukumomin yankin domin kare rayukan al'umma."
Sai dai har yanzu mazauna yankin na cewa mutanen da suka mutu a hare-haren kuskuren sun zarta mutum biyu kamar yadda rundunar ta bayyana.