Lamine Yamal shi ne gwarzon matashin ɗan wasa
Lamine Yalam ya lashe Kopa Trophy a matakin matashi mafi ƙwazo ɗan kasa da shekara da shekara 21.
Ɗan wasan Barcelona yana da shekara 18, shi ne ya lashe ƙyautar karo biyu a jere a tarihi.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Asabar 13 zuwa 19 ga watan Satumbar 2025
Mohammed Abdu
Lamine Yalam ya lashe Kopa Trophy a matakin matashi mafi ƙwazo ɗan kasa da shekara da shekara 21.
Ɗan wasan Barcelona yana da shekara 18, shi ne ya lashe ƙyautar karo biyu a jere a tarihi.
Ko za ku iya tuna sayensu? PSG za ta buga wasa da Merseille ranar Litinin a Lique 1.
Mai tsaron ragar tawagar Italiya da Manchester City, Gianluigi Donnarumma ya halarci bikin tare da iayalansa.
Lashe Champions League da Paris St Germain da ya yi, yana cikin takarar mai tsaron raga da ba kamarsa a bara domin lashe, Yashin Trophy.
Ɗan wasan Barcelona, Lamine Yamal, ya halarcin bikin tare da iayalansa, wanda ke cikin takara.
Ronaldo tsohon ɗan wasan Brazil shi ne matashin da ya lashe ƙyautar mai shekara 21 da wata uku a lokacin.
Yamal yana da shekara 18.
Ga jerin ɗin biyar ɗin farko daga mataki na 16 zuwa 20.
16 - Vinicius Jr.
17 - Robert Lewandowski
18 - Scott McTominay
19 - Joao Neves
20 - Lautaro Martinez
Jerin mata dake takara daga mataki na 11 zuwa na 30
11. Claudia Pina (Barcelona, Spain)
12. Marta (Orlando Pride. Brazil)
13. Caroline Graham Hansen (Barcelona, Norway)
14. Barbra Banda (Orlando Pride, Zambia)
15. Sandy Baltimore (Chelsea, France)
16. Cristiana Girelli (Juventus, Italy)
17. Temwa Chawinga (Kansas City, Malawi)
18. Melchie Dumornay (Lyon, Haiti)
19. Klara Buhl (Bayern Munich, Germany)
20. Pernille Harder (Bayern Munich, Denmark)
21. Amanda Gutierres (Palmeiras, Brazil)
22. Esther Gonzalez (Gotham FC, Spain)
23. Johanna Rytting Kaneryd (Chelsea, Sweden)
24. Sofia Cantore (Juventus/Washington Spirit, Italy)
25. Emily Fox (Arsenal, USA)
26. Lindsey Horan Heaps (Lyon, USA)
27. Clara Mateo (Paris FC, France)
27. Frida Leonhardsen Maanum (Arsenal, Norway)
29. Steph Catley (Arsenal, Australia)
30. Caroline Weir (Real Madrid, Scotland)
Tsohon ɗan wasan tawagar Netherlands, Ruud Gullit shi ne zai gabatar da bikin tare da Kate Scott a Theatre du Chatelet a birnin Paris.
Za a fara gudanar da bikin daga karfe 8:00 na dare agogon Najeriya
Ƴan wasan tamaula maza da mata ne za su lashe ƙyautuka a bikin Ballon d'Or
Jerin ƙyautukan da za a lashe a birnin Paris na Faransa.
Masu shirya bikin bayar da kyautar zaratan ƴan ƙwallon duniya ta Ballon d'Or sun bayyana mutane biyar da suka biyo bayan 10 na farko a jerin waɗanda ake sa ran za su lashe kyautar ballon d'Or ta bana.
An bayyana sunayen ne a shafin X na masu shirya bikin bayar da kyautar ranar Litini, inda anjima ake sa ran bayyana wanda zai lashe kyautar.
Ga jerin biyar ɗin na farko bayan manyan ƴan wasa 10 da ake sa ran a cikinsu ne wani zai lashe.
11 - Pedri (Barcelona)
12 - Khvicha Kvaratskhelia (PSG)
13 - Harry Kane (Bayern Munich)
14 - Désiré Doué (PSG)
15 - Viktor Gyökeres (Arsenal)
A bara ɗan wasan Manchester City, Rodri da ƴar ƙwallon Barcelona, Aitana Bonmatí ne suka lashe ƙyautar.
Enzo Maresca na fatan raunin da Cole Palmer ya ji ba zai bukaci tiyata ba, wanda aka sauya shi ranar Asabar a wasan da Manchester United ta doke Chelsea 2-1 a Premier League a Old Trafford.
Ɗan wasan tawagar Ingila, mai shekara 23, an fara wasa da shi karo biyu a fili, wanda ya yi minti 21 a karawar ta ranar Asabar daga baya aka sauya shi.
Da kyar ne idan Palmer zai buga wa Chelsea gasar Carabao Cup da za ta yi da Lincoln ranar Talata, kuma ba a da tantama kan koshin lafiyar Romeo Lavia da Benoit Badiashile.
Maresca zai yi amfani da matasan dake makarantar koyon tamaula ta Chelsea a wasa da Lincoln, wadda take ta uku a kan teburin League One.
Za a yi bikin fitar da gwarzon ɗan ƙwallon kafa na duniya, Ballon d'Or ranar Litinin, sai Real Madrid da Paris St Germain ba za su halarci wajen ba.
Mai rike da kofin Champions League za ta buga ƙwantan wasa da Merseille ranar Litinin, wanda ya kamata su kara ranar Lahadi, amma saboda rashin ƙyawun yanayi aka ɗage karawar.
Ƴan wasa tara ne daga PSG suke cikin yan takara 30.
Watakila Ousmane Dembele da Desire Doue da kuma Joao Neves su halarci bikin, bayan da suke yin jinya.
Sai dai Achraf Hakimi da Khvicha Kvaratskhelia da Nuno Mendes da Fabian Ruiz da Vitinha ba za su je bikin ba, sakamakon suna cikin ƴan wasan da za su buga wa PSG karawa da Merseille.
Wannan shi ne karo na biyu da Real Madrid ba za ta halarci bikin na Ballon d'Or ba.
Ba su halarcin bikin bara ba, inda ɗan wasan Manchester City, Rodri ya lashe ƙyautar da aka sa ran Vinicius Junior ne zai zama gwarzo.
To sai dai dalilin Real Madrid a bana na ƙin zuwa bikin shi ne za ta je gidan Levante a gasar La Liga ranar Talata karawar mako na shida.
A bara ne aka bai wa Real Madrid ƙyautar gwarzuwar ƙungiya, yayin da Carlo Ancelotti ya zama fitatcen kociya.
A bikin Ballon d'Or na bana ƴan wasan Real Madrid uku ne ke takara da ya haɗa da Jude Bellingham da Kylian Mbappe da kuma Vinicius Junior.
Ƴan wasa tara ne daga Paris St Germain ke cikin takarar Ballon d'Or da za a yi ranar Litinin, har da kociya Luis Enrique a matakin kociya mafi ƙwazo.
Daga cikin ƴan wasan sun haɗa da Ousmane Dembele da Gianluigi Donnarumma da Desire Doue da Achraf Hakimi da Khvicha Kvaratskhelia da Nuno Mendes da Joao Neves da Fabian Ruiz da kuma Vitinha daga cikin 30 da za a fitar da gwani don lashe ƙyautar.
Dembele ya ci ƙwallo 35 da bayar da 16 aka zura a raga a dukkan fafatawa a PSG da lashe Ligue 1 da French Cup da kuma Champions League da kai wa wasan karshe a Club World Cup da Chelsea ta lashe.
Sauran sun haɗa da ɗan wasan Barcelona, Raphinha mai ƙwallo 34 da bayar da 25 aka zura a raga da na Liverpool, Mohamed Salah mai ƙwallo 34 a raga da bayar da 23 aka zura a raga, wanda ya zama gwarzon Premier League a kakar da ta wuce da kuma na Manchester City, Erling Haaland mai ƙwallo 34 a raga da bayar da biyar aka zura a raga.
Lamine Yamal na Barcelona ya ci ƙwallo 18 da bayar da 25 aka zura a raga, mai shekara 18 yana kuma takarar Kopa Trophy a matakin fitatcen matashi ɗan kasa da shekara 21, shi ne gwarzon 2024.
Mata biyar ne daga Ingila da suke cikin ƴan takarar Ballon d'Or da ya haɗa da mai tsaron raga, Hannah Hampton da Lucy Bronze da Alessia Russo da Chloe Kelly da kuma Leah Williamson.
Ɗan wasan Barcelona Fermin Lopez zai yi jinyar mako uku, bayan raunin da ya ji a gasar La Liga da suka yi nasarar cin Getafe 3-0 kamar yadda ƙungiyar ta sanar ranar Litinin.
Mai shekara 22, wanda ya ci ƙwallo biyu a karawar da Barcelona ta caskara Valencia 6-0 a watan nan, ya ji raunin ne ranar Lahadi.
Kenan wannan raunin ba zai bai wa Lopez damar buga wa Barcelona Champions League da Paris St Germain ba ranar 1 ga watan Oktoba da wasan La Liga da Barcelona za ta ziyarci Oviedo ranar Alhamis fafatawar mako na shida.
Barcelona tana mataki na biyu a teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya da tazarar maki biyu tsakani da Real Madrid, wadda ta lashe dukkan wasa biyar a jere da fara kakar nana.
Arsenal da Manchester City sun tashi 1-1 a wasan mako na biyar a Premier League da suka kara ranar Lahadi a Emirates.
Erling Haaland ne ya fara cin ƙwallo kuma na biyar da ya zura a ragar Arsenal a wasa na bakwai da ya fuskance ta kuma na 21 a karo na 20 da ya ziyarci ƙungiyar Landan.
Bayan da aka koma zagaye na biyu ne, kuma daf da tashi Gabriel Martinelli ya farke da hakan ta kai suka raba maki a tsakaninsu.
Da wannan sakamkon Arsenal tana mataki na biyu a teburin Premier da maki 10 da tazarar biyar tsakani da Liverpool mai jan ragama.
City kuwa, wadda ta samu maki bakwai tana ta tara a kan teburin babbar gasar tamaula ta Ingila.
Za a buga wasan Olympique Merseille da Paris St Germain ranar Juma'a, bayan da rashin ƙyawun yanayi na hana buga karawar ranar Lahadi.
Masana yanayi ne su yi gargaɗin cewar za a yi mamakon zubar ruwan sama a yankin Alpes-Cote d'Azur, inda birnin Marseille yake
An kuma sanar cewar ruwan zai sauka ne tun daga bakwai na yamma zuwa 10;00 na dare da ake sa ran ƴan kallo 70,000 za su kashe ƙwarkwatar ido a filin wasa na Orange-Velodrome stadium.
Za a buga ƙwantan wasa ranar Litinin, sannan Marseille ta sayar duk wanda ya sayi tikitin kallon wasan, zai iya amfani da shi ranar Litinin.
Matukin motar McLaren, Lando Norris ya rage tazarar maki tsakaninsa da Oscar Piastri zuwa 25, bayan da ya kare a mataki na bakwai Azerbaijan Grand Prix, bayan da ɗan kasar Australia ya ci karo da cikas tun a zangon farko.
Direban Red Bull, Max Verstappen ne ya lashe tseren motocin Formula 1, amma duk da haka akwai tazarar maki 69 tsakaninsa da Piastri, wanda ke jan ragama, kuma saura tsere bakwai a kammala kakar bana.
Mai jan motar Marrsandi, George Russell ya taka rawar gani, wanda yake mataki na biyar amma ya kare a matsayi na biyu, yayin da Carlos Sainz matukin motar Williams ne na uku.
A karon farko Aston Villa ta zura ƙwallo a raga a Premier League a wasan mako na biyar a Premier League, bayan da ta je ta tashi 1-1 a gidan Sunderland ranar Lahadi.
Ƙungiyar da Unai Emery ke jan ragama ita ce tilo da ba ta ci ƙwallo ba daga wasa huɗu da fara Premier ta kakar nan, wadda ta kace zama ta uku da yin wasa biyar a gasar babbar tamaula ta Ingila ba tare da cin ƙwallo ba a tarihi.
Kuma Matty Cash ne ya ci mata ƙwallo a minti na 67 daga yadi na 25.
Sai dai daga baya Sunderland, wadda aka korar mata ɗan wasa ɗaya Reinnildo ta farke ƙwallon ta hannun Granit Xhaka.
Da wannan sakamakon Sunderland ta koma ta bakwai din teburi da maki takwas, ita kuwa Villa ta yi sama zuwa mataki 18, amma har yanzu tana cikin ƴan ukun karshen teburi.
Erling Haaland ya zura ƙwallo a ragar Arsenal a wasan mako na biyar a Premier League da suke buga wa ranar Lahadi a Emirates.
Ƙwallo na biyar kenan da ya zura a ragar Arsenal a wasa na bakwai da ya ke fuskantar ƙungiyar.
Haka kuma na 20 da ya zura a raga a wasa 21 da ya kai ziyara a birnin Landan.
Jose Mourinho ya ci AVS 3-0 a wasan farko da ya ja ragamar Benfica ranar Asabar a gasar tamaula ta Portugal - karo na biyu da yake horar da ƙungiyar.
Benfica ta fara cin ƙwallo ta hannun Heorhiy Sudakov tun kan hutu, bayan da suka koma zagaye na biyu ne Vangelis Pavlidis ya ci na biyu, sannan Franjo Ivanovic ya kara na uku.
Da wannan sakamakon Benfica ta koma ta biyun teburin babbar gasar tamaula ta Portugal da tazarar maki biyar tsakani da Porto mai jan ragama.
Mourinho ya sake karɓar aikin horar da Benfica a karon farko, bayan shekara 25.
Mai shekara 62, wanda ya taɓa horar da Porto ya bar Portugal zuwa Chelsea a 2004, kuma zai fuskanci ƙungiyoyin biyu cikin ƙwana 15.
Mourinho, wanda ya lashe kofi a Real Madrid da Manchester United da Inter Milan da horar da ƙungiyoyi da yawa, Fenerbahce ta kore shi a cikin watan Agusta.
Benfica ta sallami Bruno Lage, saboda rashin nasara da ya yi a hannun Qarabag a Champions League, dalilin da ya sa Mourinho ya maye gurbinsa ranar Alahamis
A jan ragamar Benfica da Mourinho ya yi daga farko wasa bakwai kawai ya yi daga nan ya bar ƙungiyar.