Yadda Isra'ila ta gano tare da kashe Yahya Sinwar

Yahya Sinwar a shekarar 2022 lokacin da yake gabatar da jawabi a watan Ramadan a birnin Gaza

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sama da shekara ɗaya ke nan Isra'ila na farautar Sinwar
    • Marubuci, Graeme Baker
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Dakarun sojin Isra'ila sun shafe sama da shekara guda suna farautar shugaban ƙungiyar Hamas, wanda aka daina ganinsa a zirin Gaza kwanaki kaɗanda bayan ya kitsa kai harin 7 ga watan Oktobar bara.

Yahya Sinwar mai shekara 61, yana rayuwa a cikin hanyoyin ƙarƙashin ƙasa tare da masu tsaron lafiyarsa da kuma yin shinge da ƴan Isra'ila da ƙungiyar Hamas ta yi garkuwa da su lokacin da ta kai harin na bara.

Sai dai ya gamu da ajalinsa a wata dama da sojin Isra'ilar suka samu, lokacin sintirin da suke yi a kudancin zirin Gaza. Babu wani cikakken bayani kan tsirarun masu tsaron lafiyarsa, sannan ba a gan shi tare da ko ɗaya daga cikin waɗanda a kai garkuwar da su ba.

Bayanan yadda ya gamu da ajalinsa na ƙara fitowa, kuma ga kaɗan daga cikin abin da muka sani game da lokacinsa na ƙarshe a duniya.

Kwamandojin sojin Isra'ila lokacin da suka kai ziyara ginin da aka kashe Yahya Sinwar

Asalin hoton, IDF

Bayanan hoto, Kwamandojin sojin Isra'ila lokacin da suka kai ziyara ginin da aka kashe Yahya Sinwar

Sintirin da aka saba

Rundunar tsaron Isra'ila, ta ce dakarunta na Birgade 828 sun yi sintiri a yankn Tal al-Sultan da ke birnin Rafah a ranar Laraba.

An gano wasu mahara uku, aka kuma fara musayar wuta tsakaninsu daga bisani sojin Isra'ilar sukai nasarar kashe su.

A wanna lokacin babu wanda ya yi tunanin akwai wani mutum mai matuƙar muhimmanci da Isra'ila ke nema ruwa a jallo, sojojin ba su dawo wurin ba har sai da gari ya waye ranar Alhamis.

A wannan lokacin babu wani abu da ya musu daɗi, ba su damu da lallai sai sun duba domin gano waɗanda suka kashe ba, sa dai gawar ɗaya daga cikinsu ta ɗauki hankalin sojin na Isra'ila, inda suka ga fuskar ta yi kama da ta shugaban Hamas Yahya Sinwar.

Duk da hakan ba su yi ƙoƙarin ɗauke gawar ba, a nan suka bar ta saboda tunanin wataƙila wani tarko ne aka ɗana musu, maimakon ɗaukar gawar sai suka yanki wani ɓangare na ɗan yatsan gawar domin tura wa Isra'ila a yi gwajin ƙwayar halitta.

Daga bisani an ɗauke gawar zuwa Isra'ila, bayan tabbatar da yankin ya samu cikakken tsaro.

Mai magana da yawun rundunar tsaron Isra'ila Daniel Hagari, ya ce dakarunsu ba su san Sinwar na wurin ba, kawai dai sun ci gaba da gudanar da aikinsu ne.

Sun bayyana cewa mutumin da aka kira da suna Sinwar ''ya ruga cikin ginin lokacin da suka fara musayar wuta''. Bayan jirgi maras matuƙi mai ɗaukar hoto ya gano inda yake a cikin ginin, sai aka kashe shi ta hanyar luguen wuta a ginin.

Hoton farko na ginin da aka kashe shugaban Hamas Yahya Sinwar, an ɗauki hotunan ta tauraron ɗan-adam, da ya nuna ginin da ke Tal al-Sultan a yankin birnin Rafah da ke zirin Gaza.
Hoto na biyu ya nuna yadda wani mutum ya ruga cikin ginin, daga bisani an gano Yahya Sinwar ne. Hoton da ke ƙasa ya nuna rusasshen ginin da aka yi wa ruwan makamai, ana iya ganin tagogin da suka lalace, kuma a hawa na farko na ginin jirgi maras matuƙin ya shiga.

Ɗayan hoton da aka kewaye mai zanen surar mutum zaune kan kujera, shi ne daga bisani aka gano Sinwar ne a zaune kafin a hallaka shi.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An gano gawar Sinwar sanye da rigar kariya daga harsashi, da bindiga, da kuma kuɗin ƙasar shekel 40,000.

Babu ko ɗaya daga cikin waɗanda a ka yi garkuwa da su da aka yi amanna Sinwar na yawo da su a matsayin makami ba a lokacin da aka yi musayar wutar da zuwa ɗauke gawarsa.

Sojojin Isra'ila sun yi hasasshen yana tare da tsirarun masu ba su kariya, a matsayin baɗɗa kama ta yadda zai riƙa yawo ba tare da an gane shi ba, ko kuma an kashe yawancin masu tsaron lafiyarsa.

Hagari ya ƙara da cewa, makonni shida da suka gabata sojoji suka samu ƙwayoyin halittar Sinwar a wani ramin ƙarƙashin ƙasa da aka gano gawar ƴan Isra'ila nan 6 da Hamas ta yi garkuwa da su.

A yanzu sojojin Isra'ilar sun fara neman ɗan uwan Sinwar, Muhammad Sinwar da sauran kwamandojin ƙungiyar Hamas.

Ministan tsaron Isra'ila Yoav Gallant, ya ce: "Sinwar ya gamu da ajalinsa bayan an rauna ta shi, mutuwar Sinwar babban saƙo ne ga maƙiyanmu."

Hotuna da bidiyon jirgi maras matuƙi da sojin Isra'ila suka fitar, da aka ɗauka ta jikin wata tagar ginin da aka lalata, an ga Yahya Sinwar zaune akan wata kujera a falon da aka ɗaiɗaita komai da ke cikinsa, jirgin ya ci gaba da matsawa inda mutumin yake zaune a kan kujera da fuskarsa a rufe da rawanin da Falasɗinawa ke rufe kai ko fuska da shi. Mutumin wanda ya nuna an ji masa rauni, ya na riƙe da wani abu mai kama da katako a hannu, ya kuma yi jifa da ta ɓangaren da jirgin ke ɗaukar bidiyon, an yi amanna wannan ne hoto na ƙarshe na Yahya Sinwar a lokacin da yake raye.

Bayanan bidiyo, Bidiyon da dakarun tsaron sra'ila suka fitar na lokacin karshe na rayuwar Yahya Sinwar

Mun 'halaka' Sinwar

Da farko Isra'ila ta sanar da cewa ta na "binciken tabbatar da kashe" Sinwar a Gaza ne a ranar Alhamis.

Bayan wasu ƴan mintuna da sanarwar, sai aka fara yaɗa wasu hotuna na gawar wani mutum, wanda ya yi kama da shugaban na Hamas. Ba za a iya wallafa hotunan ba saboda da muni.

Daga baya kuma, sai wata majiya daga Isra'ila ta shaida wa BBC cewa shugabannin ƙasar "su na ta ƙara samun tabbacin" kashe shi, inda a lokacin su ka ce ba za su tabbatar ba sai sun gudanar da wasu gwaje-gwaje.

Gwaje-gwajen ba su ɗauki lokaci. Da yammacin ranar Alhamis, sai Isra'ila ta tabbatar da kashe Sinwar ɗin.

Firai ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya fito ya ce, duk da kashe Sinwar ɗin, akwai sauran yaƙin a Gaza.

Sojojin Isra'ila suna sintiri a garin Rafah cike da baraguzai a watan Satumban 2024.

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto, Sojojin Isra'ila suna sintiri a garin Rafah cike da baraguzai a watan Satumban 2024

Matsa masa lamba

Kasancewar ba wai an kashe Sinwar ba ne a harin kai-tsaye da aka kai masa, IDF ta ce sun ɗauki makonni suna luguden a yankunan da suka samu bayanan sirrin cewa wataƙila yana zaune a wuraren.

A taƙaice dakarun Isra'ila sun mayar da hankalin neman Sinwar ne a kudancin Rafah, inda suka bi a hankali wajen farautarsa.

Kusan shekara ɗaya ke nan suna farautarsa. Da alama ya gane sojojin suna bibiyarsa bayan an kashe sauran jagororin Hamas irin su Mohammad Dief da Ismail Haniyeh, sannan an tarwatsa kayayyakin da suka yi amfani da su wajen kai hare-haren na 7 ga Oktoba.

A wata sanarwa, IDF ta ce aikace-aikacenta a kudancin ƙasar a cikin ƴan makonnin da suka gabata ne "suka hana Sinwar sakat saboda sojojin suna bibiyarsa. Wanda hakan ya sa aka cimmasa, har aka kashe shi."

Motoci a birnin Tel Aviv suna wucewa da wani babban banar Sinwar, inda a jiki a rubuta da harshen Hebrew cewa mutanen Isra'ila su haɗa kai wajen neman babban maƙiyinsu.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Motoci a birnin Tel Aviv suna wucewa ta wani babban banar Sinwar, inda a jiki a rubuta da harshen Hebrew cewa mutanen Isra'ila su haɗa kai wajen neman babban maƙiyinsu.

Babban burinsu, amma ba ƙarshen yaƙin ba

Kashe Sinwar na cikin manyan burukan Isra'ila, bayan ta ayyana nemansa ruwa a jallo tun bayan hare-haren na 7 ga Oktoba. Amma kisan ba zai zama ƙarshen yaƙin Gaza ba.

A ranar Juma'a, wani mamba a cikin ɓangaren siyasar Hamas, Basem Naim, ya bayyana a wata sanarwa cewa "Isra'ila na tunanin kashe jagoranmu ne zai kawo ƙarshen fafutikarmu da ta mutanen Falasɗinu," inda ya ƙara da cewa ba za a iya ƙashe fafutikar Hamas ba.

Na'im bai bayyana sunan Sinwar ba kai tsaye ko kuma ya tabbatar da mutuwarsa, amma ya ce, "akwai takaici mutum ya rasa waɗanda yake so."

Shi ma Netanyahu ya ce duk da ya samu nasarar da yake so, amma ya nanata cewa zai cigaba da yaƙi - har sai Hamas sun saki mutum 101 da suka yi garkuwa da su a Isra'ila.

A Isra'ila, iyalan waɗanda aka yi garkuwa da su ɗin suna fatan a tsagaita wuta a yanzu domin ƴanuwansu su dawo gida.