Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, A'isha Babangida, Usman Minjibir, Umar Mikail and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Ƙasashen Afirka sun nemi Iran da Isra'ila su kai zuciya nesa

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Ƙasashen Afirka da dama sun yi kira ga Isra'ila ta kai zuciya nesa yayin da kwamitin shirya yaƙinta ke tattaunawa domin yanke hukuncin ko za su kai harin ramuwar gayya sakamakon harin ba-zata da Iran ta kai mata ranar Asabar da daddare.

    Iran ta ce ta kai harin ne a matsayin martani ga hari ta sama da Isra'ila ta kai kan ofishin jakadancinta da ke Damascus ranar 1 ga watan Afrilu wanda ya kashe mata dakarun juyin juya hali.

    Iran ta kai hari da fiye da jirage marasa matuƙa 300 da makamai masu linzami - galibinsu kuma an daƙile su kamar yadda sojojin Isra'ila suka bayyana.

    Najeriya da Kenya da Afirka ta Kudu da Somalia ƙasashen Afirka ne da suka yi kiran a kai zuciya nesa domin hana ɓarkewar yaƙi.

    Cikin wata sanarwa, sashen da ke kula da haɗin kai da alaƙar ƙasashen waje a Afirka ta Kudu ya ce "dole ne duka ɓangarorin su danne zuciyarsu sannan su guji matakin da zai janyo tashin hankali musamman a yankin da ke fama da rikici".

    Shugaban Kenya, William Ruto ya buƙaci Isra'ila ta yi haƙuri ganin buƙatar duka ɓangarorin su kaucewa tsunduma yaƙi da za a yi wuyar farfaɗowa."

    Ya ce harin da Iran ta kai ya nuna barazana ga tsaro da zaman lafiyar duniya.

    Somaliya ta yi kira ga al'ummar duniya da su ɗauki mataki na sassauta rikicin tare da rage haɗarin faɗa wa tashin hankali."

    Ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ta yi kira ga Isra'ila da Iran da su yi tunani kan alƙawarinsu ga ƙudurorin zaman lafiya".

    Iran da Isra'ila ba su da wata alaƙar siyasa mai zurfi a yankin kudu da hamadar Sahara.

    • Hankalin duniya ya karkata kan martanin da Isra'ila za ta mayar wa Iran
  2. Shin wa ya fi ƙarfi tsakanin Iran da isra'ila?

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Wakilin BBC kan harkokin yaki, Jonathan Beale ya amsa wannan tambaya kamar haka:

    Da farko dai Iran ta ninninka Isra'ila a girman kasa da yawan al'umma, inda Iran take da yawan jama'a kusan miliyan 90 kusan ta ninka Isra'ila sau 10 - to sai dai hakan ba ya nufin karfin soji.

    Kasar Iran ta dade tana kashe kudade masu yawa wajen samar da makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuka. Tana da makamai masu yawa sannan kuma tana bai wa makaman masu tarin yawa ga kungiyoyin Houthi da ke Yamen da na Hezbollah da ke Lebanon.

    To sai dai abin da Iran din ta rasa a yanzu shi ne kariyar sararin samaniya na zamani da kuma jiragen yaki. Sai dai kuma an yi yakinin cewa kasar Rasha na tare da Iran din wurin samar da wadannan abubuwan, a wani yanayi ya sakayya da Iran din bisa taimakon sojin da ta bai wa Rasha a yakin da take yi da Ukraine ta hanyar amfani da jirage marasa matuka na kunar bakin wake da rahotanni ke cewa yanzu haka su ma Rasha suna kera irin jiragen.

    Isra'ila na da daya daga cikin kasashe da suke da karfi sojin sama fiye da ko'ina a duniya. Cibiyar ISSS ta ce Isra'ila na da akalla tawagar jiragen yaki 14 da suka hada da F15,F16 and F-35.

    Isra'ila kuma na da gogewar kai hare-hare zuwa cikin kasashen da suke yaki da su.

    • Iran ta kaddamar da hari kan Isra’ila
    • Isra’ila ta ce ta dakile harin da Iran ta kai mata
  3. NLC ta nemi sabon albashi mafi ƙaranci ga ma'aikta na N615,000

    ...

    Asalin hoton, other

    Kungiyar ƙwadago ta Najeriya NLC ta gabatar da buƙatar ƙarin sabon albashi mafi karanci na N615,000 domin magance kalubalen tattalin arziki da tsadar rayuwa da ma’aikata ke fuskanta a Najeriya.

    Shugaban kungiyar ne ya tabbatar da hakan ga gidan talabijin na Channel a ranar Lahadi.

    An cimma sabon albashin N615,000 duk wata bayan tattaunawa tsakanin ƙungiyar kwadago ta NLC da TUC ne da nufin rage matsalolin kudi da ma’aikatan Najeriya ke fuskanta.

    Ƙungiyoyin ƙwadagon sun ce mafi karancin albashi na N30,000 a halin yanzu ba zai iya biyan buƙatun talakawan Najeriya ba, suna masu korafin cewa ba dukkan gwamnoni ne ke biyan albashin ma’aikata na yanzu ba wanda zai ƙare a watan Afrilu, shekaru biyar bayan sohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya rattaba hannu kan dokar mafi karancin albashi ba 2019 inda za a sake duba dokar duk bayan shekaru biyar.

    Kungiyoyin NLC da TUC a lokuta daban-daban sun yi kira ga gwamnatin shugaba Bola Tinubu da ta gaggauta sake duba mafi ƙarancin albashin ma’aikata.

    A farkon watan Janairu ne gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da wani kwamitin mutum 37 kan mafi karancin albashin ma’aikata na kasa.

    Da farko dai ƙungiyar kwadago ta NLC ta sanar da naira miliyan ɗaya a matsayin sabon mafi karancin albashi, sakamakon hauhawar farashin kayayyaki a kasar da ya jefa mutane da dama cikin talauci.

    Yayin da kuma TUC ta buƙaci naira 447,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi na wata-wata ga kowane ma’aikaci, wanda daga baya kuma NLC ta bukaci N794,000 ga kowane ma’aikaci.

    Amma ƙungiyoyin biyu, a wata sabuwar shawara ga gwamnati, sun buƙaci naira 615,000 a matsayin sabon mafi karancin albashin ma’aikata.

    Kungiyoyin sun ce hauhawar farashin kayayyaki - wanda ya kai kashi 31.70 cikin 100 a watan Fabrairun 2024 ya shafi tsadar rayuwa ga matsakaitan ma'aikatan Najeriya.

    Sun kuma lura da cewa gwamnonin jihohi za su iya biyan kowane ma'aikacin gwamnati albashi saboda a yanzu suna samun karin kudaden shiga kowane wata daga hukumar dake tattara da raba arziƙin ƙasa (RMAFC).

    • Abu bakwai da gwamnatin Najeriya ta cimma da 'yan ƙwadago
    • Ƙarin hauhawar farashin da aka daɗe ba a gani ba na gigita ƴan Najeriya
  4. Yadda kama ɗan jarida ya janyo cece-kuce a Nijar

    Ƴan jarida a Jamhuriyar Nijar na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan kamen da hukumomin ƙasar suka yi wa wani ɗan jarida Usman Tudu.

    Ƴan jaridar sun buƙaci gwamnatin ƙasar da ta sake shi nan take kamar yadda za ku ji cikin rahoton Tchima Illa Issoufou.

    Bayanan sautiDanna hoton domin sauraron cikakken rahoton
  5. Gabas ta Tsakiya na cikin haɗarin ɓarkewar rikici – Antonio Guterres

    ..

    Asalin hoton, EPA

    Sakatare janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres ya ce lokaci ya yi da ya kamata a dakatar da yaƙin Gabas ta tsakiya.

    Kalaman nasa na zuwa ne bayan da Iran ta harba ɗaruruwan makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa ga Isra'ila a ranar Asabar.

    A yayin wani taron gaggawa da kwamitin tsaro na Majalisar ya kira, mista Guterres ya ce al'ummar gabas ta tsakiya na tunkarar ɓarkewar gagarumin rikici.

    Wakiliyar BBC ta ce wakilin Iran a Majalisar ya shaida wa kwamitin cewa hare-haren ramuwar gayya ne Iran ta kai kan Isra'ila kan harin da Isra'ilar ta kai wa ofishin jakadancinta a Siriya.

    • Abin da muka sani kan harin da Iran ta kai wa Isra’ila
    • Wane yanayi ake ciki a Iran bayan kai wa Isra'ila hari?
  6. Amnesty ta nemi gwamnati ta hana ayyukan kamfanin Shell a Najeriya

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnesty International ta shiga sahun masu kira ga gwamnatin Najeriya da ta dakatar da kamfanin mai na Shell daga gudanar da aikinsa a ƙasar har sai an samar da kariya ga mutanen Neja Delta.

    Ƙungiyar ta ce ayyukan kamfanin na ƙara haifar da cin zarafin ɗan adam idan har ba a shawo kan matsalar gurɓata muhalli da kamfanin ke haifarwa ba.

    Ƙungiyar ta ce dole ne kamfanin ya samar da wadatattun kuɗin da za a yi amfani da su wajen gyara gurɓacewar muhalli da ayyukansa ya janyo sannan dole a tuntuɓi mutanen yankin kan maganar sayar da kamfanin kan fiye da dala biliyan 2.4.

    Masu fafutuka sun zargi Shell da hannu wajen yawan malalar mai a yankin Neja Delta da wasu matsalolin da suka janyo guracewar magudanan ruwa.

    Gwamnatin Najeriya dai ba ta ce komai ba kan batun.

    A baya kuma Shell, ya yi alƙawarin sabbin mamallaka kamfanin za su duba ɓarnar da aka yi.

    • Shell zai biya manoma a Neja Delta diyyar dala miliyan 16
    • 'Gurbacewar muhalli tamkar shafe al'umma ne'
  7. Barka da Safiya!

    Masu bibiyar mu a wannan shafi na Kai Tsaye, barka da wannan lokaci.

    Da fatan kun wayi gari lafiya a wannan rana ta Litinin - tushen aiki.

    Sai ku kasance da mu kamar kodayaushe da za mu kawo maku labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Akwai shafukanmu na sada zumunta da za ku iya leƙawa domin karanta ƙarin labarai da kallon bidiyo.