'Gazawar gwamnati ke sa wasu jami'an tsaron Najeriya samar da makamai ga 'yanta'adda'

Asalin hoton, NPF
Wasu masana a kan harkokin tsaro na zargin mahukuntan Najeriya da rashin daukar kwararan matakan hukunta jami'an tsaro da ake samu da laifin safarar makamai ga 'yanbindiga da kuma rashin biyan jami'an tsaron kasar albashin da ya dace, da cewa hakan na daga abubuwan da ke janyo baragurbin jami'ai safarar makamai ga mayakan Boko Haram da 'yanfashin daji.
Barista Audu Bulama Bukarti, na daga cikin masu wannan ra'ayi kamar yadda ya bayyana a tattaunawarsa da BBC.
Lauyan kuma masanin harkokin tsaro a nahiyar Afirka, ya ce gwamnatin Najeriya na sakaci da lamuran da suka shafi tsaro da suka hada da rashin bibiyar yadda ake kashe kudade a bangaren da ma yin biris da makomar sojoji da sauran masu aikin samar da tsaro a kasar.
Ya ce muddin hakan ya ci gaba to ba ta yadda za a iya kawo matsalar tsaro da ta addabi Najeriya.
Bulama na magana ne kan rahotannin da ke cewa an kama wasu daga cikin jami'an tsaron Najeriya da ke samar da makamai ga mayakan Boko Haram da kuma 'yan fashin daji.
Ya ce : ''Gaskiya wannan babban abin takaici ne domin ba iya laifi ba ne, cin amanar kasa ne, a ce wanda aka dauka aka dankawa amana aka ba shi makaman al'umma da rigar-sarki shi yake irin wannan.''
''Suna amfani da ofishinsu ta yadda ba za a yi musu dogon bincike ba, to da wannan suke amfani suna irin wannan safarar.'' in ji shi.
Ya kara da cewa, ''su kansu jami'an gwamnati sun yi irin wannan zarge-zarge a baya, kuma wanda ya yi zargin a baya-bayan nan shi ne gwamnan jihar Borno.''
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dangane da rahoton da hukumomin kasar suka bayar na baya-bayan cewa an kama wasu jami'an sojoji suna samar da makamai ga 'ya Boko Haram da 'yanfashin daji, masanin ya ce, bincike ne zai tabbatar su waye da kuma yadda suke samun makaman.
Ya ce idan aka dubi yadda rahoton ya zo, su wadannan jami'ai su suke samar da makaman ga 'yanta'adda, ko dai ta hanyar amfani da haramtattun masu sayar da makamai, suna sayowa ta bayan fage suna kai wa 'yantaddan ko kuma satowa suke yi ta rumbun gwamnati ko kuma sata suke daga abokan aikinsu.
Ko a baya ma shi ma mai bai wa shugaban kasar shawara na musamman kan harkokin tsaro Mallam Nuhu Ribadu ya taba furta cewa a cikin jami'an tsaron akwai masu samar da makamai ga 'yanta'adda.
A kan hakan, Dakta Bulama, ya ce, hakan na nuna cewa lalle tsugune ba ta kare ba a wannan yaki : ''Domin wadanda ya kamata su yaki 'yanbindigan kenan sun juyo suna cin amana, suna yakar kasar.''
Ya ce: ''Tun a baya daman ana ta cewa akwai maciya amana amma za ka ga ba za a sa musu ido a bincika a kama su a hukunta su ba kowa ya gani.''
''Kuma idan aka ci gaba da wannan sai ka dauka to wannan maganar siyasa ce, ko kawai maganar banza ce ko kuma akwai sheda?''
Masanin ya ce kamata ya yi a ce ofishin mai bai wa shugaban kasar shawara kan harkokin tsaron ya bincika irin wannan su fito da hujjoji su hukunta wadanda suka yi abin gano wadanda suka yi abin, da kuma hukuncin da aka yi musu.
Ganin cewa sau da dama sojoji da sauran jami'an tsaro da ke wannan yaki sun dade suna kokawa da rashin biyansu albashi yadda ya kamata da kuma ba su hakkokinsu tare da sama musu kayan aiki sosai da kuma kula lafiyarsu musamman ma idan aka raunata a wajen aiki.
Bukarti ya ce, yana ganin wannan wasarere da ake yi da hakkoki da kuma rayuwar jami'an tsaron da kuma ta iyalansu musamman ma kanana, hakan ka iya sa wasu daga cikinsu masu raunin zuciya sa iya aikata abubuwan da ake zargi da aikatawa, domin su tara kudi.
Domin maganin wannan cin amanar, ya ce kamata ya yi gwamnati ta kara karfafa jami'an tsaron kuma ta sa ido sosai kan kudaden da take cewa tana warewa domin tsaro.
Matsalar tsaron Najeriyar dai kusan ta gagara shawo kanta duk da irin nasarorin da hukumomi ke cewa suna samu a yakin, inda sassa daban-daban na kasar musamman arewaci ke fama da ita iri daban-daban kama daga ta 'yanbindiga da ke satar mutane domin karbar kudin fansa musamman a yankin arewa masu yamma da kuma ta 'yan Boko Haram da ta addabi arewa maso gabas musamman jihar Borno inda a baya-bayan nan take kara kunno kai, take haddasa kisan sojoji da al'umma da kama sake kama garuruwa, wadanda a da aka kwato daga hannunsu.












