Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da kawo maku rahotannin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 19/10/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Bawage da Abdullahi Bello Diginza

  1. Netanyahu ya zargi Iran da yunƙurin kashe shi

    Netanyahu

    Asalin hoton, AFP

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya zargi Iran da yunƙurin kashe shi da matarsa, bayan harin jirgi maras matuƙin da aka ƙaddamar daga Lebanon zuwa gidan shi.

    Mista Netanyahu ya bayyana harin da babban kuskure, tuni kuma ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon da Iran ke mara wa baya ta ɗauki alhakin kai harin.

    Bangaren Hezbolla sun ƙara faɗaɗa hare-harensu ba kawai farar hula ba, bangaren Isra'ila abin damuwa ne a kai wa mutum mai daraja ta daya a gwamnati hari.

    Tun daga lokacin da aka kai harin, sojojin Isra'ila suka ci gaba da zafafa kai hare-hare ta sama kudancin birnin Beruit, sun ce suna kai harin ne wuraren da mayaƙan Hezbollah ke ɓoye makamai da shalkwatar tsaron sirrin ƙungiyar.

  2. Amnesty ta damu kan sace masu neman mafaka 'yan Turkiyya a Kenya

    Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta ce ta damu matuƙa kan sace wasu masu neman mafaka 'yan Turkiyya a ƙasar Kenya.

    Amnesty ta ce wasu mutane sanye da abin rufe fuska ne suka sace mutanen bakwai a ranar Juma'a.

    Ƙungiyar ta ce tana cike da fargabar ko an kitsa sace mutanen ne tuntuni.

    Daga bisani maharan sun sako uku daga ciki, amma har yanzu huɗu na hannunsu.

    Turkawan mabiya mazhabar Hizmet ne wadda fitaccen malamin nan Fethullah Gulen ke jagoranta, wanda shekaru takwas da suka gabata gwamnatin Turkiyya ta zarga da ƙoƙarin yi wa gwamnati shugaba Racep Tayyep Erdogan juyin mulki.

    Ɗaya daga cikin waɗanda aka saka Necdet Seyitoğlu, ta shaida wa BBC shekararsu biyu kenan da komawa zama a Kenya.

    Kawo yanzu dai hukumomin Kenya ba su ce komai ba game da sace mutanen.

  3. Arsenal ta sha kashi a gidan Bournemouth da ci 2-0

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Bournemouth ta caskara Arsenal da ci 2-0 a wasan mako na takwas a filin wasa na Vitality, inda Arsenal ta ƙare wasan da 'yan wasa 10 a cikin fili, bayan da alƙalin wasa ya bai wa William Saliba jan kati

    An kori ɗan wasan na tawagar Faransa tun kafin a je hutun rabin lokaci.

    Sai a wajen minti na 70 ne ɗan wasan Bournemouth, Ryan Christie ya jefa ƙwallo ta farko a ragar Arsenal bayan da aka ɗauko kwana.

    Saura minti tara a tashi wasan ne kuma Kluivert ya ƙara ta biyu a bugun fenareti bayan golan Arsenal, David Raya ya yi wa Evanilson ƙeta a yadi na 18.

    Da wannan sakamako Arsenal ta yi rashin nasararta ta farko a kakar wasa ta bana, yayin da ita kuma Bournemouth ta kawo ƙarshen rashin nasara huɗu da ta yi a jere, inda ta koma matsayi na 10 a kan teburi da maki 11.

    Wannan sakamako babban koma baya ne ga Arsenal wadda ta rasa dama ɗarewa kan tebur kafin Liverpool ta karɓi bauƙuncin Chelase a gobe Lahadi.

  4. APC ta lashe zaɓen ƙananan hukumomin Kaduna 23 da kansiloli 255

    Gwa

    Asalin hoton, Kaduna Gov/X

    Bayanan hoto, Gwamnan Kaduna, Uba Sani ya yaba da yadda aka gudanar da zaɓen

    Hukumar zaɓen jihar Kaduna ta ayyana jam'iyyar APC mai mulkin jihar a matsayin wadda ta cinye zaɓen duka shugabannin ƙananan hukumomin jihar 23 da kansilolin jihar 255 da aka gudanar yau Asabar.

    Shugabar hukumar zaɓen jihar, Hajiya Hajara Mohammed ce ta bayyana haka a ofishin hukumar ɗazu da maraice.

    Galibi dai dama zaɓukan ƙananan hukumomi jam'iyyun da ke mulkin jihar ne ke lashe duka zaɓukan shugabannin ƙananan hukumomi da na kansiloli.

    Wani abu da masana ke kallo a matsayin barazana ga dimokraɗiyya, sakamakon zargin kura-kurai da ake yi wa zaɓukan.

    To sai dai gwamnan jihar Satana Uba Sani, yayin kaɗa ƙuri'arsa a rumfar zaɓen da ke ƙaramar hukumar Kaduna ta Arewa ya kore wannan zargi, inda ya kira zaɓen jihar a matsayin ''ingantacce kuma sahihi'' da ya gudana ba tare da wata tangarɗa ba.

    A nata ɓangare babbar jam'iyyar hamayyar jihar PDP ta yi iƙirarin rashin gudanar da zaɓen a jihar.

  5. Fashewar taransifoma ce ta haddasa lalacewar babban layin lantarki a Najeriya - NERC

    Lantarki

    Asalin hoton, TCN

    Hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya, NERC, ta ɗora alhakin lalacewar babban layin lantarkin ƙasar kan fashewar wata taransifoma a tashar rarraba lantarki ta Jebba.

    Da safiyar ranar Asabar ne mafiya yawan sassan ƙasar suka fuskanci ɗaukewar wutar lantarki, karo na uku cikin mako guda.

    Cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta ce ta damu matuƙa kan halin da aka shiga na lalacewar babban layin lantarkin.

    ''Daga bayanan da muka samu, mun gano cewa matsalar da aka samu yau, ta faru ne sakamakon fashewar wata taransifoma a tashar rarraba lantarki ta Jebba, wannan shi ne dalilin da ya haddasa lalacewar babban layin wuta'', kamar yadda sanarwar ta bayyana.

    Hukumar ta kuma ce jami'anta na can suna aiki ba ƙaƙƙautawa don ganin sun gyara komai, domin mayar da wutar, ba tare da ɗaukar dogon lokaci ba.

  6. Kusan mutum 20,000 ne suka tsere daga Jabalia a ranar Juma'a - MDD

    Hukumar kula da ƴan gudun Hijirar Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya, (UNWRA) ta ce aƙalla mutum 20,000 ne suka tsere daga birnin Jabalia na Gaza a ranar Juma'a.

    "Mutane sun rasa komai. Suna buƙatar taimako da ya ƙunshi abinci da ruwa da mayafai da kuma wurin kwanciya," in ji babban kwamishinan hukumar ta UNWRA Philippe Lazzarini a wani sako da ya wallafa a shafin X.

    Ya kuma ruwaito cewa ana ci gaba da fuskantar ƙarancin man fetur da magunguna musamman a asibitoci.

    "Lokaci ya yi da za a kawo ƙarshen yaƙin nan," in ji shi.

  7. Gwamnan Jigawa ya dakatar da kwamishinansa kan zargin lalata da matar aure

    Jigawa

    Asalin hoton, Gwamnatin Jigawa

    Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi ya dakatar da kwamishinan ayyuka na musamman, Auwalu Danladi Sankara bisa zargin da hukumar Hisba ta jihar Kano ta yi masa na ''lalata da wata matar aure''.

    Cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Malam Bala Ibrahim, ya fitar ya ce an ɗauki matakin ne domin samun damar gudanar da cikakken bincike kan zargin da ake yi wa kwamishinan.

    Ya ce za a gudanar da bincike domin tabbatar da gaskiya da kuma kare martabar gwamnatin jihar.

    A ranar juma'a ne dai hukumar Hisba ta jihar Kano ta fitar da sanarwar kama kwamishinan bisa zarginsa da mu'amala da matar aure a wani gida da ba a kammala ba, a jihar Kano.

    "Muna ɗaukar duka zarge-zargen da muhimmanci kuma za mu yi bincike da nufin fito da gaskiya domin duka ƴan jihar Jigawa su gani," in ji sakataren gwamnatin jihar.

    Ya kuma ce an ɗauki matakin dakatar da kwamishinan ne domin yin sahihin bincike da kuma yin adalci ga kowane ɓangare.

    Sanarwar da gwamnatin ta fitar, ta ce abin kunya ne abin da ake zargin kwamishinan da aikatawa kuma cin fuska gare ta.

    Tuni kuma gwamnatin jihar ta kafa wani kwamiti mai mambobi huɗu waɗanda za su yi bincike da kuma gabatar da rahoto cikin mako biyu kacal.

  8. 'Waɗanda suka mutu a Gaza ya kai 42,519

    Ma'aikatar lafiya karkashin ikon Isra'ila a Gaza, ta ce an kashe mutum 19 tare da jikkata wasu 91 a cikin sa'o'i 24 da suka wuce.

    A wani sabon bayani da ma'aikatar ta fitar, ta ce aƙalla Falasɗinawa 42,519 ne aka kashe sannan aka jikata 99,637 tun bayan da Isra'ila ta soma kai hare-hare Gaza bayan harin ranar 7 ga watan Oktoba da Hamas ta kai mata.

  9. An harba rokoki sama da 50 zuwa Isra'ila daga Lebanon

    Isra'ila

    Asalin hoton, EPA

    Sojojin Isra'ila sun ce an harba rokoki 55 zuwa Haifa da wasu birane da ke arewacin ƙasar daga Lebanon.

    A wata sanarwa, dakarun tsaron ƙasar sun ƙara da cewa an samu nasarar kakkaɓo wasu daga cikin rokoki.

    Ma'aikatar lafiya ta Isra'ila Magen Adom, ta ce wani mutum mai shekara 29 ya samu raunuka, yayin da wani ma ya jikata bayan da harin roka ya faɗa kan wani gida a yankin Haifa.

    A ɗaya ɓangaren, Hezbollah ta ce ta harba gomman rokoki zuwa wani sansanin sojin a birnin Haifa, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.

  10. 'Mun ɓullo da sabbin tsare-tsaren inganta samar da wutar lantarki'

    Hukumar kula da harkokin samar da makamashi ta Najeriya, wato Energy Commission Of Nigeria, ta ce ta yunkuro a ƙoƙarin kawo sauyi game da yadda ake sama wa al'ummar ƙasar wutar lantarki.

    Hukumar ta ce ta ɓullo da wasu sabbin tsare-tsare da za su inganta hanyoyin samar da wutar lantarkin, waɗanda suka haɗa da hasken rana da iska da sauransu.

    Shugaban hukumar, Dokta Mustafa Abdullahi, ya ce Najeriya na samar da megawatt 12,000 na wutar lantarki, amma 5,000 kaɗai ke isa ga gidajen mutane.

    Ya ce ana buƙatar megawatt 40,000 na wutar lantarki kafin ta isa al'ummar Najeriya.

    Bayanan bidiyo, Latsa sama don kallon bidiyon
  11. Hamas za ta ci gaba da wanzuwa - Ayatollah

    Ayatollah

    Asalin hoton, EPA

    Jagoran addini na ƙasar Iran Ayatollah Ali Khamenei ya ce "Hamas ba za ta mutu ba za ta ci gaba da wanzuwa" duk da kashe shugabanta,Yahya Sinwar.

    An kashe Sinwar, wanda ya jagoranci kai hari Isra'ila ranar 7 ga Oktoba a wani hari da dakarun Isra'ila suka kai kan wani giri a birnin Rafah a farkon makon nan.

    "Rashinsa na da matukar raɗaɗi, sai dai hakan ba zai sa gwiwar Hamas ta karaya ba," in ji Khamenei.

    Ƙungiyoyi da Iran ke mara wa baya dai sun haɗa da ƙungiyar Hamas, da Hezbollah, da kuma wasu ƙungiyoyi a faɗin Gabas Ta Tsakiya waɗanda suka sha far wa Isra'ila.

    "Shi jajirtaccen mutum ne wanda ya yi aiki tukuru. Ya tsaya kai da fata ya kuma yi faɗa da makiya da dukkan karfinsa," a cewar Khamenei.

  12. Isra'ila ta ce ta kashe wani kwamandan Hezbollah a kudancin Lebanon

    Sojojin Isra'ila sun ce sun ce dakarunta sun kashe wani mataimakin kwamadan Hezbollah a yankin Bint Jbeil da ke kudancin Lebanon.

    Dakarun tsaron ƙasar (IDF), sun ce Naser Abed al-Aziz Rashid na da hannu a kai hare-hare da dama kan Isra'ilawa.

    Hezbollah ba ta ce uffan kan lamarin ba.

  13. Hotuna daga wajen ɗaurin auren ɗiyar abokin aikinmu Mohammed Abdu

    A safiyar yau Asabar 19 ga watan Oktoban ne aka ɗaura auren ɗiyar abokin aikinmu Mohammed Abdu Mamman Skeeper, wato Asma'u Mohammed Abdu wadda aka fi sani da Walida tare da angonta Abdulkadir Musa (Abba).

    An ɗaura auren ne a Masallacin Imam Nura da ke Tudun Wada a karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano.

    Ga wasu daga cikin hotunan abokan aikinmu a wajen ɗaurin aure.

    Kano
    Bayanan hoto, Nan Mohammed Abdu ne (daga ɓangaren dama) tare da sauran abokan aiki Yusuf Tijjani da kuma Zahraddeen Lawal
    Kano
    Bayanan hoto, Lokacin da ake ɗaura auren
    Kano
    Bayanan hoto, Wasu daga cikin ma'aikatan BBC a wajen ɗaurin auren da suka kunshi Zahraddeen Lawan, Yusuf Tijjani, Mohammed Abdu da Lawal Nuhu Sulaiman
    Kano
    Bayanan hoto, Ma'aikatan BBC tare da sauran mutane da suka halarci ɗaurin auren
    Kano
  14. Aƙalla mutum 11 aka kashe a wasu hare-hare a tsakiyar Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, EPA

    Aƙalla mutum 11 ne aka ruwaito mutuwarsu a wani hari da Isra'ila ta kai wani gida a sansanin ƴan gudun hijira na al-Maghazi da ke tsakiyar Gaza, a cewar kamfanin dillancin labarai na Falasɗinawa Wafa.

    Jami'an lafiya sun ce an kuma jikkata wasu da dama yayin da yawa ke karkashin ɓaraguzai, in ji Wafa.

  15. An kai harin jirgi mara matuki gidan Firaiministan Isra'ila

    Isra'ila

    Asalin hoton, Reuters

    An kai harin jirgi mara matuki kan gidan Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a Caesarea, da ke arewacin Isra'ila, a cewar mai magana da yawunsa.

    Netanyahu ba ya cikin gidan lokacin da aka kai harin babu kuma wanda ya jikkata, in ji kakakin nasa.

    Tun da farko, sojojin Isra'ila sun ce an kai harin jirage mara matuki guda uku zuwa garin a safiyar yau Asabar.

    Ta ce ɗaya daga cikin jiragen ya lalata wani gini, yayin da aka kakkaɓe guda biyu.

  16. Babban layin wuta na ƙasa ya sake lalacewa, sau uku cikin mako ɗaya

    Wutar lantarki

    Asalin hoton, TCN

    Najeriya ta sake fuskantar katsewar wutar lantarki sakamakon lalacewar babban layin lantarki na ƙasar a safiyar yau Asabar.

    Lamarin da ya jefa miliyoyin mutane a jihohi da dama cikin duhu.

    Wannan dai shi ne karo na uku da babban layin wutar ke lalacewa cikin mako ɗaya, kuma na takwas tun soma wannan shekara.

    Bayanai daga aka tattara sun nuna cewa babu ko megawatt ɗaya a babban layin zuwa safiyar Asabar ɗin nan.

    Masana kan harkar wutar lantarki dai sun yi kira da a sabunta kayayakin babbar cibiyar wutar lantaki ta ƙasar.

    Sun ce yawan katsewar wutar lantarkin da ake fuskanta na da alaƙa ne da rashin sauya kayyakin babbar cibiyar wutar lantakin ƙasar.

  17. Harris da Trump sun yi musayar yawu kan wanda ya fi koshin lafiya a Michigan

    Harris and Trump

    Asalin hoton, Reuters

    Yayin da gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban Amurka ya ɗauki zafi sosai, manyan yan takara a zaɓen Donald Trumo da Kamala Harris, sun yi musayar yawu kan wanda ya fi koshin lafiyar gudanar da mulki idan ya samu nasara.

    Dukkansu sun yi yaƙin neman zaɓe nesa kaɗan da juna a jihar Michigan, ɗaya daga cikin jihohin da za a kai ruwa rana a kansu.

    Ta bayyana abokin burminta Mista Trump a matsayin gajiyayye, yayin da shi kuma ya bayyana ta a matsayin wadda ta riga rana faɗuwa.

    Sakamakon kuri'un jin ra'ayin jama'a na ci gaba da nuna yadda yan takarar ke tafiya kan-kan-kan babu tazara.

  18. An kama mutumin da ke yi wa ƴan sanda sojan-gona a Kano

    Kano

    Asalin hoton, Abdullahi Kiyawa/FB

    Rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta ce ta kama wani mutum da ke yin sojan-gona inda yake cutar al'umma.

    Mai magana da yawun rundunar a jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.

    SP Abdullahi ya ce an kama mutumin bayan samun korafe-korafe daga mazauna Fagge da Sabon Gari da Koki da kuma kwaryar birnin Kano, inda suka ce mutumin yana amfani da matsayin jami'in ɗan sanda wajen karɓar kuɗaɗe a hannunsu.

    "Mun kama mutumin ne mai suna Salisu Bala mai shekara 31 ranar 14 ga watan Oktoba a Kurna Qaurters sanye da kakin ƴansanda inda yake aikata ba daidai ba," in ji Kiyawa.

    Ya ce binciken farko da suka fara yi ya nuna cewa mutumin ba shi da alaƙa da ƴansanda ko kuma wata hukuma ta tsaro, kawai yana sojan-gona wajen karɓar kuɗaɗen mutane.

    Kakakin ƴansanda ya ce sun kuma gano kakin ƴansanda har kala huɗu a gidan mutumin.

    Kwamishinan ƴansandan jiihar ta Kano, CP Salman Dogo Garba ya ce ba za su lamunci yi musu sojan-gona ba ko kuma wani ya riƙa karɓar kuɗi a hannun mutane tare da sunan jami'in ɗansanda, inda ya ce za su ci gaba da ɗaukar matakai na kare al'umma daga irin waɗannan mutane.

  19. 'Shugaban Hamas ya mutu ne sakamakon harbin bindiga a ka'

    Yahya Sinwar

    Asalin hoton, Getty Images

    Likitan Isra'ilar da ya jagoranci gudanar da bincike kan gawar shugaban Hamas Yahya Sinwar, ya ce ya mutu ne sakamakon harbin bindiga a ka.

    Da yake magana da kafafen watsa labaran Amurka, Dr Chen Kugel, ya ce ya gano raunuka a wasu sassan jikinsa, ciki har da kafaɗarsa, wanda ya ji sakamakon samunsa da kwanson maƙami mai linzami ya yi.

    Ya ce waɗannan raunuka sun matukar illata shi sosai, sai dai abun da ya janyo ajalinsa shi ne harbin da aka masa a ka.

    Da farko dai rundunar sojin Isra'ila ta ce Yahya Sinwar ya mutu ne sakamakon harbin gidan da yake ciki da tankar yaƙin sojoji ta yi.

  20. Harin Isra'ila ya kashe gomman mutane a Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, Getty Images

    An sanar da mutuwar mutane da dama a wani sabon hari da jiragen yaƙin Isra'ila suka kai kan sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia da ke arewacin Gaza.

    Hukumar kare fararen hula ta Gaza ta ce mutane 33 ne suka mutu sannan wasu da dama suka jikkata.

    Babu wani martani daga Isra'ila.

    A makonnin baya-bayan nan rundunar sojin Isra'ila ta zafafa hare-harenta a arewacin Gaza, musamman a sansanin yan gudun hijira na Jabalia, inda take zargin mayaƙan Hamas na ɓoye.

    A farkon wannan watan ne ta ba da umarnin kwashe dubban ɗaruruwan mutane daga yankin, inda ta ce su koma kudu, sai dai da yawa daga cikinsu sun ki tafiya, saboda fargabar hakan wani shiri ne na korarsu daga wurarensu, abun nan da ake cewa Nakba.