Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Labarin wasanni daga 20 zuwa 26 ga watan Satumbar 2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Asabar 13 zuwa 19 ga watan Satumbar 2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. An tashi kurman duro tsakanin Bournemouth da Newcastle

    Bournemouth da Newcastle United sun tashi ba ci a wasan mako na biyar a Premier League ranar Lahadi.

    Hakan ya sa har yanzu Newcastle United ba ta ci wasa a ba a karawar da ta buga a waje da fara kakar nan.

    Koda yake wasa na uku kenan da ƙwallo bai shiga ragar Newcastle ba, sai dai ta yi kasa zuwa ta 13 a kasan teburin Premier League.

    Ita kuwa Bournemouth tana ta huɗun teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da maki 10 iri ɗaya da na Tottenham da kuma Arsenal.

  2. Me kuke son sani kan wasan Man City da Arsenal?

    Arsenal za ta karɓi bakuncin Manchester City a wasan mako na biyar a Premier League ranar Lahadi.

    Arsenal tana mataki na uku a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da maki, tara, bayan cin wasa uku da rashin nasara ɗaya.

    Ita kuwa City tana ta maki 11 da maki shida, bayan nasara biyu aka doke ta wasa biyu.

    A bara da suka fuskanci juna sun tashi 2-2 a Etihad, sai Arsenal ta sharara 5-1 a ragar City a wasa na biyu a Emirates a Premier League.

    Kenan Gunners na fatan doke City karo na biyu a jere a karon farko tun bayan Disambar 2015.

    Kungiyar Emirates ta lashe dukkan wasa ukun da ta buga a gida a bana da cin wallo 9-0.

    Rabon da ta yi nasara huɗu a jere a gida ba tare da an zura mata ƙwallo ba a raga a Premier tun Disambar 2021.

    City ta yi rashin nasara biyar daga wasa bakwai da zarar ta buga gasar zakarun Turai a tsakiyar mako.

    Pep Guariola ya yi rashin nasara huɗu a Premier League a wasa da Arsenal, watakila ya zama karo na biyar ba zai doke Arsenal ba - kenan Mikel Arteta zai zama kociya na farko da zai yi wasa biyar a kan Guradiola ba tare da rashin nasara ba.

    Sai dai Haaland ya ci Arsenal ƙwallo huɗu daga wasa shida da ya fuskanci ƙungiyar a Premier League, sannan ya zura ƙwallo 19 a raga a wasa 20 da suka kai ziyara Landan.

  3. Magoya bayan West Ham sun yi zanga-zanga

    Dubban magoya bayan West Ham United sun yi zanga-zanga da yin kiran shugaban David Sullivan da mataimakiya Karren Brady su yi murabus.

    Sun yi zanga-zangar kafin wasan Premier League da West Ham za ta karɓi bakuncin Crystal Palace ranar Asabar.

    West Ham tana mataki na 18 a kasan teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da maki uku an kuma yi waje da ita a Carabao Cup na bana.

    Dubban magoya baya na ɗauke da ƙyalle da yawa mai sakon da yake ta kiraye-kirayen shugabannin ƙungiyar su ajiye mukaminsu.

  4. Liverpool ta doke Everton a wasan hamayya a Premier League

    Liverpool ta ci wasa na biyar a jere da fara Premier League ta bana, bayan da ta yi nasarar cin Everton 2-1 a wasan hamayya ranar Asabar a Anfield.

    Minti 10 da fara wasa Ryan Gravenberch fara ciwa Liverpool ƙwallo daga baya Hugo Ekitike ya kara na biyu tun kan hutu.

    Daga baya ne Everton ta zare ɗaya ta hannun Iliman Ndiaye a zagaye na biyu.

    Kenan David Moyes ya kasa cin Liverpool a wasa 21 a Anfiled, ya yi canjaras shida aka doke shi 15 daga ciki.

  5. Barkanmu da shiga sharhi da bayanan wasanni

    Jama'a barkanmu da shiga shirin sharhi da bayanan wasanni kai tsaye tare da ni Mohammed Abdu Mamman Skipper Tw.

    Za ku iya tafka muhawara a shirin ko bayar da gudunmuwa a BBCHausa Facebook.