Gasar Kofin Duniya 2026: Ingila ta kai wasan kusa da ƙarshe bayan doke Norway 1-2

Takaitaccen Bayanin Wasa

Gasar Kofin Duniya
- Zagayen kwata-fainal
Norway 1 , England 2 After extra time
Norway
Ingila
After extra time
Gama Wasa Norway 1 , Ingila 1,Hutun rabin lokaci Norway 1 , Ingila 1

Muhimman abubuwa

Norway

  • A. Schjelderup Goal 36 minutes

Ingila

  • J. Bellingham Goal 45 minutes plus 2, Goal 93 minutes extra time
Ba da ƙwallo a ci
Norway,M. Ødegaard (36 minutes)
Ingila,A. Gordon (45 minutes plus 2)

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi tare da taimakon AI

  1. Ingila za ta je Atlanta, An tashi wasa: Norway 1-2 Ingila

    An ji jiki, amma dai a ƙarshe Ingila ce ta yi nasara.

    Ingila ta je wasan kusa da na ƙarshe a gasar cin kofin duniya karo na huɗu a tarihi, kuma wannan ne na farko tun daga shekarar 2018.

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

  2. An tashi wasa: INGILA TA KAI WASAN KUSA DA ƘARSHE, Norway 1-2 Ingila

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

  3. An ƙara minti biyu, Norway 1-2 Ingila

  4. Odegaard ya ɗauko bugun tazara mai kyau, Norway 1-2 Ingila

    Kyaftin ɗin Norway Martin Odegaard ya ɗauko wani bugun tazara mai kyau zuwa cikin da'irar Ingila amma golan Ingila ya tashi sama ya naushe ta, ta koma cikin fili.

    Sai dai golan ya faɗi ƙasa shame-shame bayan buge ƙwallon.

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

  5. An cire Bellingham, Norway 1-2 Ingila

    Ingila ta sako Dan Burn sannan ta cire Jude Bellingham wanda shi ne ya ci mata duka ƙwallo biyu da ta jefa a ragar Norway a wannan wasa.

  6. An dawo daga hutun rabin ƙarin lokaci, Norway 1-2 Ingila

    Mun shiga falle na ƙarshe a wannan wasa.

    Idan Norway ba ta rama ba shi ke nan an yi waje da ita.

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

  7. An cire Haaland, Norway 1-2 Ingila

    An cire Erling Haaland inda aka sako Jorgen Strand Larsen wanda zai buga minti 15 na ƙarshen ƙarin lokaci.

  8. An tafi hutu, Norway 1-2 Ingila

    An tafi hutu bayan buga ƙwallo ta minti 15 na farko!

    Yanzu za a juya.

  9. , Norway 1-2 Ingila

    Paul Robinson, tsohon mai tsaron ragar Ingila a BBC Radio 5 Live a filin wasa na Miami

    Kocin Ingila Thomas Tuchel ya yi fushi sosai. Ba zai iya gaskanta hukuncin da aka yanke ba, yana ganin cewa babu dalilin da zai sa a soke wannan fenariti da Ingila ta samu.

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

  10. An soke fenariti (VAR), Norway 1-2 Ingila

    Bayan sake dubawa da kyau a na'urar VAR, lafari ya ce babu fenariti, Djed Spence ya faɗi ne ba tare da an masa ƙeta ba.

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

  11. VAR: Lafari na dubawa a na'ura don samun tabbaci, Norway 1-2 Ingila

    Ga yanda abin ya faru:

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

  12. Ingila ta samu bugun fenariti, Norway 1-2 Ingila

    Djed Spence ne ya ratsa ta tsakiyar difendun Norway kuma da alama sun taɓa shi ya tuntsura a cikin dai'irar 18.

  13. , Norway 1-2 Ingila

    Ƙwallon da Jude Bellingham ya ci ta saka shi cikin jerin ƴanwasan da za su iya lashe takalmin zinare.

    Yana da ƙwallo 6.

  14. Ƙwallo a raga: Bellingham ya ƙara cin ƙwallo, Minti na Norway 1-2 Ingila

    Morgan Rogers ne ya shararo wata ƙwallo mai zafi sai Golan Norway ya yi aman ta, shi kuma Jude Bellingham ya mayar da ita cikin raga.

    Ingila sun shiga gaban Norway.

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

  15. An take ƙwallo a ƙarin lokaci, Norway 1-1 Ingila

    Yanzu za a shafa ƙwallo na tsawon minti 30.

    Ko dai a samu ƙasar da za ta ci ko kuma a je fenariti.

  16. Lokaci ya ƙare: Za a je ƙarin lokaci, Norway 1-1 Ingila

    Da alama wankin hula na neman kai waɗannan ƙasashe dare.

    Yanzu lokaci ya cika cif, saboda haka yanzu za a buga ƙarin lokaci, minti 30.

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

  17. 'Odegaard ya zama kanwa uwar gami', Norway 1-1 Ingila

    Alan Shearer, tsohon dan wasan Ingila kuma masanin wasa

    Odegaard ya zama kanwa...uwar gami, yana ko'ina. A duk lokacin da Norway ta ɗauki ƙwallon za ka ga shi ne yake karɓa yana rarraba ta. Shi ne jagora a wannan wasa. Duk wani abu da ka ga Norway ta kitsa ta hannunsa ne.

  18. An ƙara minti 7, Norway 1-1 Ingila

    Minti 90 sun cika cif, amma an ƙara minti 7.

    Ko waɗannan mintuna 7 za su raba gardama?

  19. Saka ya sake kawo wata mai kyau, Norway 1-1 Ingila

    Bukayo Saka ya yi fushi bayan ya yi aiki tuƙuru ya jefo wata ƙwallo mai kyau ta wuce ta gaban golan Norway amma an kasa samun wani da zai tura ta cikin raga.

    Gaskiya ko wane ne dole zai ji haushi.

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

  20. Norway na amfani da damarta, Norway 1-1 Ingila

    Norway na ci gaba da matsa wa Ingila lamba.

    Sun fi kai hare-hare masu haɗari.

    Ingila ba ta kai wani harin a zo a gani ba tun bayan dawowa daga hutu.

    xx

    Asalin hoton, Getty Images