Donnarumma ya ce bai so barin Paris St German ba
Gianluigi Donnarumma ya ce ya so ya ci gaba da zama a Paris St Germain, wanda ya koma taka leda a Manchester City a ranar da aka rufe kasuwar cinikayyar yan kwallo ta Turai ta bana.
Mai shekara 26, wanda ya koma PSG daga AC Milan a 2021 ya taka rawar gani da kungiyar Faransa ta lashe Champions League a karon farko a tarihi a bara.
Shi ne ya karɓi kyautar Yashin Trophy a matakin golan da ba kamarsa a kakar da ta wuce a bikin Ballon d'Or ranar Litinin a Faransa.
Donnarumma, wanda ya lashe Ligue 1 da French Cup da kaiwa wasan karshe a Fifa Club Worl Cup kan fara kakar nan ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka biyar a Etihad har ya tsare mata raga sau biyu, ya kuma ce an yi masa tarbar girma a Etihad.